*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHEJAY* @wattpad
Page 4
Gaba dayansu ne suka fito zasu skl gashi there getting due to mae aikin su bata gama breakfast da wuri ba gashi ya Ashir ne zae kae su kuma baya son jira dan shima skl zashi yana da morning lecture driver kuma mama ta aike sa kalgo tunda safe.
Falmata da Farouk da Afeefah sune kusan sa'anni sae dae falmata ta bama Afeefah sati biyu. Kullum aka fito za'a je skl sae falmata da Farouk sunyi fadan zama gaba dama ita Afeefah ba mae hayaniya bace dariya kawae takeyi ta koma baya ta zauna abunta.
Sae da Ashir ya tsawatar kana Falmata ta koma baya tana kunkuni shi Kuma Farouk sae dariya yake mata kullum haka suke yi idan driver ne zae kae su kuma sae dae gaba daya su zauna gaba shima sae anyi rikicin zama bakin kofa.
Gaba daya yaran gdan tunda suka tashi brilliance suka ga yan uwansu nayi suma anan aka jona su.Bayan sun dawo gaba daya suka ci abinci suka fara shirin zuwa Islamiya Hajja ce ta shigo dakin kallon su tayi gaba daya sun gama shiri kallonta ta mae da kan Afeefah tace "ki sameni a daki"
Cikin sanyinta ta amsa da "toh Hajja" bayan Hajja ta bi har dakin ta sae da ta zauna bakin gado kana tace "ki shiga toilet dina ki wanke minshi dan yayi dauda"
Duk da ranta bae mata dadi ba dan bata so ta rasa tahfiz din yau gashi tana ganin tayi harda mae kyau maybe a zabeta cikin masu musabaqa amma ba yanda ta iya kullum Hajja treating dinta take kamar yar aiki bayan kuma tana da gata dan kawae an ganta marainiya ne shiyasa. kullum abunda ke cinta kenan maraici tana ganin yanda Hajja ke kula da 'ya 'yanta amma ita ko Oho gashi mama itama ba kula take da ita ba acewar ta tunda tana gurin Hajja zata mata komae dan ba wani shiri suke ba.
Haka ta koma daki ta hau cire uniform dinta kallon ta falmata tayi tace "baza kije Islamiya bane naga kina kwabe Kayan"
"Ehh bazan je ba" shine kawae amsar da ta bama Falmata dan a irin yanayin da take Jin kanta kuka kawae take so tayi idan ta tsawae ta magana tofa kukan zatayi, Falmata kuwa ta riga da tasan ba wanda zae hana Afeefah zuwa Islamiya sae Hajja gaba daya ranta bae mata dadi ba dan tana sama yar uwarta tan zuwa musabaqa dan duk tafisu hardar kwarae. Hafsa dake zaune tana wasa da Kayan wasan ta da alokacin itace karama shekaran ta uku da watanni.
Farouk ne ya shigo da gudun sa yace "adda Maryam ce fa zata kae mu Islamiya kuma kun san halinta da zafin rae ke Afeefah naga ma baki shirya ba"
"Ehh bazan je ba"
"To meyasa" Farouk ya tambaya
"Kawae" daga haka ta fice dan bata son sake magana hawayenta gab suke da zubowa
Kallon Falmata Farouk yayi yace "meke damun Afeefah ne"
"Tace bata Jin dadi ne muje ko" fita sukayi harabar gidan kowa ya fito su kadae ake jira kallon su Maryam tayi tace "ina Afeefah ne"
Farouk yace "ba zata je ba"
"Dalili" Maryam ta tambaya
"Adda bata Jin dadi ne"
Hmm kawae tace dan tasan Hajja ta rike ta kuma ita yanzu ba zata iya zuwa gurin Hajja ba dan sauri yake tana da bikin course mate dinta.Afeefah kuma bayan ta gama wankin toilet ne ta koma daki ta kwanta abunta gaba daya kadae ci take ji gashi yar kanwarta na hannun mommy (maman fu'ad) wani irin marayen kuka ne ya kwace mata sae da tayi mae isarta kana tayi shiru a haka har bacci ya dauketa bata farka ba sae da taji hayaniyar yaran gdan sun dawo daga Islamiya.
YOU ARE READING
Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ
Lãng mạnBana gaya miki bana son haihuwa ba wlh saena zubar da wannan cikin naki dan a tsari na haihuwa ki shirya karbar magani" "Wlh baka isa ka sakani zubar da kyautar da Allah ya bani ba Sulaiman kayi duk abunda zakayi" "Kayi hakuri Sulaiman bazan iya kom...