https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~**~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
💘💘💘💘💘💘💘💘. 💘💘💍ILHAM💍💘💘💞💞(LOVE STORY)💞
in the name of Allah d most beneficent d most merciful .praise be to Allah ,master of the day of judgment,
Written by mamin Abdul&umar
Story by maryam (amatullahi and Aisha
Wattpad@hassanatafarkiIna godia gareku masoyana kuma nagode da adduarku gareni ,
Ina miqa sakon godia ta zuwa gareku members din golden pen writers association,
na sadaukar muku da wannan page din saadatu (waleedar mama) and Aisha lawal(ayoush)kuyi yanda kukeso dashi
Bismillahi rahmani raheem
P🅰GE 8⃣
Bayan kwana biyu da faruwar haka su ilham suka fara exams,
Mishaal ma sun fara Dan haka ko wanne daga cikinsu baida lokacin wani , amma ilham da kaganta kasan tana cikin damuwa Duk da tana boye damuwae Dan batason kausar tasan da maganar ,Yau ta kama Saturday gaba dayan su yau basu da exam , mishaal na hango kwance saman bed dinsa , a hankali yafara bude idonai , sai naga ya danna wani Abu ,
Maaikata mata Nagani sun shigo suna good morning sir , daga masu hannu kawai yayi, inda sabo ai sun saba da halinsa , wata naga ta shiga toilet dinsa ta hada masa ruwan wanka, wata kuma ta dauko masa rigar wankansa,
Ko ya kama aikinsa bayan yafito daga wanka , wata naga ta shigo ta fara gyara masa kansa, bayan ta gama ta fita ,
Bayan 30mins ,mishaal na hango yasha wata dakakiyar shada ,
Tsaya na Baku labarin Kyan da yayi bata lokaci , wata kujera naga ya zauna sai ga wata balarabiya ta shigo , sai naga ta bude wata locker hmmm na dauka company din turarene duka udu ne , nan ta fara fesa masa take wani sanyayen kamshi yafara tashi daga jikin mishaal , sai naga sai murmushi take masa, shikuma sai wani yatsina fuska yakeyi kmr yaga kashi,Ilhma na hango kwance saman bed dinta tana bacci, kausar naga ta shigo tana fadin bestie ki tashi mana baccin ya isa haka mana, tashi naga ta fara yi da addua a bakinta ,
Kawai toilet naga ta wuce bayan tayo wanka , ta shirya sai naji tana fadin toh ai sai ki tashi muje acici, anan ne na fahimci acici wato kausar yunwa take ji,
Bayan sunje sunci abinci sun dawo hostel wayar ilham naga tana ringing wazata ga yana kirarta inba babanta ,
Cikin nutsuwa naga ta dauka tana salama,
Baba naji yana. Cewa yata ilham ya makaranta ,alhmdlh baba , masha Allah ina fatan dai bakida matsala Koh, eh baba babu , toh Allah yayi muku albarka, ameeen baba,
Ilhma yaron da kika turo wurina yazo kuma yau kwana hudu kenan da daura aurenki dashi , kuma nayi farinciki da yakasance Dana gurin mutum da yadaukeni kmr Dan uwansa bazan taba manta Wa da abunda mahaifinsa yaman aruyuwa bah , Dan haka idan kika dawo zaayi biki, sai ki tare idan hutunku ya kare Ku koma tare ,
Yata ina Fatah dai ban miki shishigi ga rayuwaeki bah,Aa wlh baba ko daya babu ,ai baba Duk abunda kakeso nima ina sonai , fatana dai Allah yabamu zaman lpia , amin diyar baba Allah yamiki albarka, kema yabaki yara masu miki biyayya kmr yanda kike mana ,
Nagode sai anjima , toh baba ka gaida mama , toh insha Allah ,Ilham na gani tana kuka tana fadin Allah na rokeka kasa na cinye wannan jarabawar, lallai mishaal yacika mugu ,mayaudari, azalumi, amma wlh sai yayi Dana sanin aurena da yayi,
Mishaal na hango cikin mota yana , sai jin nayi yana magana a waya yana fadin inso kuje Ku kawo man ita ynx nan ,
.
Ilham ce bakin gate din skul tana jiran taxi yazo zata isko kausar a wani gurin shan iceream,
Kawai mota baka taga ta tsaya basu tsaya wata wata bah kawai suka saka ta amota, ilham naga sai bude ido takeyi taga mi suke nupi da itane , wani guri taga sun bi ,mi zata gani motocici na alfarma jere , fito naga tayi suka nuna mata wata mota Wanda Duk ta fisu haduwa da tsada,Tana shiga kamshin Wa zataji inba na mishaal bah,
Bude ido tayi tana mamakinsa , sai cewa tayi wai kai na tambyeka ,
Kodai aikinka kayi kidnapping din mutane , murmushi naga yayi , sai naji yace laifine Dan mutum ya sato matarsa ,
Wani.guri zamuje ,
Waya naga yayi yana fadin Ku koma gida ,yau ni kadai zan fita nida madam, kallonshi naga tayi shima kallonta yakeyi,
Kamar bazaiyi magana bah sai naji yace idan baki dena kallona da idonunki kmr na mayu bah zan cinye miki su dama bakisan bayan kidnapping bah harda cin idonun marar kunya inayi ,
Sai cewa tayi da alama kam,
Tsaki naga yayi yana fadin zan gyara miki zamane,Sai naji tace mudai gyara ma juna ,ido naga ya bude yana mamakinta ,
Cikin xuciyarsa naji yana cewa wai ita wannan yarinyar bata da tsoro ne ko kuma rashin kunya ta mata yawa ne,
Tsaki yayi ya tada mota sai wani hadaden hotel wanda sai Wanda yaji kudi yake sauka agun sbd tsanin haduwarshi,Ilham naga ta fido ido tana fadin Kodai dagsk yana yankan mutane ne na shiga uku nikam ilham yau tawa ta kare,
Jin nayi tana fadin.mishaal Dan Allah kayi hnkr wlh wasa nakeyi , Dan Allah kada ka maidani makauniya nashiga uku na nikam yau sai ihu take mai,Shi bai masan inda zancen ta ya dosa bah ,
Daure fuska naga yayi ya daka mata tsawa, ke dakata malamaa,
Idan da ni mai yankan Kaine bazan kawoki hotel bai ,Dan haka ki fito mu shiga ciki , sai naji tace muje ciki in maka mi, wai tsaya mima zamu toh anan, sai jin nayi yace ciki xan miki, take cikin ya murda sai naji tace wai kai mikake nupi danine , toh bazan shiga bah,
Okey haka kikace , kada ki manta da mahaifinki, kuma ke ynx halali nace , Dan haka kifito ko kuma kinsan sauran,Suna shiga cikin hotel din maikatan
gurin naga sai girma suke basa , sai wani ya taso yana fadin ranka yadade ga makulin part dinka, okey kawai naji yace ya wuce ,Wata hanya naga mun bi
Sai mamaki nakeyi toh shi wanene a hotel din da ake girmama sa haka harda part garesa , babu mai bani wannan amsar
Wani guri naga mun shiga Ashe falo ne hmmm zo kuga haduwar falon baa ma magana,
Jin nayi yace ki zauna ko ki tsaya duka matsalarki CE kawai ya wuce warsa wata hanya Wanda nake kyautata zaton bedroom ne ,Zama nayi abuna ina ta tsaki , pics na hango nashi shida babansa da twinsis,
Bayan Minti goma sai gashi ya fito zama naga yayi , yana fadin ke yama sunanki, shiru naga tafi tsawa ya daka mata ke jakar inace ina tmbyarki kiman shiru , ya sunaki, ilham ,mtsw ilham inaso kisani na kawo ki nan sbd ba kori maaikata na masu mani tausa ,
Dan haka daga yau idan inason tausa ke zaki dinga zuwa kina man , dama bana son mata suna taba man tsadaden jikina , Dan haka ina fada miki daga ynx kece da wannan aikin ,
Sannu a hankali hatta masu saka man wanka zan koresu kinga dawowa gidana ya kama ki , sbd ban aureki Dan komai bah sai Dan ke baiwata ce siyenki nayi , Dan haka dole kiyi duk abunda nakeso,Sannan kisani ni bana daukarki macce Dan keda namiji nakuda banbanci,
Dan haka ki tashi ki fara aikinki ,
Ilham naji tana cewa daka mishaal kai har kana bakin da zaka ceman namiji,toh ni bana kallonka a matsayin namiji ma Dan kai kama kakeyi da yan daudu,
Kuma dakake cewa zan zama baiwa dama aini baiwa ce domin ni baiwae Allah ce ba wai da wani bawa Irina bah,Kuma tausa dakake magana akai bazan yi bah kaje cen kasamu yan iskan Matan dakenson taba wannan kazamin jikin naka, Dan ni nafi karfin na taba jikinka ,kuma da kakeman barazana da mahaifina kaje kamasa duk abunda zakayi , ai Allah na nan kuma yana bayan mai gsky,
Mishaal naga yatashi ya dauketa da mari yana wani huci sai jin nayi yace wlh sai kin zama baiwa ta kuma.wlh sai kinman tausa a cikin hotel dinan ko kuma nidake babu Wanda zai fita daga gurinan domin wannan hotel din nawane , kin kowa zan iya yin duk abunda nakeso, idan kina bukatar komawa hostel kafin abokiyarki tafara zargin kin fara karuwanci domin wlh ko shekaea goma zamuyi bazaki fita bah nima haka ki zaba da tausa da kare mutuncinki sane kika fi so , idan kin yanke tsawara ki sameni a dakina ,
Shin ilham zata ma mishaal tausa kuwa?
Shin kausar zata San da auren sirrin da akayi tsakanin mishaal da ilham?
Shin ilham zata koma baiwarsa kmr yanda ya fada,?
Shin ko mishaal zai fara son mai sifar maza ?
Sai mun hadu a page na gabaTaku a kulum hassana tafarki ,
#/vote
#/comment
#/share
#/follow
Wattpad@hassanatafarki