AURE NAKESO book 🔯🔯🔯🔯

911 37 4
                                    

💎💎💎💎page 73-74💎💎💎💎

Cast
Hanan
Ikram
Zaynab
Zarah
Ameer
Aminu
Khalifa
Nawwara
Aisha
Ummah hanne
Samira
Sagir
Dr othman
Nd other's all in 💣💣💣💣💣💣💣💣

Written by
M. HANNA 💎💎💎💎💎💎💎💎💎

💢💢💢💢💢💢💢💢💢Story by
M. HANNA

Edited by
M. HANNA ✅✅✅✅✅✅✅✅✅✅✅✅

Hajia hajia hajia, hadiza, hadiza wai kina ina ne? mahaifin zaynab ne yake kwalawa mahaifiyarta kira tamkar bangon gidan zai tsage, cikin hanzari ta fito da sauri tace innalillahi wa'inna illaihir raju'un lafiya kuwa alhaji? tsaya ta samesa jikin kujerar dake falon ya cire glasses dinsa yace ina kuwa lafiya saboda ga dukkan alamu zaynab ta jawo mana abun kunya, cikin rashin fahimta tace kamanya kenan? yace toh........ Nan ya kwashe duk yanda sukayi da sagir ya gayamata, baki ta tabe tace chab gaskiya alhaji ba karamin tadaman da hankali kayi ba toh wannan ne abun tada jijjiyoyin wuya ayyi wanna bakomai bane, cikin rashin fahimta yace kamanya kenan? tace uhmmm kamanta cewa surukinka ba karamin mutun bane sannan fah karka manta businesses dinsu daga shi har mahaifinsa ba na zama guri daya bane dan haka ba mamaki akwai abunda yasa ake nemansa, sannan zaynab ta gayaman jiya da tazo cewa tunda sukayi aure baya fita sosai koda yaushe yana gida yana bata kulawa, sai lokacin ya dan saita natsuwarsa yace uhmmm kinfini gaskiya kuma anan fah, wallahi hankalina ne ya tashi kinsan banasan abunda zai tabaman reputation wallahi sannan kinsan auren nan na zaynab babu inda baije ba toh kinga kuwa bazanso wani tashin hankali ba gashi condition dinta ba maison kwaramniya bane, hajia tace hakane yanzu dai ka zauna ka huta bari na kawo maka ruwan sanyi

***********banida wani babban tashin hankalin da ya wuce wannan aunty hanan yanzu idan farhan ya tashi wane labari zan bashi, sannan kinsan ko bai nemi mahaifinsa ba yanzu zai nemesa in d future, hanan dake rike da tea cup tanashan coffee ta sunkuyar da kanta sanadiyar tsaye take bayan kujeran da ikram take zaune ta dafa kafadarta tace kinga dan Allah banasan kisawa kanki damuwa sannan duk wanda Allah ya rufawa asiri toh duk duniya babu wanda ya isa ya tona masa asiri, ki godewa Allah babu wanda yasan kinada ciki bayan zahra kuma na tabbatar zahra mai rufamaki asiri ce dan haka ki sawa zuciyarki ruwan zafi ki tuna cewa samun namiji irin sagir banan kusa ba, he's an angel send from god dan haka ki dage da addu'a

**********kai ta daga mata alamar eh, tace uhmmm kingani koh? wallahi hanan shiyasa nake gayamaki banasan abar ikram ita kadai saboda anything can happen to farhan wallahi, hajia maryam ce take maganar lokaci daya kuma take kokarin zama akan kujeran da ke gefensu, hanan ta zagayo ta zauna tare da dora kafa daya akan daya dubanta ta maida kan mummy tace haba mummy bana tunanin ikram zata iya kashe farhan saboda nasan tasan wahalar da tasha gurin haihuwarsa saidai kawai tunaninta na banza wanda bazai wuce daya zuwa biyu ba, mummy tace nidai inaga idan zan koma zan tafi da jikana saboda ko alama ban yarda da ikram ba akan wannan yaron, murmushi ikram tayi kana tace haba ummah me farhan yaman da zan kasheshi? kidaina wanna tunanin nida nakesan ya samu rayuwa mai kyau taya kike tunanin zan masa illa ko alama kawai dai ance yanada kyau idan kana sara ka dinga duba bakin gatarin, mummy tace hakane amma kada kidamu in sha Allahu sagir zai zamewa farhan uba wanda zaiyi alfahari dashi kina gani tun yanzu before auren naku idan kukayi aure ayyi kuma shikenan, kiyi hakuri kinji? ikram tace bakomai mummy

*********wai so nawa zan gayamaka kalmar banason ka ne nasir? wai kai wane irin chewing gum ne kai maye, kai ko zuciyar nan irin ta maza bakada ita, ni wallahi banasan nacin tsiya, taya zan fito gidan talauci, na tashi cikin talauci sannan na kare cikin talauci ko alama wannan ba burina bane, kaman daga sama taji ance tau wallahi karya kike ni kam muhammadu ba talaka bane saboda baki taba rasaci ko sha acikin gidan nan ba, a razane ta juyo tace ko alama baba kaima kasan ba haka bane a tsorace tayi maganar lokacin da nasir kuwa tuni ya sunkuyar da kansa kasa, malam muhammadu yace toh uwata karya nake ya abun yake ne tunda naga ke kike auren hanne bani nake aurenta ba, cikin rashin jindadi tace kaima baba kasan da muna samun komai yanda ya kamata da abubuwan da suke faruwa agidan nan da basu faru ba, amma baba fisabilillahi idan akayi magana kace komai kana mana rabon da ka bamu kudin abinci tun yaushe, kudin makaranta adaina zancen su saboda babu ruwanka, sannan taya kake tunanin zanyi farin ciki da auren dan yayanka nasir mena sama yaci balantana ya bawa na kasa

AURE NAKESO 💔💔💔💔💔Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