MUJARRABI 2⃣5⃣
BY SNOW WHITE
This page is for u mama thank you for beieng theire, an always supporting me in every thing. lots of Luv.
****************
Narrated Aishah : "The Prophet (pbuh) used to practice I'tikaaf (confining oneself in a Mosque for worship) in the last ten days of Ramadhaan till he died and then his wives used to practice I'tikaaf after him"
[Al Bukhari 3:2026]-------------------------------------------
Tayi parkin motar ta ta fita kenan ta fara tafiya zata shiga asibitin.
A loakcin ne mahmud ma ya fito riqe da ledan magani a hannun sa dukkan su biyu basu ankara ba sai suka bangaji juna ga sofy dai tana waige waige ne kar deedat ya ganta mahmud kuma yana duban maganin da aka bashi ne ko daidai ne.
Sorry mahmud ya fada sanna ya duka ya dauka mata kayan ta daya fadi, ta karbi kayan ba tare da ta tanka ba
juyawan da zatayi sai taga kamar islam ce tsaye amma ta kasa gane ta saboda side view dinta ƙawai ta iya gani.Mahmud da yaga matar bata tanka ba sai yai tsammanin ita din bebiya ce nan yayi gaba su islam na ganin shi suka shiga mota shima shiga yayi yaja su zuwa gida.
Sofy dai bata sake samun daman tantace ko islam din ta gani ko ba ita ba don tuni sun fita daga asibitin.Nan ta shiga asibitin tayi wa nurses tambaya akan yarinyar da Dr deedat ya kawo. sukace mata yanzu ta tafi giɗa an sallameta, bataji dadi ba sam hakan nan ta kama hanyan gida ba tare da nasara ba amma taji dadin tafiyansu ko banza yanzu deedat zai daina zancen yarinyar dama tazo korar sune daga asibitin.
Ta shiga motar ta kenan taji ana knocking mata glass din motar dagowan da xatayi Sai taga deedat ne tsaye hannun shi na dama cikin aljihun wandon shi fuskan nan a hade kamar hadarin da ya kunnu kai, nan take taji hanjin cikin ta sun kada,
Wayyo Allah ya ganni shikenan me zance masa ya kawo ni nan
Ta fita motan cikin karairaya tare da cewa hoony ina ka shiga naje ban sameka a office ba.
Me ya kawo ki nan
Dama tazo da plan din ta in har ya kamata sai kawai ta mika mishi wani file dama tun kamin ya fita ta cire shi daga brief case din saTunda yazo yake neman file din bai gani ba yanzu haka dama gida zaije ya duba don ya san yasaka acikin brief case din sa to ya akyi kuma bai ganshi ba.
Amma ai na nasa shi, yanxu na diba ban ganiba a ina kika same shi.
A bed side drawer
To kawo nagode
Amma ya akayi kika kawo da kanki kwanaki wayana na manta nace ki kawo min sai dai naga drive dashi kinqi zuwa yau kuma ban nema ba sai ke kika kawo da kanki anya don shi kika zo nan kuwa
Ko kuma spying dina kikazo yiHaba honney sakaiyan da zaka min kenan don na kawo maka muhimmin abu daka manta. Shikenan ai magani na kenan, gobe ma naqara yi maka gwaninta.
Nan ta hada fuska alamar tayi fushi, shi kuma ya shiga bata hakuriTo shikenan nagode jeki gida sai na dawo
Har ta tada motar ta sannan wani tunani yazo mata.
Sai tace yauwa hooney tunda nazo ka kaini in gaida wannan yarinyar da kayi accident da ita naga kana damuwa why not inje in dubata yanzu.
Hmmmm hoony kenan yaushe kika fara damuwa da ita ina rannan ba yadda banyi dake ba amma firr kinqi zuwa. Ba sai kinje ba don anriga an sallameta,kuma ta koma gida daxun nan.
YOU ARE READING
MUJARRABI.( Completed)
Randomlabarin wata yarinya da ta rasa mahaifiyar ta Tun tana karama. ta taso a wurin kanwar mahaifiyarta, (mami) ta nuna mata kauna sosai sai qaddara ya shiga tsakanin ta da wacce ta tsane ta rayuwa ya juye mata lokaci daya. Ta fuskaci qalu bale kala ka...