AURE NAKESO book one

886 49 1
                                    

💔💔💔💔page 43-44💔💔💔

💚💚💚💚💚Edited by
M. HANNA

💕💕💕💕💕 Story by
M. HANNA

Written by💙💙💙💙💙
M. HANNA

Daga wannan lokacin rayuwar ameer da hanan ta sauya zuwa soyayyar tsakani da Allah, mace indai ba hanan ba toh baya bata lokacinsa gurin mata magana ko ya kulata, komai ya dauko hanan, ina zaka hanan, ina ka fito hanan, komai nasa hanan ne, sosai takejin dadin zaman nasu na yanzu saboda ko bakomai tasan tanada tsayayyan miji yanzu a gefe

******toh daddy sai ya kenan, ayyi ganin nayi hakan shine zaifi mana sauki ga baki daya shiyasa after case din na tura ta karatu, hanan ce zaune a falon gidansu tare da mahaifinta, yayi murmushi yace Allah kadai ne zai iya biyanki hanan kin mana komai, yar daya tamkar dubu, Allah yasa hajia maryam ta fahimci intention naki,hanan ta mike tsaye tace uhmm daddy kenan, tunda kai ka fahimta ayyi komai ya kara dama kaine mai iko akanmu kaine dinka da shanmu yake kanmu kuma kayi kokari dan haka kawai ku mana addu'a, mahaifin hanan yace Allah sarki my daughter Allah ya kara tsare mana ku, tace toh daddy am going nan ya rakata ta shiga mota tayi tafiyanta

*****dawowarsa kenan hajia maryam ta fito daga dakinta, kana ta banka masa wata uwar harara tace wato da hadin bakinka akesan a kasheman ikram koh? wai meyasa kakeman haka? wallahi da ace bani nayi nakudar hanan ba da nace turoman ita akayi ta kasheman aure, yarinya da makirci irin na manyan mata, inka ganta simi simi kaman ta Allah, nan taja wani dogon tsaki ta fice abunta, daddy dai kala baice da ita ba, hasalima cigaba yayi da kallan BBC dinsa

*******isowarta gidanta kenan ba wuya, ta samu su zaynab zaune a gardner suna hutawa tana fitowa nota direct gunsu ta karasa, bayan sun gaisa ta hanyar musabaha da juna ta zayna tace sai hutawa kuke babes, samira tace toh ya muka iya? zaynab tace kinyiwa su mum bayanin condition din ikram kuwa? hanan ta dan tabe baki tace wallahi banyi ba , kinsan yanda mummy take, daddy kuma nasan mutun ne mai yadda da kaddara duk yanda tazo masa, so nayi deciding sai ta karasa school, ta haihu ta samu wanda zai aureta a hakan sai na fito da zancen, kinga if she's around zata sanar dasu da bakinta, samira tace kinyi gaskiya hanan, toh Allah ya sauketa lafiya, na tabbatar duk inda mijinta yake he will surely find her

*******zaynab tace sosai kuwa in sha Allahu he will, hanan tace F. H bai zo ba ne? samira tace F. H kuma me haka? ke komai sabo abakinki muke jinsa, samira tace uhmm FUTURE HUSBAND take nufi mana girl shine your eyes dan Allah, nan sukayi kwa da dariya, nan sukaci gaba da firansu bayan sun amsa mata da baizo ba

********bangaren serg sagir kuwa, dakyar ya iya karasawa gida, bayan isarsa ya shiga safa da marwa a tsakiyar falon sa chak ya tsaya tare da cewa ina zan fara neman ikram? Have been looking for her but all not available ta ina zan fara, charab yayi ya dauki wayansa dake kan center table ya kira hanan wacce yayiwa saving da aunty hanan, ringing daya zuwa biyu ta daga bayan sun gaisa ta danyi shuru nadan lokaci kana tace wake magana? serg sagir yace uhmm aunty hanan serg sagir ne, kiyi hakuri na kira ki a wannan lokacin inasan magana dake dan Allah karki ce dani aaah, hanan tayi murmushi tace ba matsala bane sai kazo gida, sagir ya dauki car key dinsa ya fice cikin hanzari

******isarsa ba wuya ya sameta a falo da ita da su zaynab sai wasa da dariya suke, nan suka zauna bayan sun gaisa, yayi shuru, hanan ta mike tsaye tace ka tazo muje koh? Tana gaba yana biye da ita a baya, har suka isa wani dan karamin falo madaidaici mai dauke da royal cushines masu kyawun gaske, bayan sun zauna ta dora kafa daya akan daya tayi shuru tana kallan sagir wanda ya donar da kansa akasa hanan ta katse shurun da sagir lafiya kuwa kakesan gani na?

********sai lokacin ya dago kansa sama tare da murmushi yace uhmmm kiyi hakuri sister hanan, naso na boye abunda yake raina amma na kasa dama bakomai bane face zancen ikram, cikin rashin fahimta tace ikram kuma meta maka? yayi murmushi yace ba abunda taman hasalima nine na mata laifi sanadiyar kasa kasancewa da ita alokacin da tafi kowa bukatana, ki taimakaman aunty hanan wallahi na kamu da son ikram wuce inda bakya tunani, nasan ke kadai ce zaki isar dani inda take please help me, hanan ta danyi shuru, kana tace kayi hakuri sagir, ikram ba tsaranka bace, kafi karfin ikram, a halinda take ciki yanzu bana tunanin akwai namijin da zai iya zama da ita, sagir yayi murmushi yace wane irin hali ne ikram zata shiga da zaisa namiji yakita aunty hanan? Hanan ta mike tsaye ta huro iska mai zafi daga bakinta tace kaga sagir ya isa haka, kaje ka nemi wata daban dan Allah, ikram is not yours nd will never b yurs, nagayamaka bata bukace da namiji yanzu

