*MUJARRABI* 1⃣6⃣
*By SNOW WHITE*
*Whattpad:@ zubainaibrahim*
FATAN ALKHAIRI GA MASOYAN MUJARRBI SON SO FISABILILLAH
In the name of Allah the most high and merciful
Quran: Ghafir (40:60)
وَقَالَ رَبُّكُمُ ٱدْعُونِىٓ أَسْتَجِبْ لَكُمْ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِى سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ
Your Lord has said, “Pray to Me, and I will respond to you. But those who are too proud to worship Me will enter Hell forcibly.”
--------------------------------------
Gadan gadan baaba yayo kan islam zai aikata masha'an daya saba da 'ƴaƴan mutane wanda kaddar da Allah ya daura musu kenan ba dan sun soba kuma ba qinsu Allah yayi ba sai jarabawar rayuwa yaga zasu cinye ko akasin haka, wasu sun mutu wasu na yawo da tabon kuma har karshen rayuwar su ba zai goge ba.(Allah ka shirya mana ƴaƴan mu da zuri'ar mu ta hanya madaidaiciya)
Islam dai tana zaune ta na tunanin yadda zata kare kanta baza ta taba bari mugun nan yayi mata abunda yayi niyya ba ta gwammace ta mutu akan ta bar azzalumin nan yaci galaba akanta.
Idon tane ya sauka aka kwalban giyar da ya shigo da shi wurin da take
Nan tayi dabarar daukar kwalban shi kuma yana kiciniyar cire rigan shi
Bai ankara ba yaji
ta kwalamishi kwalban akan shi nan take ya fadi a wurin sumamme gashi abuge yake kawai sai yafadi akasa teeem kake ji.Cikin tsoro ta lallaba tabi gefenshi tana addu'an Allah yasa ɓai mutu ba don bata fatan har karshen rayuwarta ta dauki ran mutum koda cikin kuskure ne nan take hawaye ya fara zarya a idanun ta ga jikinta duk ciwo yake mata kayan jikin tama kamar a bakin kura aka fiddashi ba kyan gani sam wani wurin ma ya fara yagewa tsaban wahala da tasha mura ma yayi mata tutuqa sai wani irin tari take wanda bata sabayin irin saba don tun da ake zuba mata ruwan sanyi ta fara yi gashi kamin ta gama bushewa ankwara mata wani tsaban mugunta.
Nan ta bude kofan a hankali sai ga dayan dan ɗaɓan yana gyagyaɗi jin bude kofa ya wai ga tare da cewa har ka gama ne da baiji anyi magana ba ya tashi cikin laƴin maye ya dan yi dube dube bai ga komai ba sai ɓeran da ya gani sai ya koma ya kwantar da kanshi a wurin da suka zauna yaci gaba da gyangydin shi.
Islam na ganin ya koma sai ta lallaba cikin sanɗa ta fita da ga cikin ginin, da sauri sauri gudu gudu don dai baza ta iya gudu ba bata da qarfi sam don tunda suka dauke ta sau daya suka bata abinci. abincin da aka batan ma bata iya cin shiba don tsoron da take ciki.
*******************
Sofy ce da nimrah akan hanyansu ta komawa gida cikin farin ciki da annashuwa
wayanta da ke gefe ne ya fara ringing tana d'agawa taga mijin ta ne nan ta ansa tare da cewa.
hooney hi.
Hi,
Ka dawo ne?
Eh nadawo har nasake fita ma.
Ina kikaje ne tun nazu nake neman ki a waya ban sameki ba.
Nan ta daburce ta fara in ina
Chan dabara ya fado mata ta tuna da gidan hajiya.Tace ina gidan hajiya ne na kai imad weekend.
Ok,dama akwai wani free medical da zamuyi ne to nina manta yanxu ne daya daga cikin ƴan team din suka kira ni shine na kama hanya.
YOU ARE READING
MUJARRABI.( Completed)
Randomlabarin wata yarinya da ta rasa mahaifiyar ta Tun tana karama. ta taso a wurin kanwar mahaifiyarta, (mami) ta nuna mata kauna sosai sai qaddara ya shiga tsakanin ta da wacce ta tsane ta rayuwa ya juye mata lokaci daya. Ta fuskaci qalu bale kala ka...