https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~**_~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘ILHAM💍💘💘
💘💗( LOVE STORY)💘
In tha name of Allah d most beneficent d most merciful,praise be to Allah ,master of d day ov judgement
Story by
Mamie,maryam(amatullahi) and aisha kabeer
Written by mamien umar&Abdul
Wattpad @hassanatafarki
Bismillahi rahamanil raheem👏🏼
Ina mika sakon godia zuwa ga masoyana , yan uwa , da abokai nah masu goya man baya ,
Ban manta daku bah maryam (amatullahi),Aisha kabeer ,anty maryam tafarki,anty sajida tafarki ,Ina mika sakon godia zuwa ga yan golden pen writters association, 👏🏼
Na sadaukar da wannan page gareki Qawata @mijina abun alfaharina
P🅰GE 4⃣
Misalin karfe 10 na dare mishaal ne na hango kwance yana ta tsaki babu abunda yake gani sai lokacin da ilham take zuba masa coke ajikin kayansa mtswww, sai tunanin wane irin hukunci xai mata,
A haka har bacci barawo ya daukesa,
da safe misalin karfe goma na safe bodyguard dinsa na hango tsaye bakin kofa suna jiran shi ya karaso domin yau yana da lecture,
a hankali na yake fito duka maikatan sai zubewa suna kwasar gaisu amma ko tsayawa kulasu bai yi bah sai daga musu hannu yayi,ya wuce da gudu bodyguard suka bude masa bayan mota ,
yashiga suka tada motocinsu sai skul,bayan ya shigo skul sai ga kiran fahad yadauka sai naji yana cewa ,dgsk kakeyi okey idan na fito daga skul mu hadu a gidana kawai ya kashe wayar .
Ilham kuma yau bata da lecture tana hostel ,tana assignment a system dinta kausar CE naga tafito daga toilet tana cema ilham nifa yunwa nakeji ki tashi muje ayla restaurant ,
tsaki kawai naga tayi tana cewa acici yau idan ban tashi bah bazaki bari na karasa assignment dina bah ,
Bayan mishaal ya fito daga lecture sai ga fahad yazo yana fadin ynx gida zamuje ,
mishaal yace aa mu wuce ayla restaurant kafin mu wuce gida don yunwa nakeji ,
Ayla restaurant ilham ce na hango zaune suna cin chips da coke ,sannu a hankali nafara jiyo wani kamshi Mai dadi koda nake dago kaina sai naga Ashe mishaal ne shida fahad ,
da gudu na maikatan restaurant din suna karaso naga sai ba mishaal girma suke ,a kaisu table na manyan mutane bayan kamar minti biyu naga yayi waya yana cewa akawo masa margoogat da laban ,sai yake tmbyar fahad mi za'a kawo maka, sai yace kawai luqiamat and Arabian coffee bayan sun kare kawai ya daga idonai wa zai gani ilham kawai yayi wani irin murmushi,irin murmushin mugunta dinan ,sai a idon kausar ,ke duba mutuminki yana miki murmushi kodai kiyayya zata koma soyayya ,take ilham ta tofar da yawu take cewa Allah ya tsaran narasa Wanda zanso sai wancan mumunan mai kama da yan daudu ,
nikam nace kai ilham kiji tsoron Allah ai ko makaho ya taba mishaal yasan cikaken namijine kuma kyakyawa ,Daga nan mishaal da fahad suka kama hanya sai gida bayan sun shiga gida sai ga kiranan umar da aliyu suna cewa suna kofar gate ,
sai yace Ku karaso garden dina , bayan kmr minti 30 suka kira gamu mun karaso ,ranka yadade , yace Ku shigo kawai ,ana suka isko fahad da mishaal zaune akan wata hadadiyar kafet hmmmmm wato gaya muku yanda gurin yake baya ma faduwa domin gurine Wanda ke dauke da kayan lambu ga flowers masu kyau ta ko ina ,nikam sai dai nace tab!!! Kudi na aiki wannan guri,
Bayan sun zauna suka gaidasa sai yake cewa ina aikin da nasa Ku suka ai mun gama ba tarihinta bah harda number wayarta mun samo ga komai nan a rubuce ,sai yace kuna iya tafi Ku turoma fahad da acct numberku domin ya turo muku kudin aikinku ,suka ce mun gode suka wuce ,
