Mujarrabi
By snow white
In the name of Allah the most high and merciful
Quran: Al-Israa (17:81)
وَقُلْ جَآءَ ٱلْحَقُّ وَزَهَقَ ٱلْبَٰطِلُ إِنَّ ٱلْبَٰطِلَ كَانَ زَهُوقًا
And say, “The truth has come, and falsehood has withered away; for falsehood is bound to wither away.”
Kamin ya samu ya kaiga abba yaji an riga an daura auren islam da Ahmad
Qirjin sane ya buga da karfi ya dafeshi da hannu yana neman faɗuwa wanine ya taimaka masa ya riqesa ya zaunar dashi akasaBayan wasu daqiqu ne ya samu ya fita daga wurin bai zarce ko ina ba sai asibiti anan ya kwana washegari yana samun sauki ya koma wurin aikinsa ba tare da sanin kowa ba shikenan ya rasata ta auri wani bashi ba kai islam kin cutar da zukatan mu a banza niba farin ciki ba haka na san kema ba farin ciki zaki samu ba amma duk da Haka Allah yasa shine mafi alkhairi a garemu bakidaya, hakan nan ya dai na fita yana zaune sai sunayen Allah da yake kira da kuma nafilfilin daya dage dasu ya san ba don haka ba da bazai kai labari ba don yadda yake jin radadi cikin zuciyarsa,gashi Dr yace ya rage tunani koda akace za'a gayawa iyayensa don su san yadda za'abi dashi ya hana Dr da yake abokin aikin sane anan barac din yake aiki ya kudurta a ransa sai ya taimakesa zai samu ko da abba ne ya gayawa maganan ciwon nasa.
******************
Baƴan daurin aure da daddare aka mika ko wacce dakin mijinta saide muce Allah ya basu zaman lafiya
Amare sai kuka suke na rabuwa da iyaye islam dai kukanta da biyune na rashin Abdallah da kuma barin gida ga abba ko daurin auren bai zoba baya ma kasar baki daya
Abu goma da ashirin sun hade mata ta rasa ina zatasa kanta taji sanyi.
Fatima da nas dai tamkar su hadiye junansu mutane suna watsewa suka fara gudanar da soyyayar su tamkar su hadiye juna don so
Gefen islam kuwa mutane na watsewa bayan shudewan wani lokaci saiga ango da abokansa sunzo sayan bakin amarya bayan gaisuwa sukayi musu nasiha sannan ya rakasu waje
A lokacin ne ta karewa gidan kallo apartment ne mai dakuna uku wanda aka zuba kayan more rayuwa sai masha Allah taketa maimaitawa cikin zuciyarta ganin kudin da aka zuba ko iyayen tane suka mata aure ba zasu wuce haka ba abba da mami sunyi rawar gani sai addu'a take musu na fatan gamawa da ɗuniya lafiya Allah kuma ƴa kara tsawon rai da nisan kwana
Tana kitchen tana dubawa taji hayaniya daga waje muryar mace cikin fada amma bata iya jiyo me suke cewa
Nan ta matsa ta gefen taga taga dr deedat da wata wanda yake nuni da matarsa ce a harabar gidan ta msha gabansa sai masifa take wanda bata iya jinsu don nisan dake tsakanin su nan take ta juya ta rufe tagar tare da dafe kirjinta tace na shiga uku na yau nan kuma na kawo kaina?
Na koma palo na zauna lokacin na daina jin hayaniyan, ina nan zaune har shadayan dare ba deedat ba alamansa na gaji na kulle kofata na chanja kaya zuwa na bacci na kwanta tare da shafa jikina da addu'a nan take baccin gajiya ya kwaceni
Dr deedat na chan yana fama da soffy wanda yau a buge take bai taba sanin sofy na shaye shaye ba sai yau daya gani da idanunsa daman rayuwar data daukowa kanta kenan har da shan giya wa iyazubillahi haka nan ya daddage ya kaita dakinta da kyar tayi bacci sai sambatu take akan ya yaudareta bai riqe amanan dake tsakanin suba lokacin har shabiyu tayi
Yana komawa site din islam, ya santaji komai daya gudana tsakaninsa da sofy ya san kuma by now ta tsorata da tarbar data fara samu agidansa but he promised this will never happen again, yana taba kofan ya jita a kulle baiso hakan ba daga zuwanta ta fara ganin dramar gidansa, yaso tun yau ya fara janta a jiki kamin one month data bayar ya iso yasan kamin nan ya shawo kanta amma ba komai gobe ma rana ce
YOU ARE READING
MUJARRABI.( Completed)
Randomlabarin wata yarinya da ta rasa mahaifiyar ta Tun tana karama. ta taso a wurin kanwar mahaifiyarta, (mami) ta nuna mata kauna sosai sai qaddara ya shiga tsakanin ta da wacce ta tsane ta rayuwa ya juye mata lokaci daya. Ta fuskaci qalu bale kala ka...