Page 79-80
Cast
Hanan
Ikram
Zaynab
Samira
Zarah
Dr othman
Farhan
Sagir
Nawwara
Aisha
Malam Muhammad
Khalifa
Nd other's 💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥Story by✅✅✅✅✅✅✅✅
M. HANNA💜💜💜💜💜💜 Edited by
M. HANANWritten by
M. HANNA 💎💎💎💎💎💎💎💎Driving yake da waya a hannunsa wacce sensor din wayan ya nuna nawwara ce ke kiransa amma bai daga ba, kira na biyu ya kara shigowa wanda sai lokacin ya daga ba tare da yayi magana nawwara tace haba khalifa lafiya kwana biyu shuru? yace lafiya lau amma bakida mutunci nawwara taya zaki shanyani da sunan zaki nemeni amma kibawa banza ajiyata haba dan Allah cikin fushi yayi maganar, nawwara tace kayi hakuri wallahi tsohon aisha sai a hankali yanzu dakyar take samu tana fita wallahi amma yau ka gayaman inda zamu hadu sai nazo maka da ita, yace okay toh yayi zan turo maki address din kinada kudin transport? tace aaaah wallahi amma nasan bazata rasa ba yace nooo kada ki takurata bari zan turomaki, nan sukayi sai anjima, take yayi mata transfer din 20k, yayiwa aisha na 50k, tare sa turawa nawwara address din inda zasu sameshi
********ko wayan bai aje ba wani kiran ya shigo wannan karon kam mummy ce akan sensor dinsa, take ya samu guri gefen titi yayi parking bayan ya daga suka gaisa cikin girmamawa, yace kiyi hakuri kunjini shuru koh mummy? tace wannan kuma ayyi ya rage naka khalifa, yawwa ni kuwa ina ikram ne? yau kwana biyu da wata ta kirani taceman yar'ta ce da nace ikram sai ta katse wayan nayita kira bana samu ga alamu kuma kaman an sakani blacklist ne fah, kuma am sure ba ikram bace, so wacece ka bawa number? cikin rashin fahimta yace number kuma, ni ba wanda na bawa numberki, sannan ikram ma bata kasar nan, amma turoman number zan duba nagani, tace okay toh yayi kyau, wai yaushe zaka zama cikakken mutun ne khalifa wallahi ina son naga aurenka, dan Allah ka hanzarta, karatun nan dai angama sannan akwai business a hannu toh me ake jira? yace very soon mummy kiyi hakuri, ina baba? tace ya fita, nan dai ya tambi duka kannensa tace duka suna lafiya, nan sukayi sai anjima
*******bayan sun karasa wayan text ya shigo wayansa alamun ta turo masa number kenan, ya shiga text din kenan kira ya kara shigowa wayansa, kiran zaynab ne wannan karon ba shiri yayi rejecting kiran tare da kashe wayan ga baki daya ya aje kan seat din mai zaman banza, yaja wani dogon tsaki ya kama hanyarsa
********zaynab kuwa bayan barinta gidansu batayi birki ko ina ba sai gidanta, nan ta kasa zama bare tsayi, kofar farko ta shigowa gidan ta sakawa key, direct dakin khalifa ta fada nan take ta shiga masa bincike, daga wannan wardrobe zuwa wannan, haka taketa haukarta ita kadai, take takai ga files dinsa na makaranta da komai nasa, nan ta shiga dubasu saya bayan daya, nan takai ga number mahaifinsa da ta mahaifiyarsa wadanda suka zama tamkar guidance akan form dinda aka cika nan ta dauki number ta kira ta mahaifin bayan sun gaisa, tace daga office dinda yake aiki ne, tana magana da Alhaji ABDULLAHI, Yace sosai kuwa shine, nan take tace suna san ganinsa urgently yana wane gari ne? Yace mata yana zamfara, nan ya bata address din office dinsa tace idan ta shigo zata kirasa, nan ta zame ta zauna gefen gadonsa tana salati, murya cen kasa tace idan wannan shine mahaifin khalifa then wanene wanda yaje neman aure na?
*************yoooooh ina kuwa zasuyi laifi tun suna kirana da baffah yanzu sun dawo suna kirana da baba, ummah hanne mai dakinsa dake zaune a kofar dakinta tace yoooh ayyi baka aikin da mai suna baffah keyi, yanzu kaji malam yaushe rabon da ka bada kudin cefane? shuru yayi nadan lokaci kana yace banida shine, ayyi da inada shi da zan bada koh? hanne ta tabe baki tace wannan kuma turancin ba nawa bane gaskiya saboda auren mu ba auren da aka daura jiya bane nasan ka sosai, na kuma san halinka dan haka babu abinci saboda baka kawo ba, cikin takaici yace toh me kikeyi a kitchen dazu? hanne tace girki mana amma girkin cikin mutun uku daga ni sai yarana, yace toooh lallai hanne kin zama yar wuta kenan, Karfah kimanta aljannar ki tana kasan kafafuwana, hanne ta mike tsaye ta gama masa kallo kana tace dan Allah idan kai zaka bani aljannah kada ka bani ita nan tasa kai ta karasa cikin dakin nata tana fada
VOUS LISEZ
AURE NAKESO 💔💔💔💔💔
NouvellesMatasa ne mata uku, masu kudi, masu kyau, komai sukeso na duniya Allah ya basu but they are looking for true love, let's see how it gonna roles💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞shin zasu samu koya?