MujarrabiIn the name of Allah the most high and merciful
Quran: Al-A'raf (7:55)
ٱدْعُوا۟ رَبَّكُمْ تَضَرُّعًا وَخُفْيَةً إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلْمُعْتَدِينَ
Call upon your Lord humbly and privately. He does not love the aggressors.
Daddy zaune a offic dinsa secteriyarsa ce ta kawo masa wasu files din da zaisa hannu, hannun jarine da wani company wanda yafi shekara daya basu samu daidaituwa ba sai jiya suka samu daidaitawa.
Haka kawai yaji kamar an mintsine shi sai kuma ya fara jin kanshi yana juyawa kaman sarashi ake da gatari,yayi saurin karasa komai sauran kuma ya bari akan sai gobe idan da yardar Allah sai ya karasa,kawai yaji hankalinsa ƴa tafi gida,a take ya dauki key din motarsa gida yaje ya watsa ruwa ko zaiji saukin abunda yakeji sa'anan ya kwanta yayi bacci ,sai goshin magariba ya farka da sunan anty amarya ya tashi gashi ya jike sharkaf da zufa. hankalinsa a tashe yake yaji idan baiga anty amarya yau ba mutuwa zaiyi,hakanan yakejin rayuwarsa duk ya dogara akanta baiyi wata wata ba ya shiga bayi yayi wanka tare da yin alwala yana fitowa Ana kiran sallahr magariba,yayi sauri yaje masallaci ana idarwa ya fita ya shiga mota bai zarce ko ina ɓa sai gidansu anty amarya.
Antƴ amarya data cire tsammani don saura kwana hudu iddanta ya kare tana tsakar gida tana waya da kawarta tana gayamata gaskiya ace duk kudinda tabawa boka har yayi amfani da ita amma gashi har lokaci ya kure. sai taji ana sallama awaje kuma kamar muryan daddy ne, nan ta katse kiran tare da sake kasa kunne sosai ai kuwa shine batayi wata wata ba ko ta tura kannen ta, ita da kanta dayake da ɗan mayafi akanta tayi hanyan soron cikin sauri ai kuwa shine a tsaye ya harde hannuwa ta baya yana kai kawo.Tana ganinsa ta fara santinsa ,Ya kara kyau da jiki har da haske kamar ma bashi da damuwa gata ita ta lalace tayi baqi duk warin hayaki takeyi don gamawarta kenan yanzu.
Daddy ne ya fara bata hakuri akan sakin da yayi mata kuma yazo daukan tane yanzu don ya maƴar da aurensu tun kamin yazo.
Antƴ amarya ta harareshi sannan tace ba inda zanje sau nawa ina zuwa in rokeka ka mayar dani amma ka shafawa idonka toka ka nuna zama ya kare tsakaninmu to yanzu nima ba zan koma ba.
daddy bai ankara ba sai jin danshin hawaye na sauka akan fuskarsa ba zai iya ko da minti dayane ba tare da ita a rayuwarsa ba yaji duk duniyan ta masa kunci shi kawai zuciyarsa na azalzalarsa akanta.Don Allah kiyi hakuri ki dawo dakinki ina bukatanki dani dasu amal
Dama baka san dasu bane ka sakeni(tanayi ne don ganin ya karfin maganin aikuwa yayi mata daidai yadda take bukata)
To ki fadi abunda kikeso yanzu za'ayi miki don rayuwa babu ke tamkar rayuwa ba iska ne.Ba komai muje kawai in naje gidan zan gayamaka buqatuna.
Ta fita daga gidan kasancewar dama da karamar mayafinta ta fito ba tare da tayiwa mahaifiyarta sallama ba acewarta zata kirata sai tayi mata bayanin komai, sauran kayanta kuma bata bukatansu yanzu sabon wardrop zata bude sai ya gane shayi ma ruwane duk abunda ta batar sai ta mayar daya bayan daya.
Daddy ko sai rawan jiki yake akanta sai kace wanda ya kawo sabuwar amarya.
Wayarsa ne ya buga lokacin da suka isa gidan
Yasa hannu cikin aljihu ya fitar ya karashi a kunnensa tare da cewaƳi hakuri hajja gani nan zuwa nama riga na sayi maganin yanzu zan kawo
Yana ajiyewa anty amarya ta dubeshi sa'anan tace wai fita zakayi yanzu daga dawowata
Cikin kwantar da muraya yace dama hajja ce tunda safe da naje na samu kafanta yana ciwo bata iya tashi kuma maganinta ya kare shine na saya mata,tana jirana, ni nama sha'afa ne don tun dazu yakamata na kai mata
Amma kiyi hakuri inje yanxu zan dawoCikin tsawa anty amarya tayi magana ba inda zakaje yanzu sai dai gobe ka kai mata amma inada bukatar ka yanzu.
