part 26

260 26 12
                                    

MUJARRABI 2⃣6⃣

BY SNOW WHITE

The Messenger of Allah (blessings of Allah be upon him and his family) has said: The best of those amongst you is the one who learns the Quran and then teaches it to others.
[Al-Amali of Shaykh at-tusi]

----------------------------------------------------

MUJARRABI fans naji dadin comment  dinku na Jiya so ga break fast nan Nayi Muku, aci gaba da comments.

This page goes to my whattpad people starting with Rabimurtala,  safiyadanjuma84,ummuaulad,user07602286,spanishfly,humaierah2006,Aishaghana12, mrsbello2011,mss-dheejah,bintamuhammad8 and maman sultan thank you for readin and  voting always. Ghost readers I also thank you for reading love u all.

Bayan wasu kwanaki

Cikin kwanakin abubuwa da dama sun faru wasu masu dadi wasun ko ba dadi

Maganar su fatima da hamma abun dai ba dadi sam har ta kai ga mami kwanciyar asibiti sakamakon hawan jinin ta daya sake hawa ta kwana daya sannan aka sallameta.

Don kiri kiri ta nuna nasir take so.

Bayan ya gayamata akan yana sonta nan take ba kunya tace ita bata son sa tana da wanda take so kuma shi zata aura, ya dauki abun wasa ne ko kuma jan aji irin na mata, bayan kwana biyu ya sake tuntubarta da maganar hakanan ta rufe idonta ta sake maimaita abunda ta gaya masa kwana biyu da suka wuce.

Wannan karon dama sunyi da nasir akan yau zaizo wurinta nan tayi mishi text akan yazo da wuri kuma yanzu

Bai kai minti goma ba ya iso gidan. Kamar dama jira yake ta kira sa.

Nan ta gabatar dashi ga mahmud akan shine wanda take so. bacin rai daya shiga yasa bai tsaya amsa gaisuwar da nasir din ke masa ba

Sai ya shiga motar sa kawai tare da barin gidan bakidaya batare da yayi sallama da kowa ba.

Yaje gida bai kwana cikin kwanciyar hankali ba washe gari da sassafe ya je asibiti don ya kwana da ciwon kirji nan aka bashi maganin da yakamata duk da yana likita ba zai iya yiwa kansa komai ba a wannan lokacin.

Hakan nan ya dawo gida ya fara shirye shiryen komawa uk.

Cikin kwana uku komai ya kammala

Loƙacin da yazo yin sallama da mami ne

Mamin ke bashi hakuri akan abunda ya faru don itama bai kare musu da dadi ba da fatiman

Ta bita da rarrashi, shawara da fada duk abanza taqi ita nasir take so kuma shi zata aura.

Sadiq har dukanta yayi amma a banza.nan kowa ya zuba mata ido aga iya gudun ruwanta.

Lokacin da zai tafi ne muka dan kebe dashi ya mika min ledan da yazo dashi yace ga tsarabarki na karba nayi masa godiya da fatan sauka lafiya

Duk banji dadi ba da halin da fatima ta nuna mana ta nuna bata jin maganan kowa balle shawara ra'ayintan nan ba mai chanja matashi koda waye ne

Yanzu haka tsakanin ta da mami gaisuwa ne kawai don mami ta dau fushi sosai akan ta duk da fushin mamin bata fasa hira da nasir din ba

Yazo ya gaida abba sau daya dama har da mami yake son ƴa gayar amma tace ita ta yafe gaisuwan.nima alokacin ne na ganshi iya haduwa ya hadu gashi fari ne ya bar saje a fuskan shi sannan yana da tsayi bai da jiki sai muscle daya tara dan gaye ne na karshe don rabin rayuwar sa a us yayi wayayyene sosai.

Inaji kyawun siffan sa shi yaja fatima zuwa gare sa.

Gefena kuma gashi nan dai shima don zuwan Dr deedat biyu daya shi kadai daya kuma da mahaifiyarsa a zuwa na biyun ne yake gayamin shifa yana sona kuma da aure ,ya gayamin takaitaccen tarihin rayuwar sa

MUJARRABI.( Completed)Where stories live. Discover now