part 28

213 28 2
                                    

MUJARRABI

BY SNOW WHITE

Narrated Abdullah ibn Amr ibn al-'As: The Prophet (peace_be_upon_him) said: Those who do not show mercy to our young ones and do not realise the right of our elders are not from us.
[Dawud 41:4925]

Karfe huɗu dai dai na  shiga kitchen don yin girki,zan dafawa yaya abdallah abinci don tun ranar da yazo ni ke dafa mishi duk abunda zaici bai cika cin abincin da ƴan aiki suka dafa ba sai kuma in hajiyarsa ce zata dafa ita kuma bata cika dafawa ba kwanan nan ƴarta zuwaira tana ɗan laulayi kullum suna hanyan asibiti.

Na mishi liver sauce, fried rice and chicken da kuma friut salad. ban qare da wuri ba har goshin magariba na shiga daki don yin wanka.

Fatima na samu a dakin tana waya da saurayin ta mai suna Nas, sai murmushi take kamar gonar auɗuga ko wacce akayiwa albishir da aljanna.

Kwana biyu da suka wuce iyayen shi sunzo yin gaisuwa abba ya karbe su hannu bibbiyu duk da shima baiji dadin yadda taqi yiwa mami biyayya ba, amma ɗan yau ka haifesa baka haifi halinsa ba, yayi qoqarin nusar da ita akan tabi maganar mami ɗon shima hankalin shi yafi kwanciya da mahmud  akan nasir din amma fir taqi yarda tace ita zabin ranta take so bata son auren dangi, yayi yayi taqi ba yadda ya iya kawai sai yace mata ta  cewa yaron ya turo iyayen sa.

Amma ta sani duk abunda ya biyo baya tayi kuka da kanta,kar yaji kuma kar yaga wani abu cikin rayuwar aurenta zaiyi mata duk abunda ya kamata iyaye suyiwa ƴaƴan su yayin da suka tashi yin aure.

Ta yarda kuma ta amince akan hakan.

Ba tare da bata lokaci ba iyayen nasir sukazo aka sa rana nan da wata uku mai zuwa.

Ranar sun kwana suna waya tsaban murna don zasu mallaki juna a matsayin mata da miji.

Sanda na fito daga wanka fatima bata a dakin, na zauna a kujerar dreesin mirro, na dan shafa mai kadan don garin yau da dan zafi zafi sakamakon ruwan saman da ke son saukowa ko yanzu ko anjuma, gown na fitar  mai zanen flower green and orange na saka, ya matukar karbata don dinkin ya hadu abunda ma yasa nake son kayan kenan don kyan dinki shi kesa mutum yaso kaya,  nasa man baki kadan da powder na daura dan kwali na step step nan nayi sallan magariba don ankira sallah, ina idarwa na tashi na fita daga dakin don kaiwa yaya abdallah abinci.

A kofar dakin na hadu da mami tana shigowa dakin da charbi a hannun ta nan taja birki ta tsaya tana kare min kallo.

Ta kalleni daga sama har kasa sannan tace sai ina kuma da daddaren nan daman bata nan ta fita tun bayan sallan la'asar.

Ba inda zanje mami ina nan cikin gidan nan

shine kikayi ado kamar mai fita unguwa

Murmushi kawai nayi

Dama wurinki nazo keda khadija
Ina take ne yau kwata kwata ban ganta ba wai meke damunta kwanan nan ne?bana gane kanta kullum sai ta kulle kanta a daki yanzu fin wata daya kenan ta chanja completly bata shiga mutane gashi ta zama wata shiru shiru.

Nima mami naga chanji sosai a wurinta kuma duk tambayan da namata sai tace min ba komai.

Ko dai bata da lafiya ne cewar mami

Anya kuwa kamar fa wani abun ke damunta don yawan zurfafa tunani da take, ko mutum ya mata magana bata amsawa saika taba ta kuma ta rage cin abinci yanzu kullum sai tace batajin yunwa, Amma mami karki damu zan fara bincike akanta zan gane me ke damunta insha Allah.

To shikenan islam don Allah ki binciketa don nima iya sanina da ita tana gayamin komai dake damunta amma yanzu komai na tambayeta sai tace ba ƙomai.

MUJARRABI.( Completed)Where stories live. Discover now