Mujarrabi
By snow white
In the name of Allah the most high and merciful
Quran: An-Nahl (16:98)
فَإِذَا قَرَأْتَ ٱلْقُرْءَانَ فَٱسْتَعِذْ بِٱللَّهِ مِنَ ٱلشَّيْطَٰنِ ٱلرَّجِيمِ
When you read the Quran, seek refuge with Allah from Satan the outcast.
Yau ban dawo da wuri daga makaranta ba, na kai biyar na yamma duk a gajiye nake sakamakon exams da muka fara tun last week
Ina shiga giɗa nayi parkin a parkin lots
Sofy ce da imad zaune a gardin na cire idona tamkar ban gansu ba, amma sai tayi magana da karfi tace sannu da dawowa yar makaranta.
Yauwa sannun ku da gida nace mata tare da shigewa ciki
Kwanannan tana shigemin sosai bansan meyasa ba haka kawai ina zaune sai in ganta wai tazo taga ya nake i see it as a mock don taga miji baya kulani shine ta fara shigemin ni kuma banaso nasan ba zai kaimu ga ɗa mai ido ba don ba don Allah take son shirin na muba.
Nayi iya kokarina wurin jan hankalin deedat zuwa gareni zai nuna maitansa amma da zaran ya kusantoni sai komai ya wargaje to ni kuma a matsayina na budurwa kuma bafulatana ba zan iya bude baki in tambayi miji mai yasa baka kusanta taba ai nayi rashin kunya in nayi haka,ba wanda ya san abunda nake ciki sai khadija wanda takan zuwa wurina yanzu sosai bani da kawar data fita ita kaidaice ta san matsalata ɓa yadda bata yiba akan in tunkari deedat akan qin kulani da yake amma fir naqi ba zan iya abun kunyan nan ba sam.
******
Munyi da khadija yau zamuje gun fatima kasancewar mun kare jarabawarmu jiya tare muke zuwa makaranta da khadija amma kowa da course din da yake karantawa.
Mun iso gidan fatima misalin hudu da rabi na yamma gidan shiru tamkar ba kowa mun tsaya a palo mukayi ta kwada sallama chan saiga nas ya fito daga dakinsa, murmushin fuskarsa ne ya fadada daya ganmu sai yace mu zauna bari ya kirata
Yana shiga ya samu ta fito daga banɗaki tana daure da towel a qirji tana tafiya a hankali tare da ɗan ware kafa, gashinta a jike yana ganinta yaji sabuwar shawarsa ta tashi yace baby kamar inkara wani round yanxu don kin bala'en yi min kyau a yadda kiken nan, ta harareshi ta wuce warddrop dinta ta fara fitar da kayan da zatasa
Yaja gashinta da karfi yace ni kika harara to wlh kinci sa'an yan uwanki sunzo ne da nabaki mamaki yanzun nan,ya juyar da ita da qarfi ya matse bakinta, yace and in naji kin gayamusu yanayin zaman mu sai na lahira ya fiki jin dadi yayi kissing din bakin ta cikin mugunta sannan ya saketa.
Yace ana jiranki a palo kiyi sauri ki shirya sweetheart yasa kai ya fita ya bar mata dakin.
Da ido ta bishi har yafita hawaye ne shar suka sauka a kan kumatunta, tana tausayin kanta yanzu tayi nadaman aurensa amma ba wanda ta isa ta tunkara da maganan, wata daya ne kawai tayi cikin kwanciyar hankali a gidan ,bayan wata daya da aurensu ta fara ganin bad side of nas da farko abuge yake dawowa kuma sai tsakan dare daga baya kuma da abokansa yake zuwa dukkansu zasuyi tatill, bata isa tayi magana ba anan palon zasuyi ta shaye shayensu in sun gaji suyi bacci washe gari kowa ya kama hanya ya tafi, a barta da kwasan kwalaben giya data nuna bacinranta ya daketa sannan yace in bata iyawa ta tafi, to ina zata tafi bayan ga yadda akayi auren intaje gida tace musu meya dawo da ita daga wata daya da auren sai yanzu take ganin babban kuskuren data tabka a rayuwarta kuma ta cuci kanta da kanta, da ace ta yarda ta auri dan uwanta ta san da hakan bai faru da ita ba da yanzu tana chan uk mihgt be ma taci gaba da karatunta wanda nas ya hanata yanzu abu na gaɓa kuma yace baya son haihuwa kuma bai dauki wani major na kar ta dauki ciki ba yanzu ciki biyu ya zubar mata a cewarsa bai shirya haihuwa yanzu ba sai nan da shekara biyar zai fara haihuwa
YOU ARE READING
MUJARRABI.( Completed)
Randomlabarin wata yarinya da ta rasa mahaifiyar ta Tun tana karama. ta taso a wurin kanwar mahaifiyarta, (mami) ta nuna mata kauna sosai sai qaddara ya shiga tsakanin ta da wacce ta tsane ta rayuwa ya juye mata lokaci daya. Ta fuskaci qalu bale kala ka...