Chapter 20

910 55 1
                                    

      Kan kujera ta samu ta zauna tana sake gyara zaman mayafinta data yafa kanta.

      "I thought you run away" Taji ya fad'a.

       Shiru tayi bata ce komai ba tana hangen handbag d'inta dake kan drawer,mi'kewa tayi daga zaune ta taka inda jakar take ta ciro wayarta ta dawo ta zauna.

      "Where is my phone?" Ya tambaya ganin ta ciro tata wayar a jaka.

      Tuna inda ta jefa wayar ta shiga yi dan tun sanda aka dam'kamata a hannunta sanda tazo asibitin.Mi'kewa tayi daga zaune ta shiga duba akwatin kayansu ta bud'e can ta bud'e nan can ta gano ta 'kasan akwatin.Tana ri'ke da wayar ta 'karasa gadon ta mi'ka masa."Thank you".Ya furta.

       Suna zaune d'akin shiru bame magana nurse ta shigo,kai tsaye ta wuce inda yake ba tare da ta lura da Laila ba.

      "Amjad Mu'az,sannu koh"

     Alluransa da ake masa ta had'a ta bud'e carnula ta tsiyaya,se magani data mi'ka masa bottle of water data gani kan drawer side na gadon ta d'auka ta tsiyaya a cup a mi'ka masa se wani 'kwar'kwasa take."

      Se lokacin ta waiwayo ta kalli Laila dake latsa wayarta."Ke ki biyo ni ki kar'bi wasu magunguna nashi"Ta wani kalleta a wula'kance.

      Laila tajita sarai amma jin tace 'ke' yasa ko d'ago kanta batayi  ba balle ta kalleta.

     "Baki ji bane" Ta matso inda take.

      "Ke naji kin anbata kuma a nan d'akin ba mey suna ke" Laila ta fad'a bayan ta komo da kallonta kanta.

    "Ba irinku ya dace kuke jinyan mutum ba dan baku san darajar wanda kuke jiyyar ba," Tana gama fad'ar haka ta fita ta bar Laila.

     Ranta in yayi dubu ya 'baci ,duk wannan uban zaman da take sha a asibitin nan shine zata fad'a mata 'bakar magana.

     "What did she said?" Ya tambayi Laila.

       "Nothing" Ta amsa bata ko kalleshi ba.

        Gida'a kai yayi dukda be aminta da abinda ta fad'a ba dan yaga sauyin yanayin fuskarta fiye da da.Wayar ma ajjeta tayi dan tsabar takaici ta kasa yin abinda zatai.

      "Laila I'm hungry" Taji yayi magana.

       D'agowa tayi ta kallesa nan Mom tace yaci abinci amma ya'ki shine yanzu zece mata wani zeci abinci.A hankali ta tako zuwa inda warmer d'in yake ta samu plate ta ziba masa pasta had'e da  sweet creamy potato sauce  ta samu spoon ta d'ora ta mi'ka masa, ganin be kar'ba ba ta ajje masa kan gefen gadon ta koma ta zauna.

      "Laila can't you see ? I can't use my hand to eat"

    Se lokacin ta d'ago ta kalli hannunsa na dama  dake nad'e a plaster."Kaci da hannun hagun".

       "Laila it's not good to eat with left hand"

      Sekace ba shine mey cin abinci da hannun hagun ba wata rana."Laila I'm starving "

     Cikin sanyin jiki irin nata ta 'karasa,a gaskiya bazata iya zama gefensa ba kamar yadda taga Mom nayi, tsayawa tayi ta d'auki plate d'in  a tsayen ta d'ibo a spoon ta mi'ka masa.

      "I can't take this while you're standing"

        "It's ok for me"

         "But it's not ok for me,sit"Ya fad'a.

          A raku'be ta zauna daga gefensa dan wajen ba wani space ne dashi ba duk yadda takai ga no'kewa seda ta ra'bi jikinsa abinda bataso kenan.Bata bari sun had'a ido ba ta mi'ka masa, yana sane ya 'bata lokaci kafin ya kar'ba har hannunta ya gaji.Dayaga ya kusa 'koshi inde ta d'ibi abincin seyace lomar tayi masa girma har seta rage zeci.Tana gama bashi ta mi'ke da sauri.

AMJAD(Completed)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang