💥💥💥💥page 47-48💥💥💥💥
Written by
M. HANNA 💦💦💦💦💦💦💦Edited by
💫💫💫💫💫M. HANNAStory by
M. HANNA 💎💎💎💎💎💎💎💎Tsab zaynab da samira suka shirya cikin wani lafiyayyan lace purple riga da sket, suka dora mayafinsu black akan kafada sai wasu black flat shoes masu stones dake kan kafafuwansa wadanda suka sha zanenn lallen hausa red, yayi kyau sosai, hanan ce ta fito itama cikin kayan irin nasu amma sedai ita nata lace din red ne kallo daya idan ka mata zakaso ka sake mata dayan, samira tace basai na maganta ba ayyi wannan wankan naki albarka koda kuwa yau ne zamu kai ki gidan ameer, murmushi tayi tace uhmmm kudai akeji mahaukaci ya fada rijiya yace wanka nake, haka dai sukasa kai suka fice
******basuyi birki ko ina ba sai gidansu hanan ma'ana gidan Alhaji Ahmad zaki, nan aka wangame masu gate din gidan inda suka karasa har compound din gidan sukayi parking, chak bayan hanan ta karasa parking din tayi shuru ba tare da tayi kokarin fitowa daga motan ba, samira dake gefenta tace ya akayi? zaynab dake baya tace tana tunanin yanda zataje da maganar ne agabansu mummy, musamman daddy, hanan tayi murmushi tace gaskiya inajin dadin zama daku saboda kusan kuna karantar abunda yake raina, wallahi zaynab hakane, ina tunanin yanda zan shiga da zancen ne, zaynab tace kinga tashi muje in sha Allahu zaa dace, haka suka fito suka karasa cikin gidan sanadiyar yau kofar gidan tana bude
******shigarsu ba kowa a falon ko ina tsit, sallama suka shiga yi, hajia maryam (mummy) ce take amsa sallamar daga wata corridor wacce zata sadata da falon gidan, cen suka tsinkayota tana takonta cikin salo da isa harta karaso, murmushi tayi tare da tabe baki tace aaaah zaynab kune? har kasa suka sunkuya suka gaidata harda hanan, ta amsa masu cikin sakin fuska kana suka karasa falon suka zauna, nan ta kawo masu abun sha da snacks, zaynab da samira ne kawai ke cin abunsu, hanan tana gefe zaune zuciyarta sai duka take uku uku, mummy dake zaune akan dayan kujeran ta fahimci yanayin hanan sosai, hakan yasa ta katse shurun da lafiya kuwa hanan? sai lokacin ya dago tana smiling na dole tace lafiya lau mummmy
******dama gunku nazo dake ba daddy, inada maganar da nakesan muyi daku about ikram, cikin rashin fahimta mummy ta murmusa tace uhmmm ikram kuma ta mutu ne? hanan tace haba mummy wane irin mutuwa kuma sai kace wacce aka kashe, mummy tace aaaah toh naga kun sakata gaba dake da mahaifin naki shiyasa nayi tunanin hakan, statement din mummy yasa su zaynab suka tsaya chak tare da aje tumbler glass cup dinda ke hannunsu, samira tayi gyaran murya tace kiyi hakuri mummy, nasan wannan ba hurumina bane, amma inada tambayar da nakesan na maki dan Allah, hanan ta maida dubanta kan samira, zaynab ta lumshewa hanan ido ma'ana kada ta damu
*******mummy tace ayyi dukan ku yarana ne, inajin ki, samira tace misali yanzu ace maki ikram tanada juna biyu wane irin mataki zaki dauka? mummy tayi murmushi tace uhmmm ayyi wallahi zanfi kowa farin ciki da jindadi saboda kowa zaiso yaga jikansa, na mata tanadi na musamman ga bikin aurenta inaga ace har nakai ga grandchild ayyi abun baa cewa komai, samira tace mummy ina maki tambayar ne ba akan ikram tayi aure ta samu juna biyu din ba Kafin tayi aure nake magana? mummy ta dan soma girgiza kanta dama da hauni kana tace kai koh alama samira kidaina wannan zance marasa dadin ji na yarda da halayen ikram sosai nasan bazata tabaman aikin asha ba, dama ace hanan kikace wannan kam zance zata iya yin fiyema da hakan, samira ta kara gyaran murya tace uhmmm mummy kenan, meyasa kika dauka cewa hanan macen banza ce, wallahi mummy kina daukan alhakinta sosai, tabbas hakane so da yawa zaka haifi yaro amma baka haifi halinsa ba amma har ga Allah kin haifi hanan kuma kin haifi halinta saboda albasa tayi halin ruwa, sosai hanan takesan cigabanku duka amma koda yaushe furucinki akanta bai wuce na batanci ba ko tsinuwa which is very wrong kada kimanta fah mu yara kiwo ne agurinku wallahi yanda kuke da iko akan mu haka muma muke dashi akanku, yanda kuke da hakki akanmu muma haka muke dashi, akwai fah hisabi tsakanin uwa da danta, idan kikaje mezaki cewa Allah game da kiwon da ya baki?
YOU ARE READING
AURE NAKESO 💔💔💔💔💔
Short StoryMatasa ne mata uku, masu kudi, masu kyau, komai sukeso na duniya Allah ya basu but they are looking for true love, let's see how it gonna roles💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞shin zasu samu koya?