Mujarrabi
In the name of Allah the most high and merciful
Quran: Maryam (19:30)
قَالَ إِنِّى عَبْدُ ٱللَّهِ ءَاتَىٰنِىَ ٱلْكِتَٰبَ وَجَعَلَنِى نَبِيًّا
He said, “I am the servant of Allah. He has given me the Scripture, and made me a prophet.
Washe gari mami ta kira ni da safe ta tambayeni, na mata bayanin komai kuma na gayamata bai taba furtamin kalmar so ba in ma akwai wanda ke so na to dr deedat ne, kuma na amince masa da tayin soyayyar da yayi min.
Ta dubeni da kyau sa'anan tace kin tabbata kina son sa
Kai na daga mata sa'anan nace eh mami
Anya islam sai naga kamar Abdallah kike so duk da kina boye min baki son gayamin abunda ki ke ciki, ban san yaushe muka fara yar haka da ke ba.
In don abunda zuwaira tayi jiya ne shiyasa kika ce dr deedat kike so,kar ki damu, in don ta nine na saba da halin hajiya babba da zuwaira mai taƴata kishi, ba halinsu da ban sani ba tun kamin haihuwarku.
Kamar zan ansamata in ce mata abdallah na ke so, sai kuma na tuna maganan hajiya babba da naji rannan(wallahi idan ka ga wani abu ya shiga tsakanin ka da islam to bayan rai na ne kuma wallahi in ka nace akanta sai na ciraka da ga cikin jerin 'ƴa'ƴa na sai ka zaba ko ni ko islam)
Tuna hakan da nayi sai naji abunda nake yi shi ne daidai in dai ina son abdallah na tsakani da Allah dole in taimaka masa da yin biyayya ga mahaifiyar sa duk da bai ce yana sona ba amma akwai alamun so a idanun sa ba zan so ya bijirewa uwar sa ba don ni ko kuma su samu tsabani.Mami ba haka bane ba komai wlh zan auri Dr
Amma kin san yana da iyali ko don mahaifiyar sa ta gayamin.
Sai da girjina ya buga jin tambayar mami "na daga mata kai eh na sani
To shikenan tunda shi kika zaba Allah ya tabbatar da alkhairi.
Ban amsa ba na tashi ina shirin fita daga dakin tare da share hawaye, na ji mami na ceawa
zata gayawa abba don ita ma bata ji dadin kananun maganganun da suke tashi a gidan ba
Tace zata gayamishi da wuri kamin ya ji maganganun da su hajiya babba zasu kai masa ta san bazai ji dadi ba don ba zasu gayamasa gaskiyar maganar ba.Shikenan na rabu da abun kauna ta duk dreams dina sun tashi abanza bazan rayu da wanda nake so ba, bazan taba ganin ranar da zan auri ya abdallah ba hajiya baki kyauta mana ba.
Mami na zuwa ko ta tarar da abba yana sauraron labaran duniya ba ta kai ga yin magana ba sai ga hajiya babba ta shigo palon sai harare harare take ta zauna tare da gaishe da abban
Mami da ta daga mata gaisuwa da harara ta bita
Ai ba ansar gaisuwan ki nazo yi ba
Lafiyar ki kuwa wai.
Lafiyata kalu matar ka ce ke son shiga min hanci
Abba dai kallon su yake da mamaki
Chan yace me ke faruwa ne wai
Hajiya babba tayi saurin karba tace "Alhaji kayi wa maman sadiq da yaranta gargadi su fita harkar yarana
Bana son wani alakan da suke son kullewa. Haka nan saɗiq ya kama dukan zuwaira kamar baiwar sa.Abba ya dubi mami yace me ke faruwa tsakanin yaran wai.
Ni dai Alhaji ba abunda ke faruwa in ma don islam ne
Ta riga ta fitar da miji daman abunda ya kawo ni kenan.sadiq kuma marin zuwaira yayi kuma na mishi gargadi kar ya kara.Don haka ni dai ban san wani abunda ya faru ba bayan haka.
