part 36

167 17 0
                                    


Mujarrabi

By snow whit

Abdullah (b. Masud) reported: We were on an expedition with Allah's Messenger (Pbuh) and we had no women with us. We said: Should we not have ourselves castrated? He (the Holy Prophet) forbade us to do so He then granted us permission that we should contract temporary marriage for a stipulated period giving her a garment, and 'Abdullah then recited this verse: 'Those who believe do not make unlawful the good things which Allah has made lawful for you, and do not transgress. Allah does not like trangressers" (al-Qur'an, v. 87).
[Muslim 1404]

Yana zuwa jagoranceta har dakin da suka kama baice mata komai ba duk da tambayoyin da take jera masa bai ansa mata ko daya ba yace ta shiga ta gane wa idonta tana murda kofan tajita a kulle nan suka kwankwasa saurayinne yazo ya bude don tsammaninsa room service ne don sunyi order abinci

Yana budewa Abdallah ya bashi super man pounce a fuska nan take mutumin ya faɗi a kasa haka nan ya bishi a kasan yayita bashi naushi sai ihun neman taimako yake ga jinin dake fitowa ta bakinsa,  gashi ba kaya a jikinsa dagashi sai boxers dakyar aka samu aka kwaceshi daga hannun abdallah anisa dake kan gado sai kuka take
Hajiya ce ta matso kusa da ita ta wanka mata kyawawan mari guda biyu kamin ta sata ta kimtsa jikinta dakyar abdallah ya yarda ta shiga motarsa saida hajiya babba ta nuna masa bacin ranta kamin ta shiga ya kaita gida tare da hajiyan ta sauka hajiya sai sababi take anisa kuwa kukan baqin ciki take ta san da kyar in abdallah ya yarda da ita kuma shikenan ta rasashi auren da taci buri ya tashi a banza gashi ta gama gayawa kawayenta kan ita nan da wata daya in anyi auren a germany zata tare yanzu me zatace musu kuma amma shahid ya cuceta yau.

Yana ajiyesu ya koma gida ya fara shirye shiryen komawa abuja daga nan kuma sai germany don ba zai sake dawowa kano ba in ba da wani dalili kwakkwara ba yayiwa kowa sallama ciki kuwa har da mami sannan driver ya kaishi airport anan yake gayawa drivern yaje ya dauki hajiya a gidan yayarta

Bayan wasu kwanaki komai ya kammala game da shirye shiryen tafiyarsa, ranar alhamis suka d'aga zuwa Berlin dake birnin jamus.

****************

Yau satina uku a gidan dr deedat abubuwa da dama sun faru cikin wannan lokacin ɗon matar dr deedat ko ince sofy yadda naji ake kiranta shu'umar macece naqin qarawa in yana gida saita nuna masa lafiya lau muke zaune amma yana fita ta chanja ta zama wata kala daban more especially in wannan kawarta nimrah nan tazo yadda take gwadawa kamar da ita nake kishi
Kuma wani lokacin in suna magana sai inji muryoyinsu kamar na tabaji a wani wuri amma duk iya tunanina na kasa ganewa, rannan da yayi rabon kawana reaction dinta tamkar ta sanni a wani wuri daga bayane ta iya saita kanta da deedat ke tambaƴarta dama munsan junane sai ta wayance tare da cewa no bansanta ba haka nan minti minti saita juya ta ganni kamar she is in shock haka nan.

Rannan ina zaune a palo duk kadaici ya dameni, Imad ya shigo, yana dan xuwa in babanshi na gida in baya nan kuma bana ganinsa sai ya dawo in yazo yana debemin kewa yayita min surutansa na cartoon da kuma na makarantarsu da abokansa. imad boko kawai aka sashi baya zuwa allo haka nan baya zuwa islamiya baisan komai ba game da addininsa ba in lokacin sallah yayi in nace masa yazo muyi sai dai yace mommƴ tace sai ya girma zai rinkayi ko kuma yace sai daddy ya dawo suje masallaci tare

Haka dai na rinqa jan ra'ayinsa a hankali ina nuna masa yin sallah abune mai kyau kuma duk wanda bayayi bazai shiga aljanna ba.

Haka na samu Deedat da batun saka imad islamiya yaji dadin shawaran sosai shima yace dama yana da niyyar sakashi da dadewa mahaifiyarsa ce ta hana wai yayi kankanta amma yanxu kam bata isa tace yayi kankanta ba.

Bayan kwana biyu imad ya fara zuwa islamiya, driver ke kaishi yaje kuma ya daukosa in lokacin tashi yayi.

Ranar daya fara zuwa uwarsa ta tada bala'e wai in tsaya iya wurin da aka ajiyeni ta san nice munafukar dana zuga deedat har aka kai mata yaronta inda za'ayita dukansa kuma in wani abu ya samu danta nayi kuka da kaina haka dai sukayi ta tijararsu itada kawarta wanda ita ke kara tunzurata tayi wasu abuɓuwan abun mamaki kuma kullum kawar tana gidan kamar sun hada mijin.

