AURE NAKESO 💞💞💞💞💞💞

702 46 3
                                    

🅿🅿🅿🅿111-112🅿🅿🅿🅿🅿

Cast
Khalid
Khalifa
Samira
Sagir
Ameer
Aminu
Ikram
Zaynab
Nawwara
Aisha
Noor
Nuriyya
NABIHA
Nawal
Farhan
Mr nd mrs Ahmad zaki
Mr nd mrs ABDULLAHI SALIM
Malam muhammadu
Malam usman
Ummah hanne
Mai sunan mama
Iyya
Raliya
Gateman 1
Gateman2
Gateman3
Nd other's all in🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏

Story by
M. HANNA 💍💍💍💍💍💍💍💍

📿📿📿📿written by
M. HANNA

Edited by
M. HANNA 💞💞💞💞💞💞💞💞💞

Hajia asiya ce zaune misalin karfe bakwai bayan ta gabatar da sallah magrib zaune take akan sallaya tana jan charbi, ummah na gefenta itama sallar take, aisha kuwa har lokacin bata farka ba, nan suka karasa kana suka mike tsaye suka zauna akan kujera, mummy tace wai lafiya har yanzu khalifa bai dawo ba? ummah tayi murmushi tace gamu mai zai dawo yayi?  mummy tace mezai dawo yayi fah kikace? ayyi ba mune ya dace ace munanan ba shi mana, ummah tace uhmmm haka dai kike gani hajia, mummy tace gaskiya yakamata ki aje kunyar khalifa haba dan Allah ace mutun bai taba ganin surukinsa ba, ummah tace toh ayyi kinsan abun sabo ne kada ace nayi rashin kunya da yawa, kinsan Aisha itace ta farin, mummy tace tunda kike iya kiran sunanta toh ya kamata ace kunyar khalifa ki janyeta gaskiya, ummah dai bata kara cewa komai ba sai smiling take tana jan charbin hannunta

**********khalid ne da mai sunan mama(khadija)  zaune akan booth din motar khalid, khalid ya maida dubansa kan ta yace yaushe zaku zana jarabawar? ta turo dan karamin bakinta kana tace uhmmm sai zuwa next month in sha Allahu, yace naji kina zancen biyan kudin exams din, nawa ne duka? tace 20k ne yace okay toh yayi zan baki 30k har kudin break da wasu books koh? mai sunan mama tayi murmushi tana masa godiya, kiranta akayi awaya da'gawa tayi bakinta dauke da sallama tace gani nan a parking space aunty karaso kawai nan ta kashe wayan, khalid kuwa baice da ita komai ba yacigaba da latse latsen sa awaya

******nawwara ce na hango tafe, tafiya take cikin natsuwa da kwanciyar hankali tamkar batasan taka kasa, kanta sunkuye akasa, harta karaso gunsu, bakinta dauke da sallama, daidai lokacin khalid ya dago yana amsa sallamar tamkar mai koyon magana, ba karamin tafiya da hankalin shi  nawwara takeyi ba, tayi murmushi, suka gaisa, kana tace ya mai jikin auta? Mai sunan mama tace toh jiki da sauki tunda har tana numfashi kawai dai bata farka ba, nawwara tace naji ana maganar poison taci koh? mai sunan mama tace wallahi aunty, tare suka karasa khalid kuwa zaune yake yana kallanta ko kyabtawa babu

*********dakin suka karasa, nan suka gaisa dasu ummah da mummy dake zaune a dakin, gefenta nawwara ta karasa sosai tausayin aisha ya kamata batasan lokacin da ta shiga zubar hawaye ba, murya na rawa tace wato saida ta tabbatar tacika burinta akanki, ta Allah ba tata ba, yanda Allah bai rubuto maki mutuwa ba a yanzu in sha Allahu zaki rayu har kiga jikokin ki, wallahi Allah bazai barki ba zaynab, Allah ya hanaki farin ciki da kwanciyar hankali na rayuwa, Allah ya maki yanda kika mata, kalaman sosai suke shiga jikinsu, ummah ce ta mike tsaye ta dafa kafadarta wacce ta juyo ba shiri tana goge hawayenta, cikin fuska mai dauke da alamun tambaya ummah tace ya akayi kike magana haka nawwara? ayyi babu abunda Allah bayayi akan bawansa, kidaina kinji? nawwara ta rungume ummah tace hakane ummah amma wallahi komai yanada dalili na rantse da Allah zaynab tanada hannu acikin wannan abun, mummy ta mike tsaye ta tunkarosu, ta dubi nawwara tsab kana tace wacece kuma zaynab? badai karuwar khalifa ba? ya akayi kikasanta? ummah ta dago kai cikin rashin fahimtar kalaman mummy tace haba dai hajia, babu kyawo kana kiran dan wani da kalamai wadanda basu dace ba, ayyi zaynab ba karuwa bace itama mata ce gun khalifa kaman aisha,

********nawwara tace kwarai kuwa mummy, she's not a prostitute, mummy tayi dan guntun murmushi na takaici tace toh waya daura masa auren? wayaje nema masa auren? wanene yaje auren? kai ta girgiza tare da bawa kanta amsa kaman haka, babu saboda ni bansan khalifa yanada wata matar ba bayan aisha, ban taba zuwa auren khalifa ba, wannan shine aurensa na farko ta fadi hakan tana nunin aisha dake kwance,

AURE NAKESO 💔💔💔💔💔Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz