Chapter 23

903 58 0
                                    

     Tana had'a ido dashi ta sauke duk kunya ta isheta,fuskarsa d'auke da murmushi ya 'karaso ciki tare da rufo 'kofar.Hannayenta biyu ya ri'ko cikin hannayensa yana murzawa softly."Laila what are you hiding on your face? let me see your pretty face".

     "Laila" Ya sake kiranta ganin ta'ki d'agowa.

      A hankali ta d'ago da kanta sede ta'ki bari su had'a ido,hannayen nata duka biyun ya had'a yayi kissing."Did you know how pretty good your hands look like? I really love them".
  
      "Amjad'Ta kira sunansa.

      " uhm?"

       Be ankara ba cikin sauri ta zare hannunta kafin yayi wata maganar tayi sauri ta haye sama ta barshi tsaye a gun,tana shiga d'akinta ta rufe 'kofar se numfarfashi take hannayenta tasa a gaba tayi ta kalla.

        Amjad kuwa hanyar kitchen yayi kan dinning yaga warmer daya bud'e kuwa yaga fav d'inshi"Wow!"Ya furta ,ba 'bata lokaci ya d'auka serving spoon ya ziba a plate
har rawar jiki yake yakai loma d'aya waje ya samu ya zauna dan santi harda cire suit,seda yayi dam tukun ya tashi ya shiga kitchen daya bud'e fridge yaga pineapple juice nan ya tsiyaya a glass cup ya kora dashi.

               ★★★

     20 minutes later, taji knocking 'kofar d'akinta,a d'ari-d'ari ta 'karaso ta bud'e. Tsaye ta ganshi ri'ke da tray a hannunsa."May I come in?"

     Kai ta kad'a alamar "eh" tana sunkui da kai.Daga kan drawer side na gadon ya ajje sannan ya dawo inda take. "Laila you haven't eat and you're here alone it's boring"

     Hannunta ya ri'ke ya zaunar kan gadon,daga gefenta ya zauna ya d'auko plate d'in abincin.Open up"Ya mi'ka mata spoon d'in cikeda abincin.

     "I..." Bata fad'i abinda take son cewa ba yasa mata a baki,itade tana ganin ikon Allah 'kiri-'kiri ta kasa hanashi bata abincin kuma ta kasa hana kanta ci,tana so ta tambayeshi ko yaci abincin amma ta kasa."Is ok"Ta fad'a bayan ta 'koshi.

     "Sure?"

      "Yes" Ta amsa tana gid'a kai.

        Juice d'in ya tsisaya a cup ya bata shima ta kur'be."Laila did you know my favorite food? "Ya tambayeta bayan ya maida cup d'in.

     " Yes"Ta amsa still ta'ki kallonsa.

      "How?" Ya tsireta da ido.

       Shiru tayi ta'ki fad'a yin duniya ta'ki fad'a masa se murmushi kawai da take. "Come with me" Ya ri'ko hannunta bayan ya mi'ke daga zaune, ba musu ta tashi daga zaunen itama.

 
      Hannunta a cikin nasa suka fita daga d'akinta,a tsorace take tafiyar ganin suna yin hanyar d'akinsa.Suna shiga be tsaya da ita a ko ina ba se gaban mirror.Drawer taga ya bud'e daga gefe taga ya d'akko d'an 'karamin box blue colour.Hannu yasa ya bud'e nan had'ad'd'en necklace ya bayyana mey silver chain pendant d'in blue stone se walwali yake,bayan ya d'akko sar'kar ya ajje box d'in gefe stool d'in mirrorn ya gyarawa zama sannan ya juyo gareta."Laila ,sit"Ya fad'a cikin tattausan murya.

     Ba musu ta 'karasa ta zauna tana facing mirror d'in,a tsanake ya bud'e sar'kan tare da saka mata a wuyanta ,sosai ta zauna a wuyanta ita kanta sar'kan ta burgeta matu'ka,ta sakakance tana ta kalla taji ya d'ora ha'barsa kan kafad'arta fuskarsa d'auke da murmushi yake kallonta ta mirror tana gani sun had'a ido tayi saurin sauke idonta

   "For you only my heartbeat"

       
"Now i don't care about anything , i am not afraid of anything"

AMJAD(Completed)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang