Nan take ta dur'kusa tana dafe 'kafarta,ha'kuri ya shiga bata "I'm sorry ,I'm so sorry Laila".
" Ba wani sorry kana sani"Ta fad'a tana ri'ke da 'kafar.
Cock d'in ta kalla daya gangara 'kasa dan shi take tunanin ya fad'o mata a 'kafar.Mi'kewa tayi tsaye ta fara tafiya amma ta 'kasa take 'kafar se d'ingisawa take."Let me help you"Ya taho da shirin ri'ke hannunta ya d'ora a kafad'a aiko tayi saurin matsawa garin haka ta take 'kafar."Aghh!"Ta tsala 'kara.
Bata ankare ba taji an raba ta da 'kasa anyi mata d'aukan amarya, tuni ta shiga wutsul -wutsul tana d'uma masa duka a kafad'a."Mami!"Ta hau kiran sunan Mami.
Har seda ya kaita d'akinta sannan ya direta kan gadon."Stubborn ".Ya fad'a."Nan da nan idanuwanta sun cika da 'kwalla seda taga ya sauketa a d'akinta ta d'an nutsu." You can leave now"
"You're sending me away,what did you think I'm doing? Sometimes you're crazy"
Fita yayi daga d'akin bayan 'yan minti kad'an ya dawo da man zafi a hannunsa.Jira take taga abinda yake 'ko'karin yi,tana gani ya zauna gefen gadon tare da ri'ke 'kafar ta matsar da 'kafar."Na iya shafawa"
Duk da be fahimci abinda ta fad'a ba ganin ta matsar da 'kafarta ya mi'ka mata man "Rub it".
Kar'ba tayi cikin sanyin jiki ta bud'e man ta soma shafawa a 'kafar a hankali sekace mey tallan mai.Ta sakankance taga ya wafce man ya soma shafa mata yana matsa 'kafar,hannunsa tasa tana 'ko'karin janye nasa hannu amma ta kasa sema ri'ke hannayenta biyu da yayi waje guda ta kasa ku'bucewa ,haka tayi ta raki har seda ya gama.
" Toh sake min hannun tunda ka gama"
"Mey kika fad'a?" Taji yayi magana.
"Tunda ka iya yaran ai zaka sani"
"I can speak hausa for the whole entire day"Yadda yayi pronouncing d'in hausar kamar like " Hosa"
"Ok,start"
"Ok,yanzu" Ya fad'a yana murmushi.
Itama murmushin tayi tana kallon arm d'insa data buga d'azu har wajen yayi ja kasancewar singlet ce a jikinsa.Shikuwa murmushin datai ne yasa ya kasa dena kallonta dan ba 'karamin kyau tayi ba.Saurin kawar da ido tayi ganin ita yake kallo,wayarta dake gefe ta d'auka ta hau dubawa dukda ba abinda take da ita.
"Na fita?"Taji ya tambaya.
"Eh"Ta amsa kanta a sunkuye.
" Ok,I'm going but you have to answer my questions "
"Questions".
"Yes".
Kai kawai ta girgiza tana tunanin irin tambayar da zeyi mata."Do you have feelings on me ? don't lie"
Sam batayi tunanin wannan tambayar zeyi mata ba duk da bata rasa amsar fad'a masa ba sede kuma tana mamakin dalilinsa na tambayar.Ya tsireta da ido kawai jiran amsarta yake.
"No" Ta amsa ba tare da ta bari sun had'a ido ba.
"No" Ya maimaita abinda ta fad'a.
"Ok,let's assume I love you? Will you love me back?"
"No"
"Why?"
"Because I don't love you"
"Your heart is for only one person?"
"I want to sleep" Ta fad'a tana janyo blanket d'in.
