Page 93-94
Edited by
M. HANNAStory by
M. HANNAWritten by
M. HANNACast
Hanan
Ikram
Zahra
Khalifa
Khalid
Sagir
Ameer
Aminu
Farhan
Nawwara
Aisha
IYYA nd other's ✅✅✅✅✅✅✅✅✅✅****FLASH BACK******
Bayan wucewar zaynab batayi birki ko ina ba sai gidansu, nan tayi horn aka wangame mata gate din gidan, haka ta shiga zuciyarta tana duka uku uku, nan ta fito ta karasa cikin gidan ba tare da ta dauki komai a mota ba daga ita sai car key dinta da waya,fallo ta shiga wanda bakowa acikinsa, makeken TV dinda yake falon ma akashe yake, wani duka taji zuciyarta tayi dakyar ta iya hadiye yawun bakinta, bakin dauke da sallama harta karasa dakin mummy, ahankali ta tura kofar dakin ta hango mummy zaune akan sallaya tana lazimi, sallamar zaynab yasata tsayawa chak tace wa'alaikissalam aaaah zaynab kece, shigowar yaushe? zaynab ta zauna abakin gadon tana fadin yanzun nan mummy nayita sallama naji shuru, mummy ta karasa komai nata ta mike tsaye tare da cire hijab din wani irin kallo take yiwa zaynab mai dauke da alamun tambaya, take zainab ta fahimci abunda take nema, murmushi tayi tace uhmm mummy kenan, juna biyun kike nema koh? mummy tayi murmushi tace toh mezaisa na dinga maki wannan kallan banda juna biyu
*******zaynab tace na samu miscarriage bayan na dawo ranar da kika kirani, mummy tace innalillahi wa'inna illaihir raju'un saida nace kada ki dawo a daren ranar, subhanallah magana ce bakyaji wallahi zaynab kinfi kowa sanin mai juna biyu ba'asan tana wani aikin wahala, sannu, shine ko ki kira ki sanar dani? Shima khalifa bai kirani ba, zaynab tayi murmushi tace kiyi hakuri ni nace kada ya sanar da kowa wallahi, mummy tace toh Allah ya kawo wani mai albarka, zaynab ta amsa da ameen tana kokarin kwanci akan laps din mummy, shurun da tayi ne, yasa mummy ta shiga shafar gashin kanta ahankali tana smiling, aranta kuwa cewa tayi she's missing me alot, shedaniya, ahaka dai suka yini ranar
******bayan sallah magrib mummy ta ga alamun zaynab bata batun zuwa gida tace bazakije gida bane yanzu? zaynab dake zaune tana kallan kwana casa"in tace uhmmm baya gari mummy so shiyasa yace nazo gida na samu company, mummy tace toh ina akwatin naki? zaynab ta turo baki tana fadin yana mota, mummy tayi dariya tace okay toh yayi, nima dai daddy dinki baya gari sai muyita zama
*****STORY CONTINUES*******
Kwance zaynab take tana kallo a apple ipad dinta wani film ne take kallo mai suna adamun adama sai smiling take abunta, knocking dinda akayi ne yasa ta dago tana kallan wanda zai shigo mummy ce ta shigo hannunta dauke da dan karamin farati mai cup a sama, tana murmushi tace abun nema ya samu tashi kisha turmeric drink, wani ya mutse fuska tayi tana fadin Allah mummy banasan sa, murmushi mummmy tayi tana fadin ayyi ba dole sai abunda kikeso ba zaynab, wannan kadai idan kika dage da shansa zai gyara maki jiki oya tashi kinji, haka ta tashi mummy ta kai mata cup din bakinta saida ta shanye duka sannan ta koma tayi kwanciyarta, gefenta mummy ta zauna itama tabi sahun kallon nata, amma ga baki daya hankalinta yana kan zaynab, wacce duk wanda yasan zaynab farko yasan ta sauya sosai yanzu tamkar ba ita ba, haske kawai ta kara amma ta rame sosai, mummy tayi gyaran murya tace are you okay zaynab? ba tare data dago ba tace am fine mummy, meya faru? mummy tace bakomai, khalifa yana farantamaki rai kuwa kaman yanda yake nuna mana damuwarki damuwarsa ce? gabanta ne yayi mugun faduwa lokacin da tambayar mummy ta sauka a kunnenta, saurin dagowa tayi tana kallan mummy nadan lokaci ta kara sunkuyar da kanta tace bantaba sanin cewa haka halin khalifa yake ba, bantaba tunanin khalifa zaiman abunda yakeman ba, bantaba tunanin zai nunawa duniya ni ce ba sai yanzu, tabbas mummy zan bawa yan mata shawara da idan zasuyi aure suyi bincike sosai kaman yanda addini ya tanada saboda rashin hakan babbar matsala ce, mummy tace mekike nufi?******murmushi zaynab tayi kana tace saboda khalifa yana bani kulawa sosai, yana nunaman so da kauna kaman yanda yake nuna maku haka yake nunaman, komai nakeso shi yakeyi, bai taba tsangwamata ba, bai taba wulakantani ba, yana sona sosai zaynab ta karasa fadin hakan tare da hugging din mummy, mummy tayi murmushi tace Allah ne abun godiya, Allah ya kara hada kawu nanku, ya baku zaman lafiya sa hakurin zama da junanku
YOU ARE READING
AURE NAKESO 💔💔💔💔💔
Short StoryMatasa ne mata uku, masu kudi, masu kyau, komai sukeso na duniya Allah ya basu but they are looking for true love, let's see how it gonna roles💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞shin zasu samu koya?