Chapter 19

811 47 0
                                    

    Thank you for your warm support sister,Amjad fans kuma ina godiya ,ana tare✌

       Mey d'an sahun da aka yi 'ko'karin ciro shi daga d'an sahun aka ga ko numfashi bayayi ,kwance aka ajje shi gefe,daga 'kasan gada kuwa mutane uku ne suka shiga kici kicin bud'e 'kofar motar amma abu ya gagara ,seda ambulance suka 'karaso suka ciro Amjad da 'kyar sakamakon belt dake ma'kale a jikinsa, jini ya wanke fuskarsa haka aka sanya shi a mota a sheme.

               ★★★

     2hrs later,tana d'aki tana duba handout wayarta tayi ringing,ganin Canada jikin screen ta'ki picking.Sau biyu ana kira bata d'aga ba se ana uku."Hello".Cikeda  'kosawa.

      Jin murya daban bana Amjad ba yasa ta gyara zama.Tana jin abinda aka fad'a ta d'ayan 'bangaren ta saki wayar kan gado.

       Ta rasa abinda zatai,wayar ta d'auka ta sake kallan call d'in."Amjad "Ta furta a tsorace.Tafi 10min kafin daga baya ta d'au waya ta kira Mami.

      " Innalilahi wa innailaihirraji'un"Mami ta fad'a.

      "Kina asibitin?" Mami ta tambaya cikin rud'ani.

        "A'a"Ta amsa feeling guilty.

        " Mey kika zauna yi da baza ki tafi ba?"

        "Zan tafi yanzu" Ta fad'a.

         "Toh nima ina tahowa".

     Mami kafin ta tafi seda taje gidan Kawu Yunus ta fad'a masa halin da ake ciki,tare suka tafi asibitin kusan tare suka isa da Laila, Kawu Yunus ne ya kira Dad ya sanar masa.A gabansu aka  shiga dashi theater room hankalinsu yayi mugun tashi dan yanayin da suka tsince shi.8:15pm aka fito dashi daga nan aka kaishi d'akin kwanciya,suna kan bench ko d'akin basu samu shiga se bayan doctor ya fita daga d'akin,Mami da Kawu suka shiga abin tausayi hannunsa yasha plaster sakamakon karaya se kanshi an zagaye masa da bandage, ga 'karin jini da ake masa.

      " Allah ya baka lafiya"

       "Ameen" Mami ta amsa cikin nuna jimami.

        Kawu Yunus se can dare ya tafi ya bar Mami da Laila data kasa shigowa tana waje kan bench itama daga baya Mami fitowa tayi ta zauna kan bench d'in.

     Mom kuwa basu san mey ake ciki ba se ji sukai Dad yasa su shirin tahowa Nigeria da suka tambayesa dalili ya'ki fad'a musu.Koda ta kira Amjad d'in ma ta fad'a masa suna zuwa taji wayar a kashe.

     Washegari 9pm suna Nigeria, Mom tunda taga an shigo asibiti jikinta yayi sanyi."Tell me what's going on?"

     "It's Amjad..."

      "Mey ya sameshi ? What happened to my son?"

       "He had an accident"

       Dukansu ba wanda be firgita ba,cikin rashin ha'kuri driver na parking ta fita a motar Dad yana kiranta amma ta'ki tsayawa,da 'kyar ya samu ta tsaya ganin ba sanin d'akin tai ba.Seda suka kira Mami ta fad'a musu numbern room d'in.Cikin rud'ani suka 'karasa ,Laila tana zaune kan bench tagansu tsidik cikin hanzari suka shiga ita de ta bisu da kallo dan har lokacin ta'ki shiga d'akin.

     Har yanzu yana kwance same position ko motsi beyi ba,Mami da Zakia tuni suka fara tsiyayar hawaye.

     "Amjad" Ta 'karasa gefen gadon.

      Hannunta ta d'ora kan gashin kansa tana shafawa.

      "My child"

      Suna tsaye a kansa Mami ta shigo d'akin,bayan sun gaisa suka jajantawa juna Mami se bawa Mom ha'kuri take amma ta'ki dena sharar hawaye.

AMJAD(Completed)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon