By SNOW WHITE 12
DREAM GUY
In the name of Allah the most high and merciful
Quran: Al-Hijr (15:99)
وَٱعْبُدْ رَبَّكَ حَتَّىٰ يَأْتِيَكَ ٱلْيَقِينُ
And worship your Lord in order to attain certainty.
----------------------------------------------------------
Washe gari
Mahmud ne tsaye a kofar shiga palon mami ya na knoking tun wucewan minti biyar shiru ba a amsa kuma bai ji alamaun motsin mutane a ciki ba to ko dai ba kowa ne a gidan ?
Kai da wuya ace dukkan su sun fita.
saukowan shi kenan ko abinci bay ci ba yaji mummunan labarin da ya faru da islam wanka kawai yayi ya wutu nan don ya girgiza sosai da labarin wai ace rana tsaka an dauki yarinya ba wani bayani ba komai don kamin ya taho gidan mami ya kira abba ko mutanen sun kira amma yace ba a kira ba kumashi ma abunda yake jira kenan tun jiya amma shiru ba labari
To in dai kidnapers din gaske ne zasu nemi randsome da ga wurin iyaye ko relatives din wanda suka sata.Wayar islam din ma anyi tracin din shi an kama wani saurayi dan shaye shaye da shi wanda ya ke niyan sayarwa ya sayi kayan maye, ya sha duka sosai sai rantsuwa ya ke akan tsinta yayi kuma a exact location din da aka dauke islam din nan yace ya samu wayar.
Ya qara daga hannu zai buga kenan aka bude kofan,
Khaɗijah ce tsaye a gaban shi ta kura mishi ido kamar bata taba ganin shi ba in dai ba qarya idon ta ke mata ba wannan dai kamar yayan islam din nan ne da yake karatu a manchester don last zuwan shi basu hadu ba taje wurin kakanin ta ta wurin uwa ta kamin ta dawo kuma ya koma so ba su hadu a bakin fatima ne ma taji zuwan nashi, last ganin da tayi mishi kuma tunda suka shiga secondry school sabo a jss one kenan.
Amma in dai shi ne gayen ya hadu iya haduwa irin ɗream guy din da ta ke so ne ga kyau, ilimi, kudi,wayewa uwa uba asaliKai ita dai Alhamdullilah,
she thinks she has started havin fellings for this guy or rader say falling in love with him.
ko ma shi waye ne ashe abunda ake fada love at first sighte din nan gaske ne don gashi dai daga ganin mutum ta fara wasu dreams din da bata san ina suka fito ba don ɗai ta ra'ayinta tafi son karatu amma yau kawai komai yana son ya chanja mata,
Ya rabbi kar ka sa in ji kunya.Muhmud kam ya gaji da sayawa gashi shi sauri ya ke, ta bude kofa ta kafe shi da ido ko me take tunani ne oho mata
Sai ya daga key din da ke hannun shi ya karkadamata shi a fuskan sannan ta dawo hankalinta sai ta daburce ta fara masa sannu da zuwa ,
ya amsa mata yace "mami fa"
Nan ta gaya mishi abunda ya faru da ita jiya da daddere kuma ma asibiti suka kwana ita ma ta so zuwa tun jiya sai sadiq yace ta zauna ko islam zata dawo ko kuma za a buga waya.Innalillahi wa inna ilaihi raji un ya rinqa mai maitawa har ya samu nasuwar sa ta dawo jikin sa
Sannan ya tambaye ta asibitin da aka kai mamin nan ta gaya mishi yace to bari ya je ya dubata
Sai tayi saurin cewa nima dama chan zan je don in kai musu break fast
Sai ya ce to kiƴi sauri mu tafi
Nan ta dauko duk abun da za a bukata na asibiti suka tafiA hanyan su ta zuwa asibiti shiru kake ji cikin motar kowa da abunda yake tunani cikin ransa, ita dai khaɗija duk da ciwon mami da batan islam na damun ta amma tana dan satan kallon shi lokaci xuwa lokaci tana ina ma wannan mijin ta ne da tafi kowace mace sa'an zuwa duniya.
YOU ARE READING
MUJARRABI.( Completed)
Randomlabarin wata yarinya da ta rasa mahaifiyar ta Tun tana karama. ta taso a wurin kanwar mahaifiyarta, (mami) ta nuna mata kauna sosai sai qaddara ya shiga tsakanin ta da wacce ta tsane ta rayuwa ya juye mata lokaci daya. Ta fuskaci qalu bale kala ka...