Binsa tayi da kallo tana jira taga mey zeyi da abincin,har kusa da ita yazo ya wuce ta gefenta yana rungume da flask d'in ya haye sama ya barta a tsaye tana had'iyar miyau.Jitayi kamar ta bishi amma gudun karya wula'kantata ta nufi kitchen, seda ta fara had'a tea tasha tukun ta d'ora indomie sharp sharp ta gama da zafi-zafinta haka ta samu taci harda guntun hawayenta na takaici.Se bayan ta gama cin abincin ne ta tuna bata yi sallah ba maghrib da isha'i,shima Amjad d'in tunawa tayi beyi ba."Tabb! La'ilaha illallahu maimakon yaje masallaci ,toh ko dama haka yake wasa da sallah?"Ta tambayi kanta tana mey mamakinsa dan ita shaf ta mance yunwa ta rufe mata ido batai noticing ba.
"Astaghfirillah" Abinda ta fad'a kenan ta koma d'akinta kayan kuwa ta barsu anan. Seda ta idar da sallolin da ake binta tukun ta samu nutsuwa,tana yin wanka tayi shirin kwanciyarta koh phone d'inta bata duba ba dan gajiya.
Washegari da safe kafin ta fito taji fitar Amjad, 8:20am agogon d'akin ya nuna.Inda ta bar kayan jiya anan tazo ta tarar dasu,ta'be baki tayi tai wucewarta kitchen "Ka kaiwa budurwarka ba niba"
***
Sati d'aya su Mom suka 'kara a Nigeria suka koma ,kafin su koma seda suka zo gidan Laila.Amjad ji yake kamar ya bisu ,tun lokacin da suka koma ya dena walwala ko kula Laila bayi yake ba balle magana ,kaya kuwa bata kwashesu ba se lokacin da Mami zata zo ta d'auke ta kaisu wani d'akin daban ta rife.A yanzu sun kwashe wata d'aya kenan da aure.Saturday 8:17am,ta gama shirinta cikin lace black mey red torches,tasa sar'karta mey stones red color tayi matu'kar kyau ga d'aurinta da ya tsaru fuskarta tayi light makeup se 'kamshin turare take.Tana sauka 'kasa taga parlourn ma ba wani datti yayi ba dama jiya da yamma ta gyara shi,kitchen ta shiga dan had'a karin kumallo ,yau doya da 'kwai taji tana sha'awa ,tana d'ora doyan a pot ta nufi drawern dan d'akko bowl ,kasancewar tsahonta baya kawai setayi d'age tana janyo bowl d'in ya su'buce ya fad'o kan babban yatsanta na 'kafa Tass! Ya fashe pieces a wajen ,take ta saki wata 'kara dan azaba.Fuskarta tuni tayi jazir gumi yana keto mata,zaman dirshan tayi tana ri'ke da 'kafarta d'anyatsan se jini yake.
"What happ.." Be 'kare tambayar ba yayi shiru da bakinsa ganin yadda 'kafarta ke zubar jini.
Kuka ta shiga yi sharaf-sharaf hawaye yana zuba.
"Get up" Ya fad'a tare da d'ora hannu da niyyar mi'kar da ita.
"Aghhh!" Ta 'kwallo 'kara.
Jin 'karar da tayi yasa ya d'auke hannunsa,tana zaune ita bata tashi ba kuma bata dena kukan ba."Are you staying like this? "
Banza tayi dashi kamar bata jiba,yana sake d'ora hannunsa a kafad'arta ta kuma tsala ihu fin da.Ita bama iya zafin yasa ta 'karar ba ta'bata ne bata so yayi.
Tsaki yayi "It left for you" Ya fita daga kitchen d'in.Yana fita ta tashi se d'ingishi take,ganin jinin yana d'iga a 'kasa ta zauna kan wani couch.Tana hangoshi ya sakko daga bene hannunsa ya ri'ko first aid.
"Cabb! Zaka ga first aid"
Bata ankare ba taga yaja wani guntun table ya zauna opposite da ita."Let me see"
"Kaga mey? kai likita ne?"
Ko bin ta tata beyi ba ya kama 'kafar se fisgewa take amma ta kasa "Aghh!"Se 'kara take yayi banza da ita yana goge jinin se kuka take, seda ya gama ya rife ciwon da bush tukun ya sake mata 'kafa.
" Allah ya is a"Ta fad'a a fili tana share hawaye.
"You have to be careful"
"Ni matsa min na tashi" Ta fad'a tana 'ko'karin mi'kewa.