part 19

241 27 0
                                    

*MUJARRABI* 1⃣9⃣

*BY SNOW WHITE*

*Whattpad:@ zubainaibrahim*

He who becomes a Muslim does so in his own interest.
[Islamic Quote].

The most beloved deed to Allah is the most regular and constant even though it were little.
[Bukhari 8:471]

----------------------------------------

Tana zaune a palo gefen ta imad ne zaune yana home work, ranta duk a jagule yake tun kwana biyun da suka wuce, gashi imad ma ya tada nashi fitinan wai sai itace zata yi mishi home work abu goma da ashirin sun hade mata. Tana goda mishi home work din, in akwai abun da ta tsana bai wuce koyawa yaro karatu ba sai tayi ta mammake shi in bai gane abunda ta nuna masa ba.

To shima baya zuwa wurinta don baya son abunda zai taba lafiyar jikin shi.
To amma yau uban nashi yana fushi kuma yace dole tayi mishi kuma ya rantse in ta taba mishi ɗa sai ya saɓa mata. Tun randa ya buge mistiriouse girl, tun ranan suke samun matsala da shi har yau din nan don bata gane kanshi ba baya zaman minti talatin ba tare da yayi maganar taba jiya cewa yayi tazo suje asibitin ta ganta
Ita kuma taqi don bata ga alakar dake sakanin ta da ƴarinyar ba nan ko ya hau fushi har da barmata dakin.
Yau da safe kuma bayan awa daya da fitan shi aiki ya kirata a waya akan ta shirya zai zo ya dauke ta suje asibiti, ta kuma saka a dafawa yarinyar abinci don an fitar da ita daga(icu) ta kusan tashi don inta tashi ta samu ta sa wani abu abakin ta kafun anemi yan uwanta, kun dai san mutuniyar taku rayuwar bature gare ta bata shiga kitchen sai dai abunda masu aiki suka yi. Ta ansa mishi da to kawai ba don tayi niyar zuwa ba ita ina ruwanta da yarinyar ko mutuwa tayi ai ba damunta bane don bata ga wani alaka atsakanin su ba.

tana ajiye wayan tace ba inda zanje ta kira nanah tace tayi girki za'a kai asibiti.
Bayan gama home work din bata tashi daga wurin ba wayar ta ta fara kara yana neman dauki
Ta daga wayar ne cikin yatsina fuska wani lokacin bata son yin magana da nimrah sam don kullum tana cikin matsala ne kuma tana bukatan taimako.

Ya akayi ne nimrah.

Nimra dake sheka ayan ta da d boy a dakin shi ta kwantar da murya kamar gaske tace "dama inna ce ba lafiya na kaita asibiti shine Dr ya rubuta mana maganin kuma da alama suna da tsada"
To Allah ya bata lafiya bari inga abunda zan tura miki.ta katse wayar ba tare da ta jira cewarta ba.kamin ta kai ga ajiye wayar sai ta sake daukar ruri cikin fushi ta dauka me akayi kuma nimrah ni fa yau bana jin dadi.....kamin ta gama an katse ta da cewa.
Ai ba nimra bace kina magana ne da baaba wanda kuka sa aikin satan yarinya.
Nan kirjin sofy ya buga dumm tsoro ne karara ya bayyana a fuskanta sai ta hadiye yawu mutuqqq
I... in....na ka samu numbar wayata.
Wannan duk ba damuwarki bace.

So muke ku bamu kudin jinya dan yarinyar nan itama ƴar ta adda ce kadan ya rage ta kasheni ga abokin aikina ya samu targade a kafa.
Firgici ne ya bayyyana akan fuskan sofy wanda ba za'a iya misaltawa ba da ma akwai ta da tsoro kamar farar kura.
Da kyar tasamu ta hada kalmomin me tayi muku?
Sai baaba ya ce  "Ohhh ashe yar iskar kawarki bata gayamiki ba ko?

To ki tambayeta ni dai yanxu kudi nake son ki turamin, ko ki tura ko ke ma in dauke miki danki ko na gayawa mai gidan ki
Aaa kuyi hakuri zan baku kudin nawa ne
Kuke so nan ya gayamata tace zata tura amma nimrah anyi shegiya me sa bata gayamin abunda ya faru ba amma ta iya kira ta roki abu ai zanyi maganin ta.

Bayan ajiye wayar ne dama zata kira nimrah tayi mata masifa sai ga Dr ahmad ya dawo daga adibiti.

Shima dai basu kwashe da dadi da shi ba don ya zo daukar ta ne su je asibitin amma fir taqi tayi shigewarta daki tace ba inda zataje don ba dangin iya ba balle na baba shi ya karata chan tun da ya daukar wa kanshi wahala.
Nan ko ran maza ya baci yace ba zai dauki abincin ba ma tunda abun nata har da rashin m,  zai je wurin hajiyar shi ya karba tunda dama ita kullum sai ta tambayi jikin yarinyar zai dauke ta ma kawai suje tare in ta farka.

***********

Abdallah ya saƴi duk wani abun bukatan anfani na marasa lafiya ya kai dakin da aka kwantar da islam har lokacin bata farka ba sai ya yanke shawarar zuwa gida ya dauki su mami ya kawo su wurin islam din shi da son samu ne ma da sai ta farka an gyaramata jikinta da gashin kanta kamin kowa ya ganta don in sunganta a haka hankalin su zai kara tashi to ba yadda ya iya lokaci na qara tafiya ba amfanin yin shirun don dama abunɗa yasa bai gayawa kowa ba kenan.

Sai da ya shiga mota ne kamin ya tuna da hajiyar shi tana jiran shi a kan zasu fita gashi har yamma tayi innalillahi.... yau ya taɓo ta mai rabasu sai Allah don Hajiya akwai masifa da mita yanxu haka har sati mai zuwa tana mita akn ya ajiyeta yayi tafiyar sa ai bai damu da ita ba waya mutu waya ya dawo.

Abba ya fara kira ya gaya mishi akan yaga islam da duk wani abunda yafaru da ita wanda Dr ahmad ya sanar da shi sannan ya gaya mishi sunan asibitin da kuma dakin  da take duk yayi mishi bayanin komai.
Don yanxu dai xai je Ya fuskanci hajiyar shi ne.
Bayan gama waya da abba sai ya Kira yasir ya gaya mishi komai shi ma yayi Murna sosai kuma yace yana nan zuwa shima.

Abba dai hamdala ya rinqa jerawa sannan ya Kira daddyn Islam ya bashi kyakkyawan labarin da yasamu daga wurin abdallah, shima Murna sosai yayi har da bada kudi ayi sadaka  nan dai yakira duk Wanda Ya kamata ya sani, mami dai kukan murna ta saka haka ma fatima,da sauran masoyan islam din. kafun wani lokaci labari ya yad'u akan anga islam masu farin ciki nayi masu baqin ciki ma ba a barsu a baya ba irin su anty amarya da mukarrabanta.

Kamin kace me asibiti ya cika da dangi anata murna duk da dai har lokacin islam din bata farka ba amma kowa ya shiga ya ganta sannan ya fita ya zauna awaje.
Amma hajja dai tanace akan cewa ita dai sai ta zauna adakin ba yadda aka iya da ita haka nan aka barta dama ya take balle abun ya hada da tsufa.

Qarfe shida daidai na yamma ta fara bude idanunta a hankali, dishi dishi take gani har ta fara gani sosai ta juya taga dakin kamar dai asibiti idon ta ke nuna mata tayi yunkurin tashi sai taji jikin ta duk ciwo ga wani azaban da take ji ahannun ta na hagu wanda ta samu karaya a wurin
Hajja da ke zaune kan kujera ta tashi tsaye tace
Sannu yar nan kar ki tashi akwai ciwuka a jikin ki.
Da kyar ta samu ta iya bude baki ta ce
Hajja inane nan kuma me ya same ni?

Asibiti ne, bari in kira Dr din sai ya duba ki dan dama yace kina farkawa a gaya mishi

Tayi sauri ta fita daga dakin ta samu ƴan waje a zaune ta gayamusu islam din ta farka kuma wani yaje ya kira likitan.

Dr ahmad yaxo ya dubata ya tabbatar da babu wani matsala sai abunda baza'a rasa ba.Yace a bata tea tasha zai dawo anjima ya sake dubata.

*Mamyn ishrat ce✍*

Don't forget to vote, comments and follow.

MUJARRABI.( Completed)Where stories live. Discover now