Wani 'katon cake ta gani daya sha ado sosai pink and white rubutu akai masa akai "Happy birthday sweetheart" da candle jere a kai.
Sede ita bata ga abinda aka rubuta ba tunda bata 'karasa ba.Gefensa kuwa laptop d'insa ce yana video call,tana jiyo murya mace amma bazata iya ganin fuskarta ba,bata bari ya d'ago ya kalleta ba tayi saurin komawa d'aki."Happy birthday baby" Tare suka bushe candle d'in as if tana kusa da cake d'in.
"Thank you Baby" Ta fad'a tana washe ha'kora dan ta kasa rufe baki saboda farinciki.Balloons manya daya sa'kala jikin fridge ya ciro su."Do you like this baby?"
"Yes I love it "
Teddy bear dayai hiding a bayan laptop d'insa ya ciro 'kato pink colour a tsakkiyar cikin an rubuta happy birthday beautiful "
Nan ma wani sabon farincikin ne ya rufeta."Baby you're so sweet"
"You deserved more than this baby"
Hira suka shiga yi abinsu ,Laila kuwa jitai dama bata sauka 'kasan ba dan ma Allah yasa bai ganta ba.Dama ba wani yunwa take ji ba,gasasshen masarar data suyo a hanya ta d'akko a jaka ta soma gagayar kayanta, tana yi tana danna wayarta.
Se wajajen 8:15pm ta sakko kitchen, balloons d'in duk nemansu tayi ta rasa seda ta bud'e fridge taga cake ,yaci iya wanda zeci ya bari .Rubutun da akai ta kalla ta ta'be baki ta d'auki abinda zata d'auka a fridge d'in ta rufe.
★★★
Washegari da safe ta makara se sauri take ko living room bata gyara ba kitchen kawai tayi goge-gogenta bayan tayi breakfast ta koma d'aki ta shirya.Tana daf da fita taji ya kira sunan da yafi son gaya mata."Madam chef"
A hankali ta waiwayo fuskarta a rufe tana kallonsa ko shirin office beyi ba 3qtr ne da shirt a jikinsa.Ganin ya 'karaso ta sauke kanta 'kasa.
"Remember you're now a married woman don't tell me that you don't know your duties, I mean what you suppose to do here"
"Mey kuma zanyi bayan wanda nake"Ta fad'a a ranta.
" What?"
"Prepare me a meal"Ya amsata."It's getting late,it's almost 8 "
"I don't care "
"But.."
"Just go on with your works and stop wasting much time"
Har ya koma ya dawo "I forgot to tell you,I need omelette and sandwiches"Daga haka ya koma d'akinsa.
Tunani ta shiga yi ko tayi tafiyarta,amma kuma tana gudun abinda ze biyo baya.Haka tana ji tana gani ta cire hijab da niqab d'in ta fara ,tana yi tana mita."Da abincin kake cewa ai maka,ko dan kaga ka bani kud'i""Kuma Allah ya kaimu gobe, baza ka san lokacin da zan tafi ba".
Ba ita ta gama ba se 8:53am tana gama ajje masa a dinning ta saka hijab d'in ta ta fice.Yana daga d'aki ya hango fitarta,murmushin gefen fuska kawai yayi ya cigaba da harkokinsa.
Lokacin data isa makarantar har an shiga lecture,seda tayi missing wannan lecture d'in.Se na 'karfe 12pm ta samu 2:30pm ta dawo gida.
Motar sa da ta gani hakan ya tabbatar mata yana gida,lokacin da ta shiga a living room ta ajje jakarta ta nufi kitchen ganin plate na d'azu inda ta barsu yasa ta ci birki,'karasawa tayi table d'in ta bud'e ba abinda aka ci na ciki d'ayan ma haka ,ta rasa ma mey zatayi saboda tsabar takaici.
