*MUJARRABI* 1⃣8⃣
*By snow white*
*Whattpad:@ zubainaibrahim.*
In the name of Allah the most high and merciful
Qur'an: Al-Baqara (2:42)
وَلَا تَلْبِسُوا۟ ٱلْحَقَّ بِٱلْبَٰطِلِ وَتَكْتُمُوا۟ ٱلْحَقَّ وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ
And do not mix truth with falsehood, and do not conceal the truth while you know.
----------------------------------------------------
Abdallah Ya iso cikin asibitin ya samu abokin aikin nashi yana tsaye gefen shi matar shi ce tsaye mai juna biyu don dama abunda ya kawo su asibitin kenan.
cikin ta ya kwana yana mata ciwo shine suka zo ganin likitan ta wanda yace musu is normal ba wani damuwa kan baby ne ke saukowa.
to sun fito zasu tafi, sai yaga wata yarinya ana turata a gadon marasa lafiya, ya kura mata ido sai yaga kamar ita ce wacce aka tura mishi hoton ta jiya.
shine yace bari ya kira Abdallah yazo ya gani ko itan ce.Abdalla ya shigo asibitin ya kira shi akan ya iso.
sai yace masa yazo wurin reception.
Yana shiga da su ya ci karo.Aboki ya dai ya gajiya ashe kai da madam ne.
Eh wlh.
Sannu madam ya hakuri damu ya nauyin jiki kuma.Cikin murmushi tace Alhamdulillah!
Abokin ne yace kin ganshi ko madam yaki yin aure har yanxu gashi muna hanyan samun baby na 2 ya zauna har ya zama tuxuru.
Nan Abdallah ya kai mishi naushin wasa yace ni kake kira da tuxuru?
Karki ji maganar shi madam kwanan nan za'ayi da yardar Allah .kai in natashi ma hudu zan auro lokaci daya sai in huta da gorin ku.
Nan ko suka tuntsure da dariya gabadayan su.
Kamar gaske let go back to business.
Abokin ne mai suna yasir ya fara bayani kamar haka,
munxo ganin likita ne sai naga wata yarinya kamar wacce ka turamin hoton ta wacce ta ɓata kuke neman ta to naga ana turata a gadon marasa lafiya kuma da alama daga Intensive care unit (ICU ) aka fitar da ita to sai naga ta min yanayi da wannan daka turamin hoton ta a waya,To a lokacin madam ta je karbar magani ni kuma ina waya da kai to ban san ta ina sukayi ba sun bace min amma dai tana cikin asibitin nan don ta haka sukayi ya nuna gefen daman su.
" Abdallah ne yace Kai Alhamdulillah Allah yasa itan ce bakaji farin cikin da naji yanxu ba da samun wannan labarin"
Toh ta ina zamu fara neman ta daki daki zamu shiga ne ko zamu yiwa authority asibitin magana Sai su bincika mana ita cikin patient din su.
Gaskiya ni kar mu sasu bincike kuma yaxo ba itan ba ce fadin yasir.
Maganar kama akwai abun dubawa abokina
Yanxu dai Ga nursing station a chan muje mu nuna musu hoton ta ba zasu kasa saniba tunda sune suke attendin din patient.
Eh hakan ma yayi aboki.Nan suka je suka yi musu bayani amma fir nursis din nan sun ki magana sai da suka nuna id card din su na aiki don cikin su ba wanda yasa kayan su na soja a ranar.
To ganin dai su soja ne sai suka saurare suSukace basu san ta ba amma bari sauran su xo don sun je round check.
Bayan minti talatin sai gasu sun dawo
Duk kan su suka ce ba su santa ba don chanji suke yi basune masu kwana ba su da safen nan suka zo.Nan jikin su ya mutu murus, murnar duk ta koma ciki.
Sun juya zasu tafi sai ga wata sister mai shegen surutu ana ce mata sister barakah ta shigo dakin wai me ake tattaunawa ne babu ni aciki
Wata sis ce ta amsa da cewa neman wannan na cikin wayar suke ko tana cikin patient din mu.
In gani.
Nan aka nuna mata
Tace wannan fa kamar wacce Dr Ahmad ya kawo ne fa kwana biyu da suka wuce ai tana (ICU) don tun da aka kawo ta bata farfado ba.Inalillahi wa inna ilaihi rajiun shine abunda Abdallah ya rinqa mai maitawa cikin zuciyar shi har ya samu nutsuwa.
Sai ya tambayi nurse din ina Dr Ahmad din?Yana office
ki kai mu wurin shi.