Mishaal ne yace ma fahad dauko ka karanta mana ko ita wacce idan ma babanta wani governor toh a yau zai sauka daga kan mulkinai ,Bayan fahad yagama karanta tarihin ilham tunda ga farko har karshe ,
a take mishaal ya mike tsaye yana cewa dama wannan yarinyar ba diyar kowa bace ta dauko ma kanka abunda yafi karfinta,dama Ashe da scholarship taxo skul dinan kuma ta karkashen mahaifina taxo, dama Ashe diyar talakawa ce diyar teachern secondary school, hahahahah lallai wannan yarinyar bata San ko ni wannene bah amma xata san wanene mishaal ,
Fahad kasan mie acikin hukuncin da zan mata idan taxo nan ta duka taban hnkr xan iya rage mata su ,kira man numberta ynx nan ,Ilham kwance take bayan sun dawo daga restaurant sai taji wayarta tana ringing bata tsaya wani duba number bah kawai tay picking ,sai kawai jin tayi ance dama ke ba kowa bace kika yi kokarin shigo rayuwata ,hmmmmm dama Ashe ke diyar middle class people ce ,dama ke Ashe ubanki malamin makarnta ne dake cikin wani kazamin unguwa , Ashe uwarki ba kowa bace sai yar cirani wallahi!!! Tunda kika shigo rayuwata kikasa na kasa bacci Dan tunanin irin hukuncin da zan miki sai na lalata rayuwarki da ta iyayenki sai nayi sanadiyar ruguza Rayuwarki, ilham naji ta daka masa tsawa ,kai dan Allah dakata jahili, wawa mai Kadauki kankane zaka iya man abun a bunda Allah bai man bah toh tsaya kaji bana tsoronka ,in banda kana jahili an gaya maka dubarar ka ko wayyonka yasa ka kasance a yanda kake mtswww toh tsaya kaji da mai kudi da talaka duka allah yayi su,
kayi duk abunda zakayi ko kana daukar ina tsoronka, in banda kake jahili ai da talauci da arziki duk na Allah ,kuma da kake ceman diyar talakawa ,alhmdullahi ni ina alfahari da kasan cewa a haka ,
koda yake bari nadena wahalar da fatar bakina Dan nasan ko islamiyya ba'aje bah Dan daga yanayin mah an San kai baban jahiline ,jaki kawai har zaka ce zaka lalata rayuwata ,kai in banda tsautsayi mizaisa ma nayi magana da yaro irinka Wanda ko magana bai iya kai ko acikin dabob,i kai baban dabbane mtswww kawai ta kashe wayarta , ta cire Layin ta saka wani ,
Mishaal bayan ta kashe kiran babu maganr da yake Nana tawa sai Kalmar jahili, jaki, dabba,sai kuma naga ya wani shegen murmushi.
Ilham ce zaune kan gadonta tana kuka babu abunda yafi yima ciwo irin xagin iyayenta da yayi , sai kausar ta shigo dakin ta isko aminiyarta tana ta kuka take tmbyata miya faru halan ko wani Abu ya faru a gida ,sai ta girgixa kai tace aa kaina kawai ke ciwo ,sai kausar tace Allah yasawake amma kidena kuka nan kada kijawo ma kanki ciwon kai,
Mishaal ne tsaye shida fahad ,fahad na fadin kai amma yarinyar nan bata da hankali tako San wannne kai ni wlh nadauka hnkr zata baka ,gsky ya kamata kan koya mata hankali,sai mishaal yayi murmushi yace ka Kyaleta badai ina da tarihin gidansu bah toh insha Allah sai nasata tayi kuka da idonta sai ta duga tana bani hnkr kuma ina so ka fadama bodyguard dina ,inaso daga gobe su fara bibiyarta domin inaso ayoman kidnapping dinta a kawoman ita nan gida na,
Sai fahad yace insha Allah zaayi yanda kace .Shin ko mie zai faru idan akayi kidnapping din ilham?
Shin ko minene dalilin da mishaal yakeso a Sato masa ilham?
Shin miyakeson ya aikata?
Shin ko wanne irin hukuncin zai mata?
Shin ko ilham zatayi Dana sanin abunda ta aikata?Sai mun hadu a page na gaba
Samun waddan answers din sai mun hadu page na gaba,#/ vote
#/ comment
#/ share
#/ follow
@ wattpad_hassanatafarki