part 24

221 23 3
                                    

*MUJARRABI* 2⃣4⃣

*By snow white*

Whattpad:@ zubainaibrahim

On the authority of Al-Hasan bin Ali, the grandson of the messenger of Allah, who said : I memorized from the messenger of Allah his saying : "Leave that which makes you doubt for that which does not make you doubt."
[Tirmidhi and Nasaee]

_________________________________

Mahmud ne da sadiq a harabar asibitin sun jingina da jikin mota suna ɗan taɓa hira na yau da kullum.

Sai ga humaira kawar islam tazo dubata zata wuce kenan, sai taga sadiq din a tsaye. Nan ta juya tazo wurin ta gaisheshi da yi mishi ya jikin islam haka ma ta gaida mahmud ta gane shine sakamakon kamannin data gani na islam a tare da shi.

Sai ta juya ga sadiq  tace "yaya ina dakin yake"kamar zai kwatanta mata sai yace muje in nuna miki dakin don kar ki ɓata kin san asibitin girma gareshi sosai.

Mahmud ne ya kura mishi ido kamar zaiyi magana amma ina tuni sadiq yayi gaba sai janta da hira yake.

Akan baya ganinta yanzu kwana biyu ta buya bata zuwa gidan su kuma.

Murmushi kawai tayi batare da tayi magana ba tana ayyanawa a ranta dan adam kenan ta dalilin shi na dai na zuwa gidan su yanxu kuma yana tambaƴa ta meyasa na daina zuwa bayan idan naje gidan ganina yake tamkar kashi sai yayi ta daddaure fuska.

Ya iso bakin kofan dakin, sannan yaja birki yace  "ki shiga nan ne, in kin gama ina jiranki a waje akwai muhimmin abu da zan gaƴamiki" sannan ya juya ya fita.

Ta tsaya tayi jim a wurin tana tunanin wai magana, wacce maganar zaiyi mata haka? ba mai bata amsa sai ta shiga dakin kawai tare da sallama abakinta.

Sadiq ya koma wurin mahmud ya tsaya kusa dashi mahmud ya kura mishi ido batare da yace komai ba.

Sai ya juya ya kalleshi yace wannan kallon fa?

Tambaya ƙake ai kasan abunda kallon ke nufi

Niba abunda nayi, ku dai sai sa ido kuka iya, wai ni har london din suna irin halin nanne na sawa mutum ido.

Naji tunda baka son gaya min to wacece yarinyar don ban santa ba.

Tunda bazaka gayamin abunda ke tsakanin ku ai intayi wari maji ai.

Toh shikenan tunda ka nace ba kowa bace kawar islam ce kuma abunda yasa bana son magana ban san yadda abun zai kasance ba ne, nafi son in sanar da ita tukunnan in mun daidaita sai in sanar da kowa.ina son in aurenta.

Masha Allah abu yayi kyau kai na maka murna dan uwa Allah yasa ayi a sa'a

Amin sadiq ya amsa tare da cewa katayani rokon Allah akan Allah ya daidaita tsakanin mu ya sa kuma shine Alkhairi.

Yanzu nake son sanar da ita inta fito don ni bazan tsaya wani soyyaya ba inta amince sai ayi shi da wuri kawai.

To Allah ya sanya Alkhairi.

Dama nima akwai niyan da nazo dashi amma yanayin dana same ku sai ban samu gabatar da kudirina ba amma tunda yanzu komai yayi daidai bari in fara sanar da kai, cewar mahmud.

Dama nazo da niyan neman auren fatima ne to gashi ban samu dama ba saboda batan islam da kuma ciwon ta.

Tun ina karami na taba jin hiran su mommy da mami akan in mun girma zasuyi farin ciki ace in ƴaƴan su zasu amince su kulla zumunci ta aure tsakanin su da za suyi farinciki sosai .

To bayan rasuwar mommy sai na kudurtawa raina zan cika mata wannan buri nata na auren fatima.

Na ajiye abun as zan cikawa mommy burin tane to abunda bansani ba ashe nima na fada soyayyar fatima wanda kullum sai nayi tunanin ta abu kamar wasa har ta kai kullum kwanan duniya sai nayi tunanin ta haka ma kamin inyi bacci sai ta fado min arai yanzu yazama bana iya sati ba tare da nakirata mun gaisa ba to gaskiya yanzu nazo ayita ta kare kawai zan gabatar da kaina a wurin fatima sa'annan kai sai ka taimaka ka sanar dasu mami don yanzu kam ina kunyar ta bazan iya tunkarar ta da maganan nan ba. Daga nan sai ta gayawa abba.

