Dukansu wuri suka samu suka zauna,Shaheed da Zakia suna zaune 2 seater se Mom da Dad da suke zaune kan 3 seater Amjad ya hakimce kan 1 seater daga can 'kuryar parlon se cin magani yake.
Cikin rissinawa yaran suka gaida Mami da yaran Hausa shima yai koyi da abinda suka ce yayi mata gaisuwa,suma Mom da Dad suka sake mata gaisuwa bayan sun gaisa.
"Ina yaran suke?" Dad ya tambaya.
"Dukansu sun tafi islamiyya nan da anjima zasu dawo"
"Allah yayi albarka" Cewar Mom.Mami ta amsa da "Ameen".
Hira kad'an suka d'an ta'ba wanda kusan duk akan yaran nasu ne ,nan Mami take fad'a masu Laila ta kammala karatun secondary.Sun kwashe kusan 1hr tukun suka je gidan kawu Yunusa ,bayan sunyi kamar 40min Mom da yaran suka komo gidan su Laila Dad yana tare da Kawu yunusa suna tattaunawa.
Kamar yadda sukai zaman farko haka sukai yanzunma ba wanda ya chanja position, Amjad da zafi ya fara isarshi se d'aga 'kasan T-shirt d'insa yake yana firfita sekace ba fan a d'akin.
Zakia ce ta d'auki jug d'in da Mami ta kawo musu ruwa ta tsiyaya a cup ta sha,Shaheed ma ta ziba mishi sannan Mom.Mom da kanta ta ziba wa Amjad ta bashi,shide ya ri'ke a hannu amma ya'ki sha se danna phone d'insa yake.
5:43pm su Laila suka dawo gida tun daga 'kofar gida suka gane anyi ba'ki sede basu san su waye ba.
" Assalamu Alaykum"Sukai sallama.
"Daga parlor Mami ta amsa ,Nusaiba da Fauzan ne suka le'ka cikin rissinawa suka gaishesu da sauri Nusaiba ta tashi shi kuwa yaje ya ma'kale da Mami yana sunkui da kai.
" Suwaye suka zo?"Maryam ta tambayi Nusaiba.
Laila da take cire hijab bayan ta ajje bag d'inta tace"Idan kin damu kije mana ki gani"
Dama tun a islamiyya wani malaminsu ya bata haushi.
"Daga tambaya"
"Wa'annan d'innan 'yan uwan Baba ,'yan farare"Cewar Nusaiba.
" Laa kawu Abdallah "
Laila da ta gano suwa ake nufi amma tayi kamar bata sansu ba koda ta gama sauya kaya waje ta samu ta zauna 'karamar wayarta ta d'auka ta hau danne -danne.
Maryam kuwa tana gama sauya kayanta ta tafi parlorn ta gaishesu,daga gefen Mami ta d'an raku'ba ta zauna Zakia se faman murmushi take wa yaran tana ji ina ma ace sun saba.
Amjad tun shigowarsu be ko d'ago kai ba dan koda suka gaida su Shaheed ne da Zakia suka amsa hankalinsa na kan chat d'insa.
"Ina Yayarku?" Mami ta tambayi Maryam a hankali.
"Tana d'aki"
"Toh kice mata tazo su gaisa mana"
Tashi tayi taje ta fad'a mata ko uffan bata amsa ta ba.
"Yaya baki jini ba?"
"Naji karki takura min"
Wucewarta tayi ta koma "Tana ina"Mami ta tambaya.
" Wai karna dameta"
"Bari naje na doko ta wannan halin bazata fasa ba mutum ya shige 'kuryar d'aki yana miskilanci"
Mami ce ta tashi ta tafi zuwa d'akin yaran ta isketa ma ta shingid'a kan katifa abinta.
"Mey kike yi da baza ki taso ba ana kiranki?"