OK muje
Sunje office din basu same shi ba akace yanxu ya shiga tiyata sai dai su jira.
Sai Abdallah yace ma yasir ya kai matar shi gida shi zai jira. sukayi sallama da yasir din matar shi kam ta gaji sosai ga juna biyu kuma.Yasir yace zai dawo in Ya ajiye ta a gida.
Abdallah kuma ya zauna jiran fitowar Dr.
Bayan awa biyu
Abdallah ne da Dr ahmad zaune a office din shi bayan fitowar shi daga tiyata. Bayan sun gaisa sai Abdallah
Ya nuna mishi hoton islam din da ke cikin wayar shi akan cewa kanwarsa ce ta ɓata ana nemanta kusan sati daya daya wuce ba a ganta ba amma wani yace ya gan ta anan asibitin da safen nan
Dr Ya karbi wayar sai yaga hoton yarinyar ne.
Tabbas wannan yarinyar tana asibitin nan amma cikin mawuya cin hali daman a ICU take dazu ne datafara motsi a ka mayar da ita ward.Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! kai Dr na gode na gode naji dadin wannan batu
matuqa.
Tsabar murna har da rungumar Dr yana ta jera mishi kalaman godiya. Dr dai sai mamaki yake yadda farin ciki ya wanxu a fuskarsa lokaci daya alama ya nuna ba karamar kauna yake wa yarinyar ba.Muje sai ka ganta
Nan suka shiga ward wurin da aka ajiye islam din a wani ke bantaccen daki ita kadai.
Yadda Abdallah ya ganta ya kusan yi kwalla in ba don shi soja ne ba da tuni yayi kwalla tsaban yadda ta bashi tausayi amma idon nan yayi ja tsaban bacin rai ,ta chanja kamar ba islam ba
Jikin ta rabin shi duk plasta ne ga hannun ta dake daure.Ɗr ne yafara bayani kamar haka kamar yadda kaji ko ka gani ni bansan taba amma kwana biyu da suka wuce ne na buge ta da mota sakamakon hawa titin da tayi cikin gudu ba tare da ta dubi hanya ba, nayi iya kokari na don in kauce mata amma Allah bai kaddara ba kawai ina tuqi sai na ganta tsakiyar kwalta
Kamar wacce aka jeho ta to dai ta samu karaya a hannu da ciwuka ajikin ta.
To tunda abun ya faru bata yi motsi ba shi yasa aka ajiye ta a (ICU) yau ne ta fara motsi shine nace a kawota nan don akwai alamun sauki atattare da ita.
Toh Alhamdulillah abun yazo da sauki ma tunda ba'a rasata ba
Abdallah ya sake cewa,
Dr abinciken da kukayi akanta akwai wani ciwo ne a jikin ta bayan na accident din don ɓata tayi ba musan inda take ba iya wannan kwanakin.Eh akwai.
Zare ido Abdallah yayi cikin tsoro kar a gayamasa abunda yake tsoron ji Kai insha Allah ma bashi bane.Dr ne ya dawo dashi daga dan guntun tunanin daya tafi.
Eh bincike ya nuna ta kamu da (pneumonia) ciwon sanyi kenan Wannan ciwon dai yafi Kama yara yan kasa da shekara biyar, kuma Tana kashe wa in dai ba'a samu kyakkyawan kulawa ba.
Amma Ita in ta kiyaye dokokin asibiti xata warke insha Allah.Toh Dr nagode sosai.
Yauwa Dr dai dai inane wurin da ka bugeta da mota.
Chan hanyar fita gari
Ikon Allah har chan aka kaitaToh nagode sosai Dr ba komai ai yiwa kai ne,
Yanxu dai sai a samu wata taxo ta zauna da ita Tunda angane 'yan uwanta kuma any moment xata iya farkawa Don yan xu komai nata ya dawo normal dama she is on oxygen.
Toh Dr nagode
Yauwa kuma a kawo mata abubuwan bukata.
Toh shikenan bari inje in dan saya mata abun bukata kamin inje gidan inzo dasu.
Sukayi sallama da Dr aka kira sis barakah aka bata hakkin kula da islam din kafun 'ƴan uwanta suzo.*Mami ishrat ce*✍
Vote, comments and follow.
YOU ARE READING
MUJARRABI.( Completed)
Randomlabarin wata yarinya da ta rasa mahaifiyar ta Tun tana karama. ta taso a wurin kanwar mahaifiyarta, (mami) ta nuna mata kauna sosai sai qaddara ya shiga tsakanin ta da wacce ta tsane ta rayuwa ya juye mata lokaci daya. Ta fuskaci qalu bale kala ka...