Sadiq cikin farinciki ya rungume mahmuɗ din yace kai naji dadin wannan batu ai mami zatafi kowa murna da  farinciki, in an sallami islam daga asibiti muna komawa gida zan sanar da ita shine farkon abunda zanyi.
Yauwa nagode sosai ɗan uwa.

Mahmud ne ya sake cewa Amma ka san wani abun mamaki dake faruwa dani kuwa yanxu kwana biyu kenan ina recieving wasu text  messege na soyayya  daga farko gaisuwa ne da yimin fatan ganin islam daga baya kuma sai abun ya chanja, nina rasa gane wake turo min irin sakon kuma bansan numbern ba. Kuma inna kira no switch off take kullum. Nasan ko waye ke yi mmin haka ya sanni sosai kuma ƴana cikin family amma zan bincika saina gane ko wacece ke turomin sakonnan.

Sadiq ne yace "kawo number mu gani" nan ya miqa masa, ya karbi wayar tare dasa number a wayar sa

ya fita ba suna, nan ya mayar masa da wayan yace to Allah ya kyauta don nima bani da number acikin wayata.

******************************

Islam ce zaune akan gadonta na asibiti sai mita take ita tagaji da asibitin a sallameta tunda taji sauki

Mami tace haba islam kin tada rigima sai kace karamar yarinya ai suma ba son rike ki suke ba ai.

Mami wlh na gaji ne ina son in koma gida.
Fatima da khadija sai dariya suke mata tare da kara tsokanarta.

Nan ta harare su sannan tace ku kuma ku fita harkata.

To in Dr yazo sai ki gayamasa ai tunda baki jin rarrashi fadin mami.kamin tayi wani magana

Dr deedat  ya shigo dakin da team dinshi na Drs da  suke ward round tare.

Ya dubi islam din tare da yi mata wasu tambayoyi, ta amsa nan yayi rubutun su na likitoci a wani papper yace babu matsalan komai saboda haka zuwa yamma zan iya sallamanta amma zan tura nurse ayi mata dresing wound dinta kamin ta je gida.

Da yazo fitane Ya karbi address din gidan su wurin mami akan cewa zai ringa zuwa dubata lokaci zuwa lokaci tunda shine dalilin karyewar hannunta.

Nan suka fita daga dakin suka shiga wani don duba marasa lafiyan dake cikin asibitin.

Mami ce ta dubi islam tace shikenan ko rigima ya kare ai, tunda an miki abunda kikeso sai mu fara shiri ko.

Hajja kema ya kamata ki samu hutu kar kafan ki ya tashi inta nice ma bai kamata ki zauna anan ba tunda gani dasu fatima.

Hajja tayi murmushi tace in banyi jinyan jikata ba wa zanyi. Yanzu ba sai inje gidan ba tunda ta ji sauki

Mami ce ta dauki wayarta wai ina su sadiq ne suzo su fara rage kaya kamin a bamu takardar sallama.

Ta kira shi a waya yana dagawa tace zo kufara rage kaya don za'a sallameta zuwa yamma.
Sadiq da ke tsarawa humairah kalamai na soyayya, Yace "mami nayi dan nisa amma bari in gayawa mahmud".

*****************
Sofy cikin shirinta na zuwa asibiti wurin mistirious girl sunan da tasa mata kenan don bata tsaya taji sunan yarinyar ba lokacin da deedat ke yawan maganan ta amma yanxu ya daina, jiya har imad sai da yayi mata tadin antyn da suka je wurin ta a office din daddyn shi abunda ya kara daga hankalinta kenan harta kasa bacci da daddare tana tsaka da war warewa.

Yanzu haka ta jira ya fita kamin ta bi bayan shi, nurses din asibitin zata tambaya baxata bari deedat ya san taje asibitin ba.

Tana tafiya ne ta samu pounce tire.
Ta Kira driven ta tace ya kawo wani mota yazo ya dauketa.

To bai zo cikin lokaci ba don dama yaje shan mai ne nan ranta ya qara baci bata so hakanba sam ta so war haka har tayi abunda ya kaita har ta koma gida.

Bayan an gyara motan ne ta kama hanyar asibitin.

Lokacin kuma su islam an sallamesu har sun fito harabar asibitin mahmud ne yace bari ya karbi sauran maganin islam din wanda da safe sukace babu sai zuwa rana za'a kawo. To har ya fita sai ya tuna yace su jirashi anan gurin yana zuwa.

Anan kuma sofy ta danna hancin motan ta cikin asibitin.

To ga dai sofy ga kuma islam ya haduwar su zai kasance
Shin islam zata gane sofy kuwa? ina jira daga gareku.

Muje zuwa

*Mami ishrat ce*✍

Vote
Comment
Follow and share.

MUJARRABI.( Completed)Where stories live. Discover now