Chapter 21

775 52 0
                                    

Alamun murya taji a waje wanda yake tabbatarwa d'akin za'a shigo."Dan Allah ka sakeni,please let me go"

"You have to repeat what I will say before I let You go"

"My husband, please let me go" Ya fad'a.

Ganin ba mafita ta maimata"My husband please let me go ".Tana fad'a ya saketa yana murmushi.

Da sauri ta mi'ke ta bar gurin tayi chan nesa dashi " Mugu"Tayi maganar a ciki.

"Assalamu Alaykum" Akai sallama bayan an turo 'kofar d'akin.Laila tana d'agowa ta had'a ido da Aisha ri'ke da 'yarsu se Farouq a bayansu.

"Waalaikumussalam" Ta amsa fuskarta a sake.

Da yake Aisha irin mutanennance masu saurin sabo kamar ta dad'e da sanin Laila haka suka gaisa ,dukda yarinyarsu mey 'kwiyace da Laila ta kirata bata 'ki zuwa ba.

"Fad'a min sunanki?"Ta tambaya tana d'orata kan cinyarta.

"Minal" Ta amsata tana wasa da takalmin 'kafarta.

Amjad dake hira da abokinsa Farouq rabin hankalinsa na kanta ,seyaga tayi 'kyau da kid a hannunta.Zuwan Aisha ya d'ebe mata kewa taji dama karta tafi,lokacin da zasu tafi har rakasu waje tayi bayan sun tafi maimakon ta dawo setai zamanta a waje kan bench.

Amjad jin shiru bata dawo ba ya kirata a waya sejin ringing d'in wayarta yayi a d'akin,yasan dama so take ta samu damar da zata fita shiyasa tayi rakiyar.

Seda taji zaman wajen ya gundireta tukun ta komo ciki.

"Meyasa baki zauna chan ba?" Taji ya fad'a.

"Ai yanzu zan koma" Ta fad'a stubbornly.

"Zan gani taya zaki fita"

"Taya za'a iya ,mutum a kwance"Tayi maganar a hankali.

"Haka kika fad'a koh?"Ya kad'a kai.

Jin haka yasa bata 'kara fad'ar 'kala ba se wayarta data d'akko ta soma dubawa.

★★★

Haka suka cigaba da zaman asibiti koyaushe rikici na yau daban na gobe daban ,wani sa'in ko ze iya yin abu da kansa seyace baze iya be setayi masa ,seda suka kwashe sati biyu cir aka yi discharging d'insu daga asibitin lokacin ya samu sau'ki sosai dan a yanzu an cire masa plastern hannunsa an sauya masa da arm sling,bandage dake zagaye a kansa shima an cire iya patch d'an 'karami be ya rage gefen eyebrow d'insa na hagu.Mom kuwa kwanansu biyu da komawa Canada,Laila jefi-jefi tana shiga school yanzu ma exam zasu fara result nasu na wancen semester ya fito ta samu sakamako mey kyau.

First day da suka komo gida,tunda ta shiga d'akinta kuma shikenan ko le'kowa ta'ki yi 7:30pm se addu'a take karya kirata dan tana expecting hakan.

Ring! Ring! Wayarta tayi 'kara ,har cikin zuciyarta taji kiran."Canada"

"Mutum sekace tsoho"Ta d'aga kiran.

" Laila where are you?"

Bata amsa ba ta katse kiran ,mayafinta ta sura ta yafa ta fita zuwa d'akinsa.Tana shiga ta tsaya daga bakin 'kofa tana kallan gefe.Yana zaune yayi d'are- d'are kan mirror drawer.

"Laila you left me alone,I'm hungry"

Juya tayi zata fita ya tsayar da ita"You didn't ask me what I wanna eat"

"What is your favorite?" Ya tambayeta.

"D'an wake" Ta amsa dukda kuwa ba shine fav d'inta ba.

Kasa repeating d'in abinda ta fad'a yayi dan haka ya gid'a kai kawai.

"OK,make me your favorite".

" Uhum"Ta fita.

"Zaka ga favorite sekayi regretting cin d'an wake,bade kai d'an takura ba" Ta fad'a tana d'akko bowl zata had'a d'anwaken.Cikin 'kan'kanin lokaci ta gama kwa'bawa ruwan data d'ora ya tafasa nan ta soma sakin d'anwakenta kai kace d'an 'karamin ball ne dan girma,tana gamawa after few minutes ta sauke.Plate ta cika taf ta ziba manja ko soyawa batai ba danma ba'a daskare yake ba,Maggie ta 'bare ta barbad'a ta d'ibi yaji tea spoon hud'u ta ziba akai ta ko ina,ta d'akko fork ta d'ora.

Dayake tasan mey ta shirya se gimtse dariyarta take ta shiga d'akin,daga drawer side na bango ta ajje plate d'in dake a rufe. Ganin haka Amjad ya sakko daga kan mirror drawern ya 'karaso inda take.

"Sit" Ya fad'a yana d'aukan plate d'in.

Tana tsaye kawai jira take taga ya bud'e taga irin reaction d'insa,d'an basarwa yayi ya kalli kalar d'an waken ya d'anyi guntun murmushi. "Feed me" Ya mi'ka mata plate d'in. Daga gefen gadon ta zauna opposite dashi,'kwaya d'aya ta soka wanda yaji yake mamaye a kai ta mi'ka masa saitin bakinsa.Amjad yana kallonta ya mi'ka baki ya kar'ba ,tashin farko yaji uban yaji gashi ya shika masa bakinsa ko taunawa da'kyar yake,kamar ma'kogoronsa ze fashe haka ya had'iye.Kafin ya dawo cikin nutsuwa tasake sokar wani ta mi'ka masa, kamar wanda aka dannewa baki ya kasa maganar,haka ya bud'e bakinsa ta sake zirawa.Ma'kwat! kuke ji take bakinsa ya d'ad'e shhh! Ya fara.

Tana sake mi'ko wata lomar ya kauda kai murmushin fuskarsa ya d'auke.Wata muguwar dariyace ta ku'bucewa Laila har tana rufe bakinta.

"What did you do?" Ya kalleta cikeda tuhuma

Tashi tayi da sauri ta dire plate d'in tayi hanyar 'kofa tana dariya harda dafe ciki,kamar kiftawar ido taga yasha gabanta"You're not going anywhere"Ya kulle 'kofar dakin.

I'm sorry for the short chappy am busy sosai.Love ur

Dijensy









AMJAD(Completed)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora