mujarrabi
By
Zubaina Ibrahim.Bissmillahi rahmani rahim Alhamdulillah ala kulli halin Alhamdulillah ala ni'matil Islam.
Sai juyi take da alamar baccin da take ba mai dadi ba ne Don mafarkine da ta saba yi in dai ta kwanta bana kowa ba Illa na mahaifiyar ta Wanda wani lokacin ta ganta cikin farin ciki wani lokacin kuma akasin sa Wanda in da sabo ta Saba da su Tun bata san itace mahaifiyar ta ba har dai ta fara tambayar mami.tun tana karama mahaifiyar ta tarasu a wurin haihuwa Wanda da ita da abunda Ta haifa ya koma sai zamanta ya koma wurin kanwar mamanta Wanda suke cewa mami. Mami macece Mai hakuri da hangen Nisa bata da son hayaniya ga saukin kai in dai ka zauna da ita. macece mai yawan ibada Wannan da kyautatawa na kasa da ita. Haka dai tayi ta juye juyen har akayi kiran assalatu Wanda ya tayar da ita dama Batayi barci da wuri ba ta tashi da Salati abakin ta, ta shiga ban daki tayi wanka Sannan tayi alwala tayi sallah ta sake komawa kan gado ko ta samu ta Runsa kamin time din tafiya makaranta yayi, ta na ko kwanciya barci ya fara fisgarta taji an yaye borgon da ta rufa da shi da karfi ta San ba mai mata irin haka sai Khadija ba tun Yau ba Khadija bata son xaman ta a gidan. Kullum Sai ta mata gori Na yau da ban na gobe daban kullum Sai sunyi Wannan ma don Mami na shiga tsakani ne shiyasa yayi sauki kuma Mami na son Khadijah sosai don suna shiri da maman khadijan kamin rasuwar ta. Don baban su Khadija Wanda muke Kira da Abba matan sa uku hajiya Maryam ita ce uwar gida kuma ita ne Mai yawan yara. Yaranta biyar Abdullah, Umar da zuwaira Sai Amina da auta khalil sai Mami ce ta biyu yaranta uku Sadiq usman da Fatima Wanda mu ke Sa o e ne Sai maman Khadija Wacce a wurin haihuwarta ta koma ga mahalliccin ta Sai zamanta ya dawo wurin mami da ma Tana shiri da Mami sosai kamin rasuwarta Wanda kuma hajiya babba ta tsana ta Don yadda Alhaji ke nuna rawan Kai akanta Don Allah yayi mata baywar kyau ga Gashi har gadon baya kuma ta na daukar wanka sosai da yake ita Amarya ce Wannan ke Kona ran hajiya babba.
Vote and comment pls
YOU ARE READING
MUJARRABI.( Completed)
Randomlabarin wata yarinya da ta rasa mahaifiyar ta Tun tana karama. ta taso a wurin kanwar mahaifiyarta, (mami) ta nuna mata kauna sosai sai qaddara ya shiga tsakanin ta da wacce ta tsane ta rayuwa ya juye mata lokaci daya. Ta fuskaci qalu bale kala ka...