part 27

245 26 7
                                    

MUJARRABI

BY SNOW WHITE

Mujarrabi fans this whole  page is for you. Thank you sweets hearts.

In the name of Allah the most high and merciful

Quran: Fatir  (35:13)

يُولِجُ ٱلَّيْلَ فِى ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِى ٱلَّيْلِ وَسَخَّرَ ٱلشَّمْسَ وَٱلْقَمَرَ كُلٌّ يَجْرِى لِأَجَلٍ مُّسَمًّى ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمْ لَهُ ٱلْمُلْكُ وَٱلَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِهِۦ مَا يَمْلِكُونَ مِن قِطْمِيرٍ

He merges the night into the day, and He merges the day into the night; and He regulates the sun and the moon, each running for a stated term. Such is Allah, your Lord; His is the sovereignty. As for those you call upon besides Him, they do not possess a speck.

__________________________________

Muna zaune a park nida ya Abdallah wanda yazo kwana biyu da suka wuce sai hiran mu mukeyi tamkar yadda kasan saurayi da buɗurwa yanzu haka ba abunda bansani ba game da rayuwar sa haka shima ba abunda bai saniba ta gefena ko mai ya faru sai mun labartawa juna bama ɓoye komai ni tuni na manta da wani zancen abokin sa da yake sharewa fage shima yanzu ya daina magarsa sha'anin mu kawai mukeyi inka ganmu sai ka rantse mun fi shekara da fara soyayya ɗon wani shakuwa ce mai ban mamaki ya shiga tsakanin mu cikin lokaci kankani

Yanzu haka jira kawai nake ya furta min kalmar so,  in bada kai bori ya hau.tuni nasan na fada tarkon soyayyar sa don alamomi duk sun nuna kuma iya binciken da nayi da kuma tambayoyin da nayiwa mutane duk abu daya suke ce min wannan ai alamomin sone, gashi duk abunda nake karantawa a novel ina jin su yanzu game da abdallah.irin yawan tunaninsa,faduwar gaba in na ganshi,bana iya kalon kwayar idon sa don ji nake kamar tsokar kibiya ne cikin idona ko Kuma kamar ana diban wasu abubuwan daga idanun sa ana sawa cikin nawa uwa uba yawan hirarsa da nakeyi yanzu.

Nifa yanzu yana gayamin bazan ɓata lokaci ba zan amsa masa kawai don banga abun jira ba ko wani jan aji ina jinshi sosai cikin zuciyata da gangan jikina. Yanzu jina nake kamar yau aka haifeni na fara rayuwa don duk tsawon rayuwata ban taba jin abubuwan da nakeji yanzu cikin zuciyataba ina jina daban kamar wata sabuwar halitta.

In muna waya tamkar karmu ajiye hakanan in yazo kulawan da muke bawa junan kamar mu haɗiye juna kawai mu huta, don ya abdallah na kiyaye duk wani abunda zai bata min rai haka nima duk abunda ya nuna bayaso da sauri nake Barinsa.

Ya daukeni yau muna shan yawo acewar sa yana son muyi mgana sirri yasan in a gidane za'a takura mana dasa ido shiyasa yace muje park, mun fara biyawa ta ice cream joint, inajin ya manta an hanani shan sanyi inata jin ɗadi yau zansha ice cream har ya sayi guda biyu, ya mika min.na mika hannu zan karba ,saiya janye hannun shi yana girgiza kai

Tare da cewa no, no no

Ai na manta an hanaki shan sanyi

Na turo bakina gaba "nace yaya don yau kawai ai ba abunda zai faru.

Ya girgiza kanshi bazaki shaba sai kin warke haka nan ya zauna yasa chokali daya a bakinshi tare da rufe ido yayi hmmm kai dadi ya wuce wata

ni kuma sai kallon sa nake ko zai tausaya min ya ɗan bani in taba.

Ya sake sa spoon din ya diba sai yace

"Kina so"

Na d'aga kaina tare da cewa ehhh

Oya to buɗe baki in baki one spoon

Na bude baki don akwai ni da son zaki na rufe ido ina jiran inji ice cream abakina me zanji sai sanyi ice cream a tip of my nose maimakon baki a hanci ya diga min.

MUJARRABI.( Completed)Where stories live. Discover now