MUJARRABI 9

316 24 2
                                    

                 MUJARRABI 09

Whattpad:@zubainaibrahim

Two days later

GIDAN HAJJA

Ina dakin hajja muna waya da fatima don tun da naxo ba muyi magana ba nan take labar tamin yadda hajiya babba da mijin anty zuwaira sukayi

Ita hajiya ta ɗage sai dai yar ta ta dawo gida wanka daga asibiti shi kuma mijin ya ce ba za a tafi masa da ƴ'a ba in ma zasu tafin sai anyi suna kamin ta je wankan da farko ma cewa yayi baza su ji ba ai zuwa wankan ma ba addini ba ne Al'ada ce kawai irin ta hausa fulani

Nan dai hajiya ta kara hawa sai fada take wai yayi mata rashin kunya kuma ma agaban kishiya ɗon mami na wurin lokacin da su ke maganar dan Ɗr yace zai sallameta zuwa da yamma don ba ta da matsalan ƙomai haka ma baby

Mami dai da taga abun ba zai yi kyau ba sai tace wa mijin yayi shiru ya je waje zata same shi don ta na son magana da shi
Da harara hajiya ta bishi lokacin da yake fita
Da ga dakin

ace ita da ƴar ta wani yana son ya nuna mata iko da ita sai tayi kwafa

Abunda hajiya ta manta ai yanxo mijin ya fita iko da zuwaira don shi ne mijin matar sa ce sai yadda  ya so zai yi don Allah ne ya bashi
ikon kuma aljannarta na qar qashin kafar shi, miji ɓa abun wasa bane Allah ne ya daga darajar maza a kan mata kuma ya ce ayi musu biyyaya(manzon Allah (saw) yace da xa a bada umurnin wani yayi wa wani sujjada da nace wa mace ta yi sujjada ga mijin ta)kuji fa darajar da Allah ya bawa maza amma mu mata ba mu dauki miji a bakin komai ba ba mu girma masu ba mu yi musu biyayya sai kasamu mace na sa'in sa da mijin ta kuma a gaban 'ƴaya har makobta na jin muryoyin su ta ina auren zai iya albarka ,shi yasa yanxu mace macen aure ya yawaita(Allah ka bamu ikon yin biyyaya ga maxajen mu ka kuma bamu zaman lafiya).

Nan dai mami ta samu mijin ta taushe shi da nuna masa misalai don mijin dan boko ne kunƙan
Har dai ya yadda bayan suna zasu koma wurin hajiya anan
Abba ya shigo asibitin ya same su suna tattaunawa yadda za ayi nan ya ji me ke faruwa  
Yace aikin banza in bai yarda ba ai sai abari baza a tursasa masa ba
yaro da matar sa ace za a masa fin karfi Zuwaira ta koma giɗan ta don nima banga anfanin zuwa wankan gidan ba abu tun kaka da kakanni ake yin sa ya qi ci yaqi cinyewa
ta zauna  gidan ta shi ke da iko da matarsa.sai mijin" yace"
Abba ba matsala na yarda in anyi suna sai ta koma gidan .

MUJARRABI.( Completed)Where stories live. Discover now