Ta gefena da deedat kuwa Yana iya kokarinsa wurin kyautata min da kuma jana a jiki don in saki jiki dashi kamin wa'adin mu ya cika, to dai zan iya cewa yanxu kashi hamsin sun ragu don mukan zauna muyi hira sosai yayimin tadin abubuwan daya faru da dadewa wasu masu ban dariya wasu kuma na tausayine,na ganeshi mutum ne mai saukin kai da sanin ya kama wanda ya san hakkin na kasa dashi in dai yana gida ko da wasa baya barin sofy ta takeni sai dai in bayanan sannan take abubuwanta.

Yau Dr yace nayi musu girki shida abokansa wai zasuzo don lokacin bikin basu nan yanzu kuma da suka dawo shine sukace zasuzo suci girkin amarya. Kullum in yanacin abicin dana dafa sai yayi santi yace duk duniya daga hajiyarsa saini na kansa masa pillow a baya ince karka fadi don santi, sai yace da gaske nake ai Alhamdulillah nayi dace ɓakiga harna fara aje tumbi ba, dariya kawai nake masa inyana wannan maganan.gashi yana son kayan mu na hausa fulani duk sanda ya ganni cikin atampa sai ya yaba wani lokacin har da tukuici yake bani.

Na shiga kitchen din da wuri don kar in makara suzo ban kare ba don yace min bayan sallan azahar zasuzo su.

Ina cikin girkin ne misalin karfe daya da dan mintoci sainaji knock a kofa don na kulle kofan tunda ni kadai ce
A gidan
Ina budewa naga imad da kayan makarantarsa yana riqe da goran zoɓo
Nayi mamakin ganinsa don uwarsa bata barinsa yazo indai uban bayanan amma sai na bude masa nace ya dai imad gudowa kayi kazonan ko don naga ko uniform baka cire ba

Sai ya mika min goran zobon yace na kawo miki ne ki taba

Sai naqi karba, nace

Kasha nakane na gode kaji good boy
Saiya make kafada wai shi yayi fushi ba don naso ba na karba na dan sha kadan

Sai na mayar masa da goran,yana karba ya ruga da gudu ya tafi murmushi nayi na koma kan aikina wanda ya rage kadan na kare

Cikin minti biyar naji kaina na juyawa sai biƴu biyu nake gani dakyar na iya jan kafata zuwa palo, na kwanta akan kujera dishi dishi nake gani, ina son intashi amma na kasa gashi na fara jin kaurin abincin da nake dafawa

Inanan a wurin aka bude kofa aka shigo sai idona ke nunamin kamar antƴ amarya nake gani nayi nayi in bude idon da kyau amma na gagara

Anty amarya data shigo gidan dama tana tunanin yadda zata aiwatar da plan dinta ba tare da an samu matsala ba don islam ta shammaceta tana jira ta dawo ta mayar da ita yar aikin gidanta kwatsam tana dawowa daga dubai sai taji anyi aurenta, shine taje gun bokanta akayi mata aiki da zata hanata jin dadin zaman gidan mijinta taso su hada kai da sofy amma sofyn taqi tace bata yarda da bokayen nan ba saboda ba sai taje wurin wani ba ita da kanta zata fitar da ita a gidan.

Tana ganin condition din islam tayi murmushi tace ai wannan kishiyar taki ma ta isheki dama na hutar da kaina na barta tayi abubuwan ta amma duk da haka ba zanyi asarar kudina a banzaba tunda na karbo sai nasa miki in yaso daga nan na barki ko banza kinsha wahala kema yanzu.

Ta shiga dakin islam da sauri ta ajiye komai yadda boka ya gaya mata ta fita daga gidan lokacin hayaki ya cika dakin itama kamin ta fita harta fara tari.

Bayan sallahr azahar ya iso shida abokansa guda biyu. Suna shiga layin anty amrya na fita daga layin ita ma.

Direct site din islam ya nufa yana dosan wurin ya fara jin kauri yayi sauri ya shiga dakyar yake ganin hanya ya shiga kitchen ƴa kashe gas din sai tari yake ya samu ya bude back door da labulaye don hayakin ya fita

Nan ya fara neman islam tare da taimakon abokansa

Chan suka ganta yashe akan kujera da sauri ya ciccibeta ya kaita mota ya shiga shima yaja da sauri zuwa asibiti, abokansa suka mara masa baya abincinda basu ciba kenan.

Sofy da nimrah dake leke ta window nan suka tafa tare da yin shewa dama sunyi hakane don su bugar da ita in deedat ya ganta zai dauka shaye shaye take. paln dinsu zasu rinqa bugar da ita kullum harya gaji ya saketa don sunsan yadda bayason maganan kayan maye.

Vote, comment an follow

MUJARRABI.( Completed)Where stories live. Discover now