Our Love Story

280 62 1
                                    

*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_

Written by *NEESHAR.JAY*

*NEESHEJAY* @wattpad

Page 6

#Our Love Story

Bayan na dauko hijab dina na fito banyi tunanin zasu ganni ba dan kamar munafuka haka na dinga tafiya sadaf sadaf sae ji kawae nayi ya Uthman yace "Afeefah kawo mana ruwa plss"

Ras naji gaba na ya fadi kuma bazan iya ce maku ga dalilin faduwar gaban nawa ba haka kawae na tsinci kaena da jin wani iri. Kitchen na shiga na hado masu ruwa da drinks akan wani karamin trey na kawo masu kae na a kasa na gaidashi, maimakon ya amsa sae ji nayi ya jefo min wata tambaya "are you done with the assignment i gave you?"
Girgiza kae na nayi nace "not all"
Yace "ok go and bring it"
Banji dadi ba dan gani nake kamar takuramin yake son yi a skl bae barni ba haka ma ya biyoni har gida "maye kawae" na fada ina shiga cikin dakin mu
Ya Uthman ne ya kallesa yace "ina kasanta kuma"
"She's my student" ya fada smilingly
Uthman yace "oh really"
Yace "yes but do you know what?"

Uthman yace "aa sae ka fada"

"I think am in love with this girl since from the very first day I saw her"

Gyara zama Uthman yayi yace "tell me something, Ina ka fara ganinta"

Smiling yayi yana cire shade dinda ke idon sa yace "a skl ne fah" nan ya bashi lbrn tundaga ranar da suka hadu har zuwa yau sosae Uthman yayi dariya yace "you're my good friend, so I will help you fight the battle" Hanna ya bashi sukayi dariya.
Daram naji gabana ya fadi zuciyata ta shiga dokawa kamar zata tsaga kirjina ta fito, kamar saukar aradu haka naji maganar ta dirar mun lokaci daya dakyar na iya dai daita natsuwa ta kana na shiga da sallama a bakina kallo kawae suka bini dashi hakan yasa na fara feeling guilty mika masa book din nayi yace "where is your sister"
Nace "she's inside"
Yace "ok call her"

Haka na mike naje na Kira Faty muka dawo duba assignment din yayi yaga munyi dai dai sae dae kwara daya da bamuyi ba shima dan bamu gane bane Kuma Farouk yace idan ya dawo sae ya nuna mana dan ba lecturer dinmu daya dasu ba.
Haka dae ya koya mana dayan duk da ba wani ganewa nakeyi ba dan gaba daya hankali na baya gurin, maganar sa da ya Uthman kawae nake tunawa. Bayan mun gama muka koma daki Faty sae tsaki take sbd tana bacci na tadota komawa tayi ta kwanta ni kuma na jawo diary na na rubuta abunda ya faru.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya bazan iya ce maku ga lokacin da na fara dating Sulaiman ba sae dae kawae na tsinci kaena cikin soyayya tsundum koda yake ance zuciya nason mae kyautata mata inaga ta wannan hanyar ne Sulaiman yayi amfani gurin winning heart dina, sosae muke zuba soyayyar mu duk da a skl yi muke kamar ba komae tsakanin mu and baya nuna bambamci between ni da sauran students but idan aka dawo gida hmm abun ba'a magana.
Ina 200level ne Sulaiman ya matsa akan yana so ya turo magabatan sa dan baya so wani ya masa kwace dariya kawae nayi Bayan na dawo gida ban boyewa Adda Maryam ba na gaya mata abunda ke tsakanina da Sulaiman dan sun saka mun ido kullum Faty cikin basu lbrn abunda ya faru take ba yanda basuyi ba amma naki Kulasu ba sae yanzu. Ta bani kwarin gwiwa sosae duk da lokacin itama ana shirye shiryen bikinta ne, Aunty ta samu da maganar Bayan ta gaya mata ta kirani ta tambayeni, ban boye mata komae ba nace mata ehh tace toh zata samu Abban mu da maganar. Bayan Sulaiman ya kirani waya da dare na gaya masa zae iya turowa duk da Aunty bata sanardani yanda sukayi da Abba ba amma am 100% sure Abba bazae ce aa ba kawae zae saka a mashi bincike ne akan Sulaiman.

Bayan sati biyu da kwana uku magabatan Sulaiman suka zo tambayar iyayena sosae kowa yayi farin ciki Bayan an gama abunda ya tara mutane, abun yazo da sauki dan Abba yasan baban Sulaiman tare sukayi Service.

Soyayya tsantsa muke nuna ma junan mu inason Sulaiman son da baki bazae iya fadarsa ba ni kadae nasan yanda nake dawainiya da zuciyata akan son shi amma haka nake dannewa dan bana so na nuna masa yayi using wannan opportunity din ya yaudare ni duk da bana tunanin hakan daga garesa na yarda dashi fiyeda da tunanin mae tunani ban taba kawo ranar da Sulaiman zae cutar dani ba ko a mafarki ballantana a zahiri. Ranar daya gaya mun yana da mata na tsorata sosae dan bana son tashin hankali amma son da nake masa ya danne wanna nan tashin hankalin nawa addu'a kawae na cigaba dayi akan Allah ya zama min abunda yafi alkairi.

Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ  Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ  Where stories live. Discover now