Chapter 15

984 54 0
                                    

   Tana tsaye ita bata ce ya shigo ba kuma bata rife 'kofar ba.

"Can I come in?" Ya tambaya.

    "No" Ta girgiza kai.

    "OK,then I will wait for you outside"

    "Me..? "

     "Yes ,you're following me home"

      "I will not"

       "Stop wasting your time,just hurry up and park your things"

       "Laila!" Tajiyo Mami ta kirata.

       Sauri tayi ta bar gun ta tafi."Naji shiru,waye?

      "Uh..Amjad ne"

       "D'aukan ki yazo yi kenan?"

       "Mami nifa.."

        "Ke mey?,kinga ki shiga ki shirya kayanki"

       A kasalance ta shige d'aki,cikin sanyin jiki ta soma shirya kayanta  kamar mara laka a jiki.Hijab d'inta ta d'akko ta zirma ta ri'ke niqab d'in a hannu ta fito d'ayan hannun ta ri'ko akwatin.

     "Kin fito?"

       "Uhmm" Ta amsa.

        Su Maryam suna daga d'agi suka fito,ganin Fauzan yasa ta fad'in."Mami dan Allah Fauzan ya bini".

      "A'a ba yanzu ba,se anyi hutun makaranta"

      Ita tama manta yau Sunday,tana jin haushi ta fita su Maryam suka rakota har bakin mota,Amjad yana ciki yana jiranta.Da kanshi ya fita ya taimaka mata tasa kayan a baya,kafin ya koma motar ta rigashi shiga.Niqab dake ri'ke a hannunta ta d'aura a fuska ko idanuwanta ba'a gani,jin alamar ya shigo motar ta kawar da kanta window.Har suka hau titi ba wanda yayi magana ,sede lokaci-lokaci yana kallonta.Suna isa gida tayi tafiyarta ko kayan bata bi ta kansu ba,key dake jakarta ta ciro ta bud'e 'kofar.

      Sama ta haye direct d'akinta ta shiga ta rufo 'kofarta.

      "An dawo Prison"Ta fad'a a fili.

      Knock!knock! Tajiyo bugu,handbag d'in ta ajje sannan taje bud'ewa.Amjad ta gani ri'ke da akwatinta,jira take taga ya mi'ko mata amma shiru.

       "Remove this from your face" Yayi nuni da hannunsa.

       "I wanted it this way"

        "And I don't like it"

         "But you don't wanna see ugly face"

        Se yanzu ya tuna ,dariya abin ya bashi dan shi ya mance ya fad'a.Seda ya d'an murmusa tukun yace"So now you believed you're ugly?"

     Komawa tayi cikin d'akin ta barshi a tsaye gun, gefen gado ta samu ta zauna tare da ciro wayarta cikin jakarta.    Akwatin ya ri'ko ya shigo da ita d'akin daga gefen gado ya ajjeta."Answer my question "

      "Did you believed?"

       An d'au mintina a haka ita bata amsa ba shi be fita ba yana tsaye a kanta.Laila data gaji da zaman hakan tashi tayi ta wuce bathroom kafin ya farga ta rufo 'kofar.

      "Laila!" Ya kira sunanta.

       "I'm not going anywhere until you answer my question?"

         "Shiru tayi kamar ba jinsa take ba,niqab d'in kuwa ta yaye shi tana tsaye jikin 'kofar tana jira ya fita.

      " Laila,can't you hear me? talk to me"

AMJAD(Completed)Where stories live. Discover now