AURE NAKESO book 📚 one

953 45 4
                                    

💫💫Page 35-36💫💫💫💫💫

Story by
💛💛💛💛💛M. HANNA

    Written by
M. HANNA 💝💝💝💝💝

Edited by
💜💜💜💜💜M. HANNA

Khalifa kuwa lokacin da duk ikram ta kirasa yana tare da zaynab, tafiya suke ga dukkan alamu strolling suke, ganin yanayin fuskarsa ya sauya, zaynab tace lafiya kuwa baby? yace lafiya lau kawai business partner dina ne kinsan basa gajiya da batawa mutun rai da lokaci, zaynab ta dan murmusa tare da kara saka hannunta acikin nasa tace uhmmm u nd this ur business, Allah dai ya taimaka, ya amsa da ameen, aransa kuwa tuni ya fara tunanin me ikram takeyi a station? haka dai yinin ranar suka kasance amma duk tunaninsa yana kan kiran da ikram ta masa

*******haka rayuwar ikram ta kasance a station koda yaushe cikin kuka take, tayi baki ta rame duka ta fita hayyancinta, zaune take ta cusa kanta acikin cinyoyinta taji sergeant ya kira sunanta cikin kulawa, wani sergeant kyakkyawa mai kyau dashi, cikin uniform dinsa yake a tsaye murya cen kasa yace ikram, zo mana, ahankali ya dago kanta kana ta mike da kyar ta karaso tayi tsaye, yace kina nufin bakida kowa wanda zai shige maki gaba a wannan case din ba  mamaki wallahi zasu turaku kotu,and you are too beautiful da hakan wallahi

*******cikin tausayawa yake maganar, ikram tace uhmm ya zanyi? bayan wacce nake da tabbacin zata iya fitar dani ta cire hannunta, ni yanzu banida kowa bayan Allah, saboda mahaifana can't do it all alone ta fadi hakan tare da share guntayen hawayenta,yayi murmushi yace ita wannan da kike tunanin zata iya cireki daga nan ya kuke da ita ne? ikram tace uhmmm she's my elder sister, yace what? dsme mum? Ikram tace uhmm kada kaga laifin ta, it is not my fault nd her's too but our mum's fault, cikin rashin fahimta yace kamanya kenan, explain mana may b i could help, anyway AM SERGENT SAGIR SALIM, ranar da aka kawo case dinku ranar akaman transfer to sokoto, so da naji case din abunda ya faru nayi mamaki  sosai

******ke kuwa ya akayi kika fada wannan harkar? ikram tace uhmmm sagir bansan mezan gayamaka ba yanzu kam, saboda duk wannan aikin son rai ne, aikin da gamgam, aikin yarinta da kuma jahilci, nan ta kwashe komai tun daga farko har izuwa yanda da suke magana ta gayamasa, sagir ya saukar da wani nauyayyan numfashinsa yace uhmmm tabbas ikram wannan aikin son zuciya ne da kuma son rai, amma kuma ayyi wannan ba laifin hanan bane, meyasa mamanki take dora mata laifi?

******saboda ga abunda take maki gudu kenan kin fada farkon duniya, yanzu kuma ita kadai ce take da kudi da power din taimakon ki, gashi kuma ta cire hannunta sai ya kenan? Ikram tace uhmm sai zama agidan yari saboda bantaba ganin bacin ranta ba irin wannan karon, sagir yace gaskiya kinyi kuskure sosai, amma kuma in sha Allahu i will hel dan haka ki bani number ita yayar taki, nan take hanan ta basa number hanan din ya rubuta awayansa, kana yace mekikeson kici yanzu? ikram tace banajin yunwa, banasan komai sagir nagode da kulawarka,

******yace uhmmm ko alama baza'ayi  haka ba ikram bari naje na samo maki abunda zakici, bai jira feedback nata ba yasa kai ya fice abunsa, yana tausayawa ikram sosai saboda yaga nadama sosai a idanuwanta, haka ya kawo mata abinci mai kyau taci tasha, ya kuma tayata fira, sanadiyar yau bakowa shine akan duty, amma sauran sergeant  din ko alama basa tausayamata, dan ko kallo bata ishesu ba,

******yau ta kama sunday weekend kowa yana gida, hanan tana kwance sai kallanta take hankalinta kwance, knocking taji anayi wanda hakan yasa ta tashi zaune kana tace kai malam, na shiga uku nifah daddy wallahi there's nothing da zanyi akan case din nan tunda dai  mummy  ta nuna man ni banza ce toh ni kuwa bazanyi amfani da power dina ba, knocking dinda aka sakeyi ne ya katseta daga iyarda zancen nata, ta mike ta nufi door din ga mamakinta bayan ta bude sai taga sagir, cikin rashin fahimta tace kai kuma wanene? sagir yayi murmushi yayi introducing kansa kaman yanda yayiwa ikram, cikin girmamawa yace zan iya shigowa?

AURE NAKESO 💔💔💔💔💔Donde viven las historias. Descúbrelo ahora