Haka kawai ya samu kansa dayi mata biyayya,yaso yanuna mata qin amincewa amma sai yaji ba zai iya bijiremata ba amma deep down yaji zafin maganan ta.
Suna shiga saiga yaranta sunzu sun mata oyoyo tare da tambayarta ina taje basu ganinta kuma me ta kawo musu.
Anty amarya dai likkafa tayi gaba sai abunda tace daddy zaiyi ya watsar da kowa da komai sai abunda ta gindaya masa yakeyi hakannan tana karban kudi wurinsa bana wasa ba har harkokinsa suka fara yin baya abba daya masa magana cewa yayi ba ruwansa ai dukiyar sace, ba wanda ya tayasa nema, abba abun ya daure masa kai daddy da kullum suke shawara tare suyi abunsu kansu a hade amma yau shike gayamasa haka,shi abun da yafi bashi mamaki ma yadda yanzu daddyn ya chanja gabadaya komai sai yace sa'a sa'a hatta hajja yanzu baya ganinta da qima rabonshi da gidanta tun washe garin dawowar antƴ amarya gidansa, tayi magana abanza bayama sauraronta daga bayama ya daina d'aga wayarta,shine ta kira Abba ta tambayeshi dalilin chanjawar daddy shima yace hakanan ya ganshi amma yana gani ba banza bane don bayan rabuwarsa da antƴ amarya ba yadda bai rarrashe shi ba amma ya rantse akan ba zai taba mayar da ita ba shi yana neman wani aure yake ma don ya gaji da halinta na rashin kunya, duk bin duniya amma fir daddƴ yaqi amincewa,sai kuma ace rana tsaka kawai sai ya gansu tare kuma wai ya mayarda ko hajja ma abakin mutane taji ya dawo da anty amarya.
Kuma a binciken da yayi ma duk kudadensa da yake fitarwa antƴ amarya yake bawa tashin farko million biyar ya fitar kuma duka ya batasu bai cire ko kwandala ba.
Sun aje kawai yanzu abunda zasuyi zasu fara roka masa sauki a wurin Allah ko za'a dace amma dai abubuwan ɗa yake yi ba banza ba ya daina hulda da kowa.
Hajja tayi kuka harta gode Allah yanzu kawai ita bataga ta zama ba to ko abincin da zataci ya gagareta gashi yar ta hassana bata kasar tana kasar waje tare da mijinta, kuma batason ta gayamata ta tayar mata da hankali
Haka dai ta zauna taci gaba dayiwa daddy addu'a amma abun kamar karuwa yake gashi duk magungunan da take sha donta samu sauki na ciwon kafar ta sun kare ya kai ya kawo tayi kwana biƴu bata iya fita daga dakintaba sakamakon kafarta daya fara ciwo ranar haka ta kwana ta yini ba mai taimakonta tayi kuka har ta godewa Allah.
kawar ta hajiya lami ce ta shigo ta taddata cikin yanayin da ba kyan gani ga fisari da take tayi awurin har da kashi ma, kawar ce ta taimaka mata ta kintsa sannan ta kira ɗanta wanda take zama a gidan sa,yazo suka kaita asibiti aka bata gado, anan suka kira abba ɗon daddy yaqi daukan wayar sa ,abba har kwalla yayi don ganin yanayin da hajja take ta jeme ta lalace ta zama abun tausayi, kai duniya ina zaki damu ace yadda daddy ke son mahaifiyarsa amma ƴau wai mace tashiga tsakaninsu, harta shiga hali irin haka baizo ya dubata ba (ya Allah kasa mufi karfin zuciyar mu)
Ya kira kanin dady hamid ɗa yake zama a kaduna ya shaida masa hajja ba lafiya,shima dai da yazo yayi baqin ciki sosai da ganin yanayin mahaifiyar tasu,yaje wurin dadday dakyar ya samu ganinsa,daya tashi zuwa ma da anty amarya yazo,kallon hadarin kaza tayi mishi kamin ta zauna gefen daddy.
yace yanason ganawa da yayan shine ,sai tace duk abunda zai fada ya fadeshi a gabanta, daddy ma ya goyi bayanta akan haka bazataje ko ina ba ai ba abunda yake buye mata da yaga abun zai zama tozarci sai kawai ya tafi batare da sunyi maganan ba.Bayan hajja taji sauki ne aka sallameta daga asibiti, bai kaita gidanta ba, ya dauke ta ya tafi da ita gidanshi don bata kulawan daya kamata.
Mami ishrat
Vote, comments,share and follow
YOU ARE READING
MUJARRABI.( Completed)
Randomlabarin wata yarinya da ta rasa mahaifiyar ta Tun tana karama. ta taso a wurin kanwar mahaifiyarta, (mami) ta nuna mata kauna sosai sai qaddara ya shiga tsakanin ta da wacce ta tsane ta rayuwa ya juye mata lokaci daya. Ta fuskaci qalu bale kala ka...