👎👎👎👎Page 37-38👍👍
Written by
M. HANNA 💕💕💕💕💕💕Story by
💙💙💙💙💙M. HANNAEdited by
M. HANNA 💚💚💚💚💚💚Bayan dawowar hanan gida, da kyar ta samu bacci ya dauke, sanadiyar yanda ta dinga jin abunda hajia maryam(mummy) ke mata ko alama bata kyauta mata, haka dai ta kwana tana tunanin anya ko mahaifiyarta ce?
******kai bazaka gane ba friend wallahi wani lokacin matan saida haka, Karfah kamanta hausa kance "Idan kaga bera ya sake toh ka tabbatar kenwa bata nan"dan haka tunda su mazan aure suke nema kuma suna tunanin sun samu ka barni naci duniya ta kawai wallahi, wani matashi ne zaune a gefen khalifa kansa sun kuye a kasa sai lokacin ya dago yana murmushi wanda ya kara fitowa sa kyawun fuskarsa bakowa idanuwana suka ganeman ba face sergent sagir, cike da mamaki nace mezan gani?
********sai lokacin serg sagir yace khalifa kenan, wallahi duk ranar da ka shigo hannunmu zamu gasa maka aya a hannu Allah, badai ina baka shawara baka dauka ba, zaka gane cewa"kwai a baka yafi kaza a akurki"khalifa yayi murmushi yace nadaiji uban hausawa, yanzu dai mu bar zancen ya aikin naka? meya kawo ka sokoto?
*******sagir yace wallahi yanayin aikin mu ne saida transfer, kasan aikin uniform yanda yake, kaidai kaki karatun koh? Khalifa yace uhmmm yanzu ni wazan yiwa karatu bayan inada over 20mil a account dina ba tare da nasha wahalar komai ba, sauki ya sameni har gida,sagir yace Allah ba wani sauki yaudara dai kuma Allah zaka gane kuranka, khalifa yayi kwa da dariya kana yace kada kadamu abokina, any interesting case ? kasan lokacin kana kd kana bani labarin cases sosai
**********sagir yace guy bari kasan baza'a rasa ba, wallahi akwai wani case dake going yanzu abun ya tabani sosai, ba'a taba case dinda naji ya shiga raina ba kaman wannan, khalifa yace ko meyasa? sagir yace labarin case din is a lesson serve to everyone both mata da maza, sannan babban abun tashin hankalin daya ne, yanzu haka yarinyar tana hannun mu, sannan ance her elder sister can help her out amma could you believe yayarta taki yin komai akai, cikin rashin fahimta khalifa yace malam ka fito ka bani labari in details mana komai bangane ba
********sagir yace ayyi nasan bazaka gane komai ba, wata ce ake case dinsu two friends ne kagane? khalifa yace ina jinka ya fadi haka tare da daga masa kai, sagir yaci gaba da cewa toh bazan kirasu da prostitute ba saboda kaddara tana kan kowa, so sun biyewa son duniya da son zuciya suka fara bin sugar daddy's, toh wannan karon kam kasuwar su batazo a sa'a ba, bayan sun gama abunda suke, he was found dead, khalifa ya zaro na mazurunsa tare da cewa kashe sa sukayi? sagir yayi murmushi yace we are still investigating akan case din, amma no proof nacewa sune ko basu bane, khalifa yace chab amma gaskiya suna cikin tashin hankali na tausaya masu sosai wallahi, sagir yace inama kasani, wallahi matasa yan mata masu mutuwar kyau wallahi, kaman su suka zana kansu, khalifa ya washe 32 dinsa yace kace irin namu ne? sagir yace dan iska dama nasan cen hankalinka zaije, amma kasan me yake bani mamaki?
******khalifah yace no sai ka fada, sagir yace daya daga cikin victim din sister dinta is rich, famous, beautiful nd gorgeous amma bansan meyasa taki saka hannunta a case din ba, tun farkon abun ba though naje her explanation kaman ba laifinta bane, amma nidai koma menene Allah zanso yarinyar ta fito khalifa Allah yarinyar taman, ta kwantaman sosai,khalifa yayi murmushi yace naga alamu, yau ne karo na farko da naji kana yaba kyawun mata, in sha Allahu zasu fito indai basu suka kasheshi ba, sagir yace i don't think sune, saboda babu alamun jini ko rauni ajikinsa, may b dai lokaci ne kawai, khalifa yace only god knows
***********sagir yace hakane wallahi,wai ina girl din nan taka, young lady din nan? khalifa yace uhmm tana nan wallahi, ni ko zancen ta banaso Allah, sagir yace uhmm yanzu kana nufin kabarta koh? khalifa yace kaga dan Allah mubar zancen kawai, ni yanzu ba type dina bace, sagir yace kai amma idan ka mata haka baka mata adalci ba, upon all dix love data nuna maka, khalifa yace toh nadaiji, menene ya rage toh? nayi sex da ita times without number, nasanta cikinta da wajenta so menene abun so acikin wannan? kawai yanzu ina jiran wasu kudi ne gun samira dana samu zan masu basaja kawai nabar gari, naje wani country na nemi business mai kyau, nayi aure shikenan, sagir yace Allah kana cikin hadari dan wallahi duk sanda ka shigo hannun mu bazamu raga maka ba, musamman nida nasanka sosai
*******khalifa yace uhmmm ayyi nasan bazaka bari na wahala ba ko na wulakanta, so zanso ma ace ku ne kuka kamani din bakowa ba, sagir yace uhmmm Allah dai ya kyauta, nidai fatana kawai babe din nan ta samu ta fito saboda akwai case babba wallahi, saboda idan ta fito bansan yanda zata fuskanci iyayenta da second case din ba, khalifa yace wani case kuma ta shiga kai wannan yar hannu ce kawai, ka nemi wata akwai alaji, sagir yace you will not understand amma banyi confirming ba hasashena ne kawai kasan abunka da wanda ya karanci health, khalifa yace hakane, Allah dai ya kyauta,
*********da sassafe misalin karfe 6:30am hanan ta farka daga bacci, tana bude idanuwanta sai kan agogon bangon da yake dakinta, cikin muryar bacci tayi addu'ar bacci tare da saukowa daga kan gadon, direct bandaki ta nufa inda ta dauro arwala ta gabatar da sallah subhi, tayi karatun alqur'ani da azkar dinta na safe kaman kullun sai misalin karfe bakwai ta karasa abunda take, ta mike tare da cire hijab din ta nade tare da sallayan ta koma tayi kwanciyarta, ba tare da bata lokaci ba bacci mai nauyi ya kara daukanta
********sannu ikram kinji, sannu, ahankali yake shafa gadon bayanta, ikram ce a tsugunne wajen station din sai kwarara amai take, serg sagir ne bayanta sunkuye da ruwan pure water hannunsa yana shafa gadon bayanta, cikin kulawa ya bata ruwan ta wanke fuskanta da bakinta, idanuwanta sun rine sunyi jawur, haka ta mike tsaye dakyar suka koma ciki,ya nema mata guri ta zauna, sauran ma'aikan sai sannu suke mata ikram kuwa sai yawwa take ce masu dakyar
*******direct office din babban su sagir yaje inda ya bankare tare da masa gaisuwa irin ta manyan yan sanda, bayan sun gaisa yace ka zauna mana sagir, sagir ya zauna cikin natsuwa yace dama sir wata alfarma nake nema gunka dan Allah, babban dan sanda dake zaune yana kallan sagir yace anything for you, yace dama wannan yarinyar ce ba lafiya, sai vomiting take kwana biyu, shine nakesan a bani dama nakaita hospital, babban yayi murmushi yace uhmm kasan mai laifi ce amma babu damuwa na yarda dakai sosai, dan haka you are good to go, nan ya masa godiya ya fice
********bayan fitowar sagir nan ya dauki car key dinsa cikin kulawa yace muje koh ikram? dakyar ta iya mikewa tsaye ya riko hannunta suka nufi gun wata dankareriyar mota kirar jeep baka, nan ya bude mata ta shiga kana ya zagaya abunsa, bai taka birki ko ina ba sai babban hospital dinda yake nan sokoto UDUTH suna isa, ya kira wani dr abokinsa yana fitowa suka gaisa kana suka karasa office dinsa har lokacin yana rike da hannunta, sagir yace dr Othman kenan, kwana biyu? dr Othman yace lafiya lau, ka boye? Kabar aikin dr ka koma kaki, sagir yace toh abunda nake sha'awa kenan tun farko, amma ayyi ko yanzu na so dawowa dr dina zan dawo
******dr Othman yace gaskiya ya kamata saboda u re among d best dr's anan wallahi, sagir yace zan duba nagani, dr othman yace wannan fah kanwar mu ce ko our wife to b? sagir ya maida dubansa kan ikram wacce kanta yake sunkuye akasa yace duk wanda kaga ya dace, sunanta ya kira cikin natsuwa ikram, ahankali ta dago suka hada idanuwa yace kada kidamu, Kiyiwa dr bayanin duk yanda kikeji, tace okay, nan ta masa bayanin komai da takeji, wanda hakan yasa sagir yin cirko cirko da idanuwansa da suke kanta har lokacin, nan take dr othman ya kira nurse ta dauki blood sample dinta, dana fitsarinta, nan shima karan kansa ya dubata
******bayan an karasa komai dr othman yace zan bata wasu drugs make sure tasha su before result nata ya fito mu tabbatar idan abunda muke tunani ne, sagir yace okay then babu matsala, nan ya rubuta drugs din sukayi sai anjima, akan hanyarsu sagir ya tsaya pharmacy ya siye maganin ya dawo, bai taka birki ko ina ba sai wani dan madaidaicin gida wanda ya keru sosai, haka aka bude masa gate din ya karasa nan suka fito, ikram biye kawai take dashi kaman rakumi da akala, haka suka shiga falon gidan mai kyau, komai gold ne a falon, haka ta zauna ya hado mata tea tasha dakyar, ya bata magani ta kwanta akan kujeran falon nan take bacci yayi gaba da ita
**********sagir dake zaune akan dayan one sitter din falon dake kallon ta shuru yayi yana kallanta ko kyabtawa babu, murya cen kasa yace ikram is pregnant, for who? innalillahi wa'inna illaihir raju'un dama tunanin da nayi kenan tun farko, yanzu ta ina zan fara, gashi dr Othman is my best friend idan nace zan aureta ta ina zan fara kareta? ya subhanallah, i have to do something about dix before d world get to know, nan take ya mike tsaye ya shiga yin safa da marwa, sai kai da kawowa yakeyi, ba tare da daukan wani dogon lokaci ba ya tsaya chak a tsakiyar falon yace i know what to do
*********toh fah wata sabuwa?
Hausawa kance"sai yadda ta yu nakuda a dakin mayya "🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
Cast
Khalifa
Ikram
Zaynab
Zahra
Hanan
Ameer
Aminu
Sagir
Dr othman
Mum
Dad nd other's all in AURE NAKESO book one🙌🙌🙌🙌🙌🙌🙌🙌🙌🙌🙌More vote
More likes
More post🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
YOU ARE READING
AURE NAKESO 💔💔💔💔💔
Short StoryMatasa ne mata uku, masu kudi, masu kyau, komai sukeso na duniya Allah ya basu but they are looking for true love, let's see how it gonna roles💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞shin zasu samu koya?