*This page is dedicated to my amazing soul, my sister Slimzy my love for you is endless ❤️🔐 thanks for your kindness and caring🦋*
*Not edited 💔🤧😤*
Page 18
#Tolerance
Bayan kwana biyu Atik ta matsa ma sulaiman akan ita fa ta gaji da girki ita kadai idan zaije ya maida dani yaje dan ita baza ta Kuma yima girki ba ranar girki na "in ban da samun guri da iskanci irin nata daga kawai cikin ta ya zube zata wani koma gida kwanan ta goma fa yau toh wlh bazai taba sabuwa ba idan zata dawo ta dawo idan kuma bazata dawo ba nima sai na kwashi kayana na koma gidan mu tunda gida ba din gida yayi ba ko uban wani yace tayi cikin ne" cikin tsawa da daga murya Sulaiman yace "enough Atika am tired of all this your nonsense don't lemme lose my mind if not you will not find it easy with me" daga haka ya fice fuuu kamar isa ita kuma ta cigaba da surfa masifa ita kadai dole Ranar a gidan mu sulaiman yasha ruwa dan Atika cewa tayi bata girka komai ba sai doya data siya ma kanta ita kadai saboda tsabar kishi ko nace hauka yo hauka mana idan ba hauka ba kina da kishiya zaki bari wani abu ya shiga tsakanin ki da miji.
A gida na karasa azumina Kuma alhmdllh duk da cikina hakan bai hana ni yin azumi ba dan 8 ne kawai banyi ba Allah da rahamar sa ya ni'imanta min na gama. Ana sallah saura sati daya su Waheedah suka dira cikin birnin kebbi naji dadin ganin yar uwata sosae dan ba'a gidan mommy ta zauna ba gida ta dawo dan dama duk sallah a nan takeyi cikin zuri'ar ta, sai dai daren sallah suka je suka kama ma Aunty seeyamah aikin snacks din da zata tayi dan ko a nan kebbi gida daya suke da mommy sai dai kowa da nasa part din dan gidan babbane duk da Bayan mommy batayi ba akan ya samu ya gama gidan saa dake Gwadangwaji quarters yace aa sai idan Farouk zaiyi aure sai su zauna tare tunda gidan da sunan mutum uku akayi ya shi da Farouk sai Ashraf.
A daren sallah aka kira mana mai kale tazo har gida tamin daya yake tunda nayi ciki sai ya zamana bana son taba kaina ba yanda Aunty batayi ba akan naje saloon amma naki sai dai Waheedah ta mun shiku guda ashirin shima dakyar na bari. Washe gari sallah kowa ya tashi cikin tsananin farin ciki da dauki tun asuba suka fara shiga wanka iyaye mata kuwa da masu aiki suka duku fa kitchen din waje dake Bayan part din mama suna aiki, nikam ina daki ko niyar tashi wankan na banyi ba dan bazan iya zuwa masallaci ba duk sona dashi, al'adar gidan mu ce koda kuwa kinyi aure tunda muka tashi haka muka ga ake mana kaya iri daya abba ke mana gaba daya harda mazan gidan kowa iri daya sai iyayen mu mata su uku suma iri daya da da Ammi na ke raye su hudu zaka gani kayan iri daya dinki ma haka, toh muma yan matan gidan haka ne abba ma da mazan iri daya ne wannan aladar ba karamin dadi take min ba, su Adda Maryam da Adda Hadeexa ne masu zaban kaya idan suka zaba sai a kawo wa kowa ya gani.
Wannan sallahr wata red and ash super muka dinka sosae mukayi kyau dan ba wanda kalar bata karbesa ba abunka da fulani😆. Gaba daya duk masu zuwa masjid suka fito harda su hajja da Aunty da suka gama aiki sai abunda ba'a karasa ba suka barma masu aiki amma duk an jera abinci a parlourn Abba saboda bakin sa, dama mana ita ba zuwa take ba dan haka ta shigewar ta part dinta gaba daya gidan duk suka fito kowa ya shiga motar da zai shiga suka har gidan saboda lokaci na tafiya ga abba sai fada yake akan suna bata lokaci. Turaren wuta na kunna a burner na koma na rufe kofar parlour na dawo daki na wuce Ina cire riga bacci na dan nasan idan suka dawo banyi wanka ba zasu dameni da surutu ne hakan yasa na shiga toilet nayi wanka da yake garin da dan sanyi dan yau akawai hadari sai dai iska keta kadawa. Ina fito wa na shafa lotion dina lovely na oriflame na dauko kaya na dama doguwar riga ce na saka na zauna Ina kallon kaina a mirror tunanin sulaiman ne ya fado min waccan sallahr daya dinga damuna akan na bata masa lokaci shifa zai tafi sai dai na tafi ni kadai smiling nayi Ina shafa powder da kwalli sai dan nude lipstick dana shafa na murza daurin dan kwalina na zara buhari sosae nayi kyau abuna duk da kurajen da suka fito min na ciki amma dana shafa powder duk sai suka kwanta luff abunka da Kayan oriflame.
![](https://img.wattpad.com/cover/210623472-288-k184867.jpg)
YOU ARE READING
Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ
RomanceBana gaya miki bana son haihuwa ba wlh saena zubar da wannan cikin naki dan a tsari na haihuwa ki shirya karbar magani" "Wlh baka isa ka sakani zubar da kyautar da Allah ya bani ba Sulaiman kayi duk abunda zakayi" "Kayi hakuri Sulaiman bazan iya kom...