Tana gani ya rifo 'kofar hanjin cikinta ya kad'a ta soma had'iye dariyarta.A hankali ya soma takowa inda take ta fara ja da baya ganin ta kusa 'kure bango ta fara zagaye a d'akin "What did you do?"Ya fad'a yana nufar inda take.Ganin ya'ki tsayawa gashi tazo daf da gadon aiko take ta haye kan gadon tana so ta zauka gefe." Laila you better stop you can't run away from me because I have the key with me"
Dukda abinda ya fad'a bata sauraresa ba seda ta 'karasa 'kofar tayi ta girgizawa amma ta kasa bud'ewa,ganin ya zagayo inda take ta sake guduwa yayi can tayi nan haka sukai ta zagaye a d'akin ,daga 'karshe yayi nasarar ri'kota."Please I'm sorry"Ta fara bashi ha'kuri take idonta ya raina fata.
"Why? did you want me dead?"
Girgiza kai tayi alamar a'a."Then why did you do it?"
"I said I'm sorry"
"I don't need your sorry, this is pay back time now is my turn" Ya fad'a yana ri'ke da hannunta ya janyo plate d'in d'an waken ya mi'ka mata.
"Eat"
Ita kanta data saba ganin d'anwake seda taji tsantsamin ci gashi yaji burjik ya ratsa ko ina."Please sorry "
"Don't sorry me ,you didn't offended me ai I just want you to taste it isn't it your fav?"
Da sauri ta girgiza kai "No" Ta amsa.
"Then why did you lied?"
"I'm sorry"
"You lied because you wanted to purnish me ,now eat"
Ya sake mi'ka mata,fafur taki kar'ba aiko ganin haka ya zaunar da ita daga can jikin gadon ya zauna daf da ita yadda bazata iya gudu ba.Hannunta ya sake ya d'auka fork d'in ya soka d'aya kamar yadda yaga tayi ya mi'ka mata "Arhh"
'Kin bud'e baki tayi ta marairaice ,yana sake matso da fork d'in tasa hannunta ta rife bakin, yin duniya ta'ki yarda ta bud'e bakinta garin zillewa ta kwanta kan gadon a rigingine kafin ta yun'kura ta d'ago yayi mata runfa.
"Sorry" Ta fad'a kamar zatai kuka.
"Don't mention" Yayi maganar cikin sanyi murya wadda bata ta'ba jin yayi irinta ba.
"Please let me go"
The more tana magana the more yana sake matsowa kusa,ganin baida niyyar dakatawa tasa bayan hannunta ta rufe bakinta ta rufe idanunta.Tafin hannunta taji yayi kissing wani irin shock taji take ta soma mutsu-mutsu,garin haka ta bigi hannunsa mey karaya."Auchh!"
D'agowa tayi da sauri tana kallonsa cikeda rud'ewa ta dafa kafad'arsa "Sannu ,sannu".
D'ago da kansa yayi yana kallonta ya soma murmushi,ganin faking ne ta d'auke hannunta ta d'aure fuska da sauri ta mi'ke harta kai bakin 'kofa be mata magana ba.
"Please ka bud'e min"
Shiru yayi bece mata komai ba se blanket d'inshi daya janyo ya gyara kwanciyarsa bayan ya cire Shirt d'in jikinsa.
Ganin ya juya baya ta dafe kai "innalillah kwana anan d'akin?" Ta fad'a a ranta.
Tsaiwa ta cigaba dayi tana ri'ke da handle d'in 'kofar,tafi 30min a tsaye harta gaji gashi couch d'in d'akin bata nan balle ta zauna.Drawer mirror ta soma dubawa ko zata ga key amma babu alamarsa,drawer side na bed ta dudduba nan ma babu a cikin sand'a ta 'karasa drawer side d'in dayake kwance taga ya rife idanunsa yana bacci.A hankali ta duba itama babu ,wani tunani ne ya fad'o mata aiko ta zagaye baya tana tunanin ta ina zata soma lalubar aljihunsa,cikin sand'a ta d'an d'age blanket d'in a hankali ta zira hannunta a cikin pocket d'in sede ba komai ciki ganin alamar yana motsi tayi sauri ta d'auke hannunta taja baya.