🔝🔝🔝page 71-72🔝🔝🔝
Cast
Hanan
Ikram
Samira
Sagir
Aisha
Nawwara
Ameer
Khalifa
Aminu
Zaynab
Zahra
Ummah hanne
Malam muhammadNd other's all in🔛🔛🔛🔛🔛🔛🔛🔛🔛🔛
Written by
M. HANNA 🔯🔯🔯🔯🔯🔯🔯🔯🔯🔯🔯💎💎💎💎💎💎💎Story by
M. HANNAEdited by
M. HANNA 💢💢💢💢💢💢💢💢💢Sagir yayi murmushi yace toh mummy, duk yanda kukayi ayyi daidai ne dan haka banida matsala, amma zan turo maki number ita yayarta sai kuyi magana, waya yake abunsa, zaune yake akan booth din motarsa cikin kananun kaya riga fara wando baki, yaiyi murmushi yace toh sai na turo kiyiwa daddy maganar okay? dayan bangaren tace okay son ba matsala sai na kiraka, bayan sun karasa wayan, ya sauko daga booth din motarsa ya dawo cikin motarsa ya shiga ya fice abunsa
*******bai taka birki ko ina ba sai kofar atiku daidai gidan malam muhammadu yayi parking, bayan ya kira shi yace ina waje baba, yace toh toh gani nan zuwa, bayan fitowar sa yayi tsaye yana kallan tsadaddiyar motar da ke fake a kofar gidansa, murya cen kasa yace uhmmmm toh wanene wannan mai shamshakiyar mota? bai karasa rufe bakinsa ba sai ga sagir agabansa yana baba ina wuni, hannu ya mika masa suka gaisa bayan sun gaisa sagir yace ko zamu karasa mota baba? malam muhammadu yace eh muje gaskiya kowa yana bukatan sirri, tare suka karasa cikin motan sagir, bayan yan mintuna, malam muhammadu yace toh Allah yasa lafiya kake nemana? sagir yace lafiya lau baba, ahankali ya dauko tag dinsa na aiki ya nunawa malam muhammad tare da cewa am secret servant of police, am sagir by name, cikin razana malam muhammadu yace kaman boyayyan dan sanda fah ake nufi da hakan? sagir yace kwarai ma kuwa baba shine
********malam muhammadu yace innalillahi wa'inna illaihir raju'un na shiga uku ni kuwa mena maku kuke nemana haka? nida banida kudi, banida mota, banida kuma gida ko abunda zaace kudin government ne, sagir yayi murmushi yace ka kwantar da hankalinka baba, nasan da hakan sosai, sannan da ace tashin hankali nake nema da bazanzo maka cikin wannan yanayin ba, dan haka ka kwantar da hankalinka, ka bani hadin kai kaman yanda ya saba idan ba haka ba sai kasa ni yin abunda banida niyar yi, malam muhammadu ya soma gumi tako ina, sai karkarwa jikinsa keyi, yana lumshe idanuwa tamkar wani tsohon maye, idanuwansa sukayi turuturu tare da yin jawur tamkar wanda yayi yaki da barkono
************ganin yanda ya wani rikicewa sagir yayi murmushi yace baba dan Allah ka kwantar da hankalinka, daga ni sai kai nakesan muyi wannan maganar, malam muhammadu ya wani shan toka tamkar ba tsoro yaji ba, yace eh eh toh toh mekakeso na maka ne? ba wani tashin hankalin da nake ciki kawai dai bansan meyasa kake nemana ba, sagir yace zan maka bayanin yanzu in sha Allahu, ahankali ya bude side durowa ta mota ya dauko wani envelope fari yace toh baba ga wannan koh? malam muhammadu ya karba yana satar kallan sagir, bayan ya karba sai ya juya envelope din gaba da baya yace shi kuma wannan menene?
*******sagir yace idan kaje gida zaka gani amma fah yanzu ba zamuyi maganar komai ba kaje duk lokacin da ka shirya sai ka kirani muyi magana, malam muhammadu yace uhmmm yoooh ina zakaje tunda dai gani Allah ya kawoma ayyi sai ka gayaman dalilin da yasa kake nemana koh? sagir yace toh baba tunda haka kakeso banida matsala saidai fah ka tabbatar idan na tambaye ka zaka gayaman tsakani da Allah, ni kuma zan maka alkwarin maka duk abunda kake so, sannan daga yanzu nakesan mu fara mekakeso yanzu a rayuwar ka ta duniya? malam muhammadu ya girgiza kansa tare da cewa ikon Allah, ni yanzu ayyi banida burin da ya wuce naga nayi kudi wallahi, ko bakomai a kirani da Alhaji muhammadu mai dollar
**********sagir yayi murmushi yace uhmmmm lallai kuwa meze hana ka zama Alhaji muhammadu mai dollar idan ma shirya zama? malam muhammadu ya kara gyara zamansa tare da saka envelope dinsa a aljihun wandonsa yace toh na shirya ta ina zamu fara? 💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥
ŞİMDİ OKUDUĞUN
AURE NAKESO 💔💔💔💔💔
Kısa HikayeMatasa ne mata uku, masu kudi, masu kyau, komai sukeso na duniya Allah ya basu but they are looking for true love, let's see how it gonna roles💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞shin zasu samu koya?