*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHEJAY* @wattpad
Not Edited 🥺💔
Page 20
#Regret
Marrying Sulaiman is the greatest mistake I've ever made in my life, am just regretting but idan na tuna haka Allah ya gira ga da ya tsara min sai kawai nayi addu'a amma Ina cikin wani hali Ina cikin tsaka mai wuya tun daga ranar da muka je hospital ban Kara ganin Sulaiman ba ya dai na zuwa part dina ya dai na cin abinci na komai nawa ya dai na kulawa hakan ba karamin ciwo yake mun ba, gashi matar sa ta saka ni gaba gorin yau daban na gobe daban idan iskacin nata ya mota a ba ita kadai zata zo ba harda frnd dinta "ai tunda Allah ya yanke maki kazar wahala dole ne ki figeta tassss ma wlh" Atika ta fada tana kara gyara daurin dankwalinta kawarta ma sai da ta tofa albarkacin bakin ta "hmmm ni Wlh Atika da ace ban San yar gidan masu kudi bace da nace abunda yasa tayi cikin nan dan ta samu gadon abunda sulaiman zai mutu ya bari ne"
Dariya suka sheke da ita ni dai ko kallon su banyi ba na cigaba da abunda nake a waya na a toh meyasa zan damu kaina Bayan ko wanda ya kawo ni gidan ya juya min baya ya nuna ni ba kowa bace to Dan su Atika sun min dan wannan abun sai ya dameni, wani irin zafi naji zuciyata namin kamar wuta hakan hasa na mike na shige kitchen suma a haka suka gama habaicin su suka tafi, ruwa masu dan sanyi nasha Ina maida numfashi dan ji nake kamar wuta ce ke balbal a cikin zuciyata kiran sunan Allah na koma yi har na samu na fara jin dai dai sai na fito daga kitchen din na wuce daki.
*Few weeks ago*
Kwance nake a parlour gaba daya ba abunda nake sha'awar ci sai dan wake da yaji kuma bana so naga anayin sa a gaba ni ci kawai nake son yi ajiye remote din da ke hannuna nayi Ina laluben wayana dake bayana, Aunty na jira bugu biyu ta dauka Bayan mun gaisa na fada mata abunda nake so tace "shikadai kike so ko akwai wani abu" nace "aa aunty shi kadai" tace "toh yayi bari yanzu zanyi sai na bama su Husna su kawo maki kinji" nace "toh Aunty nagode" da haka mukayi sallama na mike na shiga dan an fara kiran sallahr azahar sai da na dan watsa ruwa kasacewar dan zafin da akeyi yau duk da akwai hadari amma bai gama haduwa ba Bayan na fito na gabatar da sallah.
Kamar yanda Aunty ta fada su Husna ne suka kawo mun dan waken naji dadin ganin su sosae har na naso su zauna sai dai shirin Islamiya da naga sunyi ne yasa na bar su, "Adda baki ga sabon uniform dinmu ba" ni sai yanzu da Dawood ma yayi magana na kula "sabo aka chanza ne naga ai da army green ne" dariya yayi yace "aa Islamiya aka chanza mana ne" jinjina kai nayi nace "eyye kaga yaran abba yanzu wane Islamiya aka maida ku" Afrah tace "B.I.C.E kuma fa yau har ranar friday ana zuwa" ka karasa fada kamar tayi kuka ni dariya ma ta bani amma saina gimtse kayana dan nasan halin ta yanzu sai ta fara kuka sauran yaran kuma sun samu abunso haka zasu ta tsokanar ta zaro ido nayi nace "Friday kuma toh sa karfe nawa?" "After jumu'at prayer amma 4 muke komawa gida" nace "masha Allah amma dai ana karatu ko" Bello yace "sosae na Wlh ba kamar waccen Islamiyan malam fatihu ba sai uban duka ni Wlh naji dadi ma" dariya nayi nace "lallai kuce guduwa kuka yi kenan saboda duka" Hasana tace "kaji Adda ba dole ba ni kam kuzo mu tafi Allah fah munyi late" hakan yasa suka tashi gaba dayan su sweet da biscuits din da aka kawo mun na engagement din frnd dina da basu da 1k suka tafi suna godiya, har bakin mota na kara su muka gaisa da Ali driver kana na koma cikin gida.
Kitchen na wuce direct na dakko wani bowl dan ni bana son cin abinci a plate dama basket din dan waken na jawo na bude daga kallo ma zaka ji ya shiga ranka dan ya hadu sosae gashi yaji su Kwai da salad ji nayi baba son ci da salad din hakan yasa ya ajiye bowl dinda aka zubo shi na zuba dan wakena da yayi laushi da Mai sai yaji Mai dadi gashi yaji tafarnuwa sosae na baje Ina cin dan waken dan yamin dadi sosae.
YOU ARE READING
Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ
RomanceBana gaya miki bana son haihuwa ba wlh saena zubar da wannan cikin naki dan a tsari na haihuwa ki shirya karbar magani" "Wlh baka isa ka sakani zubar da kyautar da Allah ya bani ba Sulaiman kayi duk abunda zakayi" "Kayi hakuri Sulaiman bazan iya kom...