To don Allah bana son kananan maganganu ku na mata.ku hada kanku ku zauna lafiya shi ne kwanciyar hankali na ace har yanzu da girmanku ban huta da raba fada ba har jika fa gare ki maryam amma kina abu kamar wacce aka kawo jiya dakin miji, haba nima fa yanzu hutu nake so don na gaji
Insha Allah zamu kiyaye cewar mami.
Kwanan biyu ina wasan buya da ya abdallah duk hanƴar da nasan zai hada mu bana bi ,yayi ta kira duk abanza bana daga wayan daga baya na rufe wayar ma baki daya don Dr yanzu sai ya kira sau goma.
Abdallah abun duniya sun taru sun masa yawa gashi islam bata daga wayar shi daga baya ma wayar bata shiga yayi yayi su hadu amma ya kasa kamar ma bata gidan.
Shi fa bazai taba bari hajiya ta shiga cikin soyayyar da ya gina shekara da shekarau ba
Ya je gurin abba don gayamishi kudurin sa akan islam, sai ya hadu da abunda ya fi karfin sa
Wai shi abba ya ba alhakkin bincikin Dr deedat a matsayin wanda zai auri islam ta ya ma hakan zai faru shi bai san ta ina zai fara ba
Ya so ya gayawa abba amma lokacin ranshi ya bace sosai ba zai iya magana ba yadda yake ya san kanshi kar yayi wa abba rashin kunya.
Ya bari akan in ya huce zai je ya samu daddyn islam ya gayamishi komai tun da shi ne uban ta ya san kuma zai goya masa baya.
Amma islam bata kyauta musu ba ya zata yanke irin wannan hukucin ba tare da sanin sa ba, wai me ta dauke shi ne sauna wanda bai san abunda zai yi ba, ya san taji maganganun hajiya ne kuma bai san iya adadin abun da taji ba.
Amma duk da haka bai kamata tayi abunda tayi ba,ya san ba son deedat take ba shi take so,don haka sai inda karfin sa ya kare,bazai taba bari ta auri wanin sa ba shine nan mijin ta daga nan duniya har aljanna mutuwa ce kawai zai raba su insha Allah.
**************************
Anty amarya ta samu ta sayar da gold dinta har ta je niger gun bokan,boka sai da ya biya bukatan shi da ita kamin yayi mata abunda ya kaita gurin sa.
Bata damu da abunda ya faru sakaninta da boka ba muddin bukatan ta zai biya.
Na farko dai tana son komawa dakin ta da zarar tana komawa nigeria na biyu kuma hankalin dady ya dawo kanta ita kadai ya manta da kowa ciki kuwa har da mahaifiyar sa da ƴaƴan sa ya kuma tsanesu ƴaƴan da mahaifiyar gaba daya kuma tana son ayi mata aiki akan islam don ta dalilinta ne ta fita daga dakin ta har taje tana bauta agidan innan ta wacce da take girmamamta amma yanzu kowa ya renata ta zama abun takawar kowa har qannenta da da suke darajata fiye da uwarsu da ta haifusu.
Boka yayi mata aiki sosai kuma ya mata alkwari in tana dawo wa nigeria ba zai kai sati ba zata ga daddy kuma in yazo zai mayar da ita dakin ta.
Maganan islam kuma ta gayamishi amma tace yayi duk yadɗa zai yi zaman gidan mami ya fita daga ranta ita kuma in ta koma nigeria zatayi yadda islam din zata dawo gidan ubanta don ta haka ne kawai zata iya gana mata azaban da ta tanada mata cinkin ruwan sanyi.
Bayan dawowarta ta fara shirye shiryen komawa gidan ta tun dadyn bai zo ba,har akayi sati a bata ga daddy ba har ta fara tunanin ko cinye mata kudi kawai akayi ,rannan kwasam sai ga.............
Vote,comment and share
YOU ARE READING
MUJARRABI.( Completed)
Randomlabarin wata yarinya da ta rasa mahaifiyar ta Tun tana karama. ta taso a wurin kanwar mahaifiyarta, (mami) ta nuna mata kauna sosai sai qaddara ya shiga tsakanin ta da wacce ta tsane ta rayuwa ya juye mata lokaci daya. Ta fuskaci qalu bale kala ka...