Laila at side
8:46pm,mutanen dasu ka kai amarya ba wani yawa ne dasu ba,cikin 'kan'kanin lokaci kowa ya kama hanya se Bahijja da Maryam su d'in ma ba zaman sukai ba 9:30pm nayi suka tashi zasi tafi,Laila se ro'konsu take kar su tafi dole ta ha'kura tana ji tana gani suka tafi.
A take ta fara jin tsoro jin tsit,ganin da gaske ta bar gida ta sake saka wani kukan har seda ta gaji kanta ba abinda yake se ciwo.10:03pm ta gani lokacin da ta kalli agogon dake d'akin,se yanzu ta kalli ma irin d'akin ta waiwaya can ta waiwaya nan duk irin kyawun d'akin da kayan dake ciki ba birgeta yayi ba komai duhunsa take gani,ganin lokaci yana sake ja ta tashi.'Kofa data gani daga can side na d'akin ta nufa ,koda ta murd'a taga bathroom ne 'kayatacce,seda ta dawo ta bud'e wardrobe ta dubi wata doguwar riga na bacci har 'kasa ta d'akko.
Hijab ta soma lalubowa amma bata gani ba,wani mayafi ta samu mey d'an nauyi ta d'akko ta shiga bathroom, bayan data samu gu ta sa'kale kayan seta tsaya dube-duben bucket na wanka.Babu shi ba alamarsa haka buta ma balle kuma mod'a.
"Mtchww!" Tayi tsaki.
Jacuzzi ta tsirawa ido tana tunanin ta ina zata soma amfani dashi, bathtub d'in ta samu ta 'ko'karta ta had'a ruwan tana la'kai-la'kai kamar bazata shiga ba,se can ta samu ta shiga ,d'aya daga cikin shower gel d'in ta d'akko da sponge tayi using, se bayan 17min tukun ta fito already ta zira rigarta sauran kayan kuma ta ninke su tasa a wardrobe.
Kan mirror ta duba wayam ba kayan shafawa,se can data duba drawer tagansu a jere.Mayukane wanda bata ta'ba shafasu ba,d'aya-bayan d'aya ta bisu tana karantawa yawanci lighten lotion ne da'kyar ta samu wani mey dama dama tukun ta shafa ita wai bazatai bleaching ba😂 komai ta maidashi muhallinsa ta dawo kan gadon ta zauna tare da d'ora hannayenta kan gwiwoyinta.Se yanzu tunanin wayarta ya fad'o mata ,mi'kewa ta sake yi ta bud'e wardrobe d'in daga 'kasan kaya ta d'akko ta kamar inda Maryam ta ajje mata.
"Toh wa zata ma kira?" Ta tambayi kanta.
Wata zuciyar tace kiyi game,aiko snake ta hau yi lokaci yana taja.
Amjad
Mom da ta shigo d'akinsa dan tana da tabbacin be tafi ba ,baki ta saki tana kallonsa yana kwance abinsa bacci yake kamar ba gobe.Ba halinsa bane bacci da wuri amma dan wula'kanci yau shine tun 9:30pm ya kwanta har 10:36pm.
"Amjad"
Seda ta 'karasa tai tapping shoulder d'insa tukun ya d'anyi motsi.
"Amjad,wake up!"
"Mom what?"
"Do I have to tell you?"
Yana la'kai-la'kai yatashi zaune,yana wani mirza idanuwa.
"Amjad, do I have to tell you what to do ,it's almost 11pm.."
"Mom you're sending me away,can't believe it you're sending your own son"
"No I'm not, how will I send m beloved son away ?"
"I'm tired I need to rest"
"Rest!" Ta maimaita ,dariya ma abin ya bata tana kallonsa.
"Your Dad doesn't know you're here"
"I gerrit ,don't worry I'm leaving now"Ya fad'a tare da mi'kewa.
Kallo kawai ta bishi dashi tana girgiza kai,watsa ruwa yayi ya fito ya saka wata black T-shirt mara nauyi tare da black jeans.Dad yana d'aki besan abinda ake ba har Amjad ya fito,Mom har bakin mota ta rakoshi su Shaheed daga nesa bakin 'kofa suna waving hand yadda sikeyi za'asan cewa na tsokana ne shide banza yayi musu Mom a cikin ranta tana jin zafin rabuwa da d'anta kawai de daurewa take.