"*******har zatasa kai ta fice sagir ya mike tsaye yace kina tunanin koda akwai namijin da zai guji ikram ina cikinsu ne? bana cikinsu aunty hanan, nasan cewa ikram tana dauke da juna biyu sannan ga duk kan alamu cikinta ya tsufa yanzu shiyasa kika boyeta saboda gudun abun kunya, nasan da cikin ikram tun day one dinda na fara ganinta, but anyway bakomai kiyi tunani akan zancen nawa, ina sonta kuma am ready to spend d rest of my life with her nor matter what, haka yasa kai ya fice daga falon, yabar hanan tsaye cike da mamaki da kuma ikon Allah

********dakyar ta iya komawa akan kujera ta zauna tare da dafe kanta

*****cikin hanzari sagir ya fice ba tare da yayiwa su zaynab sallama ba, hakan yasa samira tace lafiya kuwa? Zaynab ta tabe baki tace i don't know, amma muje mugani koh, cikin hanzari suka karasa falon, zaune yanda mukabar hanan haka suka sameta, samira da zaynab suka kalli juna kana suka karasa, gefenta suka zauna, samira ta dafa kafadarta tace lafiya hanan? ahaka ta dago tayi murmushi tace ina kuwa lafiya take samira, zaynab tace me kuma yazo dashi? hanan tace ba wani abu bane zuwa yayi yagaman yanasan ikram da aure, shine yakesan na hada su, samira tace alhamdulillahi, toh ayyi wannan abun farin ciki ne, sannan abun jindadi ne, meyasa kika shiga damuwa? zaynab tace haba samira ki tuna fah da condition nata, sai lokacin samira tace uhmmm hakane kuma amma ayyi kaddara tana kan kowa, hanan tace ayyi duk ba wannan ne tashin hankalina ba

******do you know dat sagir yasan da cewa ikram tana dauke da juna biyu tun day one, samira da zaynab suka dafe kirji tare da cewa what? hanan ta koma ta jingina gadon bayanta akan kujeran tace uhmmmm shine damuwata fah, samira tace uhmmm toh ayyi inaga komai yazo da sauki tunda har yasan da halinda take ciki,zaynab tace da maganar ki kuma samira ayyi hanan bakomai bane wannan kawai,  zaynab tace, masharuwa fah magini karki manta, hanan tace hakane fah da zancen ba matsala bane dan haka, I will do as you all said, samira ta rungumota tace ma sha Allahu shiyasa nake  mutuwar ji dake wallahi, haka suka zauna sukaci gaba da firan tasu

*********** bayan komawar sagir agida, kasa zama yayi, tsayi kuwa adaina maganarsa, haka ya shiga shirya akwatinsa,tsab ya hada kayansa, kana ya fice abunsa,fitowarsa kenan, ya saka Kayansa a booth din motarsa, kana ya kira maigadinsa wanda ya karaso cikin hanzari ya durkusa agabansa sagir yace yau zanyi tafiya zuwa kaduna, dan haka ka kula da gidan nan sosai, haka ya saka hannu a aljihun wandon sa ya zaro yan kudade, kana yace ga wannan ka dinga cin abinci har na dawo, cikin girmamawa ya karbi Kudin yana masa godiya, ahaka ya wangame masa gate din gidan, ahaka sagir ya kama hanyarsa ta zuwa kd, gudu yake kaman zai fira sama

********hanan ce zaune a falo dasu zaynab yau kam harda ameer, yayu murmushi yace naji zancenki, yanzu meyasa bazaki basa damar zuwa gida yaga su mummy ba? Hanan tace uhmm taya zan iya hakan bayan su mummy basuda masaniyar komai dangane da cikin ikram, ameer yayi murmushi tace com on hanan, kiyi hakuri, ki je Kiyiwa su daddy bayani na fahimta sosai, na tabbatar daddy zaifi kowa fahimtarki saboda yasan bazaki cutar da ikram ba, zaynab tace wallahi zancenka zanene akan dutse ameer, samira tace wallahi hakane hanan, talk to him Allah, nasan dai mummy  will b a bit angry but all will b right, ameer ya dan janyota jikinsa yace kiyi hakuri, haka ta kara shigewansa jikinsa tana smiling, zaynab da samira tace awwwwnnnnnn omo seee love

************haka dai suka yini sunta firansu gwanin ban sha'awa, ameer yace toh yanzu zai abu na gaba, ya ake ciki game da plan din neman khalifa ne? Samira ta tabe baki tace uhmmm wannan dan akuyar ayyi wallahi no more information game dashi, ameer yace nifah abunda yake bani mamaki daya ne, wai me police sukeyine akan abun? Hanan tace Allah they are trying too kasan yanda abun yake, ameer yace but wait a second  meyasa bazakusa serg sagir a case din nan tunda naga he's very smart, hanan ta dan tabe baki tace uhmmmm bana tunanin he's so good at dat, ameer yace nooo girl ayyi tunda ki kaga an masa transfer dat means he's very intelligent, hanan tace alright then zan kirasa, kura ga tsoro ga ban tsoro, ameer yace zama da madaukin kawa, samira ta katsesa da hausawa abeg kubarmu ahaka,



More vote
More likes
More comment
More post ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤

AURE NAKESO 💔💔💔💔💔Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin