💥💥💥💥page 83-84💥💥💥💥💥
Cast
Hanan
Ikram
Sagir
Samira
Zarah
Zaynab
Dr othman
Nd other'sEdited
M. HANNA 💥💥💥💥💥💥💥💥🔯🔯🔯🔯🔯🔯🔯Story
M. HANNAWritten
M. HANNA 💜💜💜💜💜💜💜Abu kaman da wasa,amma sai gashi ya fara zama gaske, haba dan Allah mezai hana ki kaini in fara gaida ummah kana daga baya azo tambaya, wannan wacce irin soyayya ce wacce ko gidan ku ban taba sani ba aisha, ni gaskiya na fara tunanin wani abu, aisha tace uhmmm kada kadamu khalifa wannan duk ba abun tashin hankali bane, so nawa akayi kuma ni kawai nafisan sai anfara komai sannan kazo ku gaisa dasu ummah, khalifa dake tsaye jikin motarsa aisha tana gefensa ya nade hannayensa biyu tare da yiwa aisha kallan mamaki kana yace meyasa kikafi son hakan? aisha tace saboda shine tsarina, yayi murmushi yace tsarinki kuma shine nawa dan haka banida matsala a kan hakan, aisha ta kwantar da kanta akan kafadarsa tace shiyasa nake son ka hayateeee
**********ummah hanne ce zaune akan katifar aisha, kinga wannan na wanka ne, idan zakiyi wanka kije gunsa sai ki saka ya tsunki biyu banda manuni ki dibi garin ki zuba da ruwan har sau uku, wannan kuma kwalli ne kinsan yanda ake shafa shi ba sai nagayamaki ba, aisha ta karba tana murmushi, tace kada kidamu ummah duka nagane, ayyi wannan kwallin kaman yanda ake shafawa sauran zan shafasa bayada illah, ummah tace toh shikenan Allah dai yasa mu dace, fatana duk abunda kikace masa shine shine banasan ya maki gardama, aisha tace indai inada ke ummah ayyi duk duniya bana tsoron zama da kowa
*******da sassafe sukayi waya da khalifa ya gayamata cewa da marece zaizo dan haka ta shirya zasuje tayi register koyon mota, cikin muryar shagwaba tace ni Allah nafisan ka koyaman, gashi wasa wasa ka fara koyaman kuma na fara ganewa shine yanzu kuma zakaje ka kaini school ni wallahi ba inda zanje Allah, khalifa yace uhmmm kai aishana banasan tashin hankali ya isa, sai nazo toh, zamu fita na fasa kai ki driving school din shikenan? tayi murmushi tamkar yana kusa tace eh shikenan
*******kwance yake yana waya da aisha, amma kiran zaynab ne yaketa shigowa a wayansa amma idan ya duba yaga itace sai yacigaba da wayansa, saida suka dauki 1hour suna wayan kana yace toh kije sai na kiraki anjima, aisha tace toh bakomai, bayan ya gama wayan da aisha, ya kira zaynab back, tana dagawa tace haba dan Allah khalifa wannan wane irin tashin hankali ne haka, kana ganin kirana amma bazaka daga ba, khalifa yace kaman ya bazan daga ba hala mekike dashi da zaki bani? kinga malama kada ki bataman rai yanzu da sassafen nan wallahi, ya akayi ne?
Zaynab tace kayi hakuri toh, dama kira nayi na baka hakurin abunda ya faru in kuma kara neman alfarmar ka karaman koda 1week ne before na dawo, khalifa yace da kike maganan alfarmar na kara maki kwanaki hala da zakije kingayaman zakije ne? shuru tayi, yace banasan makirci da munafurci wallahi, kiyi duk yanda ranki yakeso, babu ruwana, idan kinga dama ki dawo, idan kuma bakiga dama ba ki tabbata acen, bai jira feedback dinta ba ya kashe wayansa ya gyara kwanciyarsa
*************ZAMFARA*******
Kwance zaynab take akan gadonta, tayi rufa da wani red silky bedsheet dinta, murmushi tayi tana kara kallan sensor din wayan nadan lokaci, kana ta gyara kwanciyar ta tayi shuru tana tunanin irin yanda khalifa yake nuna halin ko in kula akanta, gata da ciki kuma, murya cen kasa tace gashi tunda nazo garin nan bansamu ganin ALHAJI ABDULLAHI SALIM ba, ko ya suke da khalifa shine babban abunda nakesan sani, saboda idan nasan koshi wanene tabbas nagama sanin ko wanene khalifa, amma ya zanyi? ya zama dole naje gidansa ko da zan taki sa'ar ganin mai dakinsa, itama nasan bazata rasa sanin wanene khalifa ba, da wannan nazarin bacci barawo ya sace ta*********misalin karfe 12 na yamma ta tashi daga baccin nata, kitchen ta fara shiga ta dora indomie da kwai taci kana ta nufi bandaki tayi wanka, ta saka arabian dress purple mai ratsen black, tayi dora mayafinta akai 3 in 1 black yayi mata kyau sosai, ba wata kwalliya tayi ba yar powder ce ta shafa da lipgloss, ta dauki fashion handbag dinta karamar black mai flower's, ta dauki car key dinta ta fito, tana fitowa ta shiga kiran ALHAJI ABDULLAHI SALIM amma baya dauka, kira take akan Kira
ŞİMDİ OKUDUĞUN
AURE NAKESO 💔💔💔💔💔
Kısa HikayeMatasa ne mata uku, masu kudi, masu kyau, komai sukeso na duniya Allah ya basu but they are looking for true love, let's see how it gonna roles💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞shin zasu samu koya?