*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHEJAY* @wattpad
Page 24
*This page is dedicated to #TeamMalamSule😂💔 #TeamAfeefah karku damu soyayyata a gareku ta musamman ce❤️🔐*
*I love the way you guys comment on this book I feel awn😍 am so happy Allah ya barni da ku*#FamilyMeeting
Da safe Bayan Afeefah ta farka as usual gyara bedroom dinta ta fara yi kana ta shiga dakin Aunty ta gyara duk da ba wanda ya kwana a ciki Aunty na part din Abba, Bayan ta gama mai masu gyaran parlour da kitchen ta shigo tayi aikin ta ta gama ta shirya breakfast a dining burner ta dauka taga turaren dake ciki ma ya kone tsaki tayi dan tasan aikin Hasana ko Husaina ne zubar wa tayi cikin waste kana ta bude show glass ta zuba wani ta jona ya socket ba jimawa parlour ya dauki kamshin turaren wutan mai sanyi lumshe ido Afeefah tayi tana tuna irin wannan kamshin parlourn ta keyi gaba daya irin turarukan wutan Aunty ba wanda batada irin sa. Ajiyar zuciya ya sauke tare da fesar ma gaba daya sofa din parlourn wani air freshener mai sanyin kamshi hakan yasa parlourn bada wani scent mai dadi.
Bayan ta gama ta fada toilet tayi wanka sauri kawai take saboda yau flight dinsu Waheedah zaiyi landing gashi yau Friday tasan gidan zai cika yau, wata atampha ta dakko dinkin doguwar riga ta saka tsaki tayi ganin zip din yaki tafiya hakan yasa ta cire kayan ta dakko lace mai army green and lamon green flowers ta saka dinki riga da skirt daya sha bit work ba wata kwalliya tayi ba powder kawai ta shafa ta saka kwalli sai chap pet lipstick data saka hakan yasa fuskarta fitar da wani sanyayyen kyau haka ma dan kwali ba wani dauri tayi ba African turban ta daura ta saka earrings dinta fashion green mai adon stone diamond tayi kyau abunta. Faty ce data fita itada da Ammi suka shigo dakin kallon Afeefah tayi tace "wow Mrs Sulaiman is looking gorgeous" hade fuska Afeefah tayi tace "wlh Faty zamu samu matsala dake na gaya miki bana so" ta karasa kamar zatayi kuka. Faty ta ajiye Ammi tace "sorry darling nima bari nayi wanka sai mu fita gaba daya amma dai bari na fara ma Ammi saiki shirya mun ita yanda baza mu maki wai sting time ba" Afeefah tace "toh kiyi sauri". Ammi ta dauka tayi ma wanka Bayan ta gama ta nado ta a towel ta Mika ma Afeefah ita Nono ya fara bata kana ta hau shirinta ba bata lokaci sai ya Faty ta fito.Tabe baki Afeefah tayi tana dakko ma Ammi riga green tace "ke dai wlh wannan wankan naki dama kin daina wahalar da kanki kina yinsa" dariya Faty tayi tace "me yasa" Afeefah tace "daga kin shiga ko good 5 mins bakya yi kin fito wanda bai sanki bama sai ya dauka wlh watsa ruwa kawai kikeyi" sosae Faty tayi dariya tace "toh haka kawai zan wani zauna a bayi" bata ce mata komai ba itama ta shirya cikin lace irin na Afeefah Bayan ta gama shafa powder tace "Adda feefah dan Allah ki daura min dankwali irin naki" dariya Afeefah tayi tace "dole Kice Aunty muguwa" Faty tace "toh yana iya na bar maki girman yau" dankwalin ta karba ta fara daura mata Faty tace "ki shirya on Monday muna da lectures naga tunda abun nan ya faru kika rage zuwa skl gashi mun kawo karshe" shiru Afeefah tayi chan Bayan ta gama daura mata dankwalin tace "insha Allah....wow mrs Abbah kinyi kyau" dariya Faty tayi tana kallon kanta ta mirrow vail dinta ta yafa kana ta dakko wayarta Afeefah ma vail dinta ta dakko ta dauki Ammi dake wasa da abun wasanta Faty tace "bari muyi Friday pictures" gyarawa Afeefah tayi Faty ta dauke su mirrow pic da yayi kyau sosai.
Suna fitowa parlour Aunty ta shigo kallon su tayi cike da shawa tace "masha Allah yan matan Aunty sun cakare" dariya sukayi gaba daya bayan sun gaisa suka zauna zaman breakfast, ba jimawa su twins suka shigo suma sunyi kyau sosae cikin dinkin atamphar su gaba. Haka gidan Alh Mahmoud Bagudo yake cikin hadin kai zaman lpy duk Friday kuma haka suke yinta kamar sallah zaka gansu sun chakare abunsu.
Bayan sun gama suka fita part din matan gidan as usual suka gaida kowa daga karshe part din Abba suka nufa yana zaune shida ya ukasha suka shiga suka gaida su Abba ya amsa cike da fara'a da kulawa ukasha kuma tsokanar su ya fara "yan matan Abba irin wannan wankan kamar masu fita gasar kyau dai" dariya sukayi Afeefah ta zauna kusa da Abba tana ajiye masa Ammi tace "Allah ya ukasha baka da dama" wayarsa ya ciro daga cikin aljihu yace "a toh gaskiyar kenan bari na maku Friday pics kafin mu fita sallah" Abba na gayara ma Ammi dake bacci kwanciya yace "Allah dai ya shirya ku yanzu mutanen duniya basu da aiki sai hoto komai ace hoto" Faty ta turo baki ya zauna dayan side din Abba tace "toh Abba ba dole ba tarihi zamu ajiye" baice komai ba ukasha ya masu pictures masu kyau Faty tace "ya dan turo min dan Allah" harara ta yayi yace "kin San dai ba Xander ne da ni ba" tace "ai na sani nima na gyara waya ai" yace "Uhmm to gashi kiyi connecting airdrop saiki tura ki bani wayana dan kin San yara nasa rike min waya" Faty tace "karka damu yah Allah nima da nayi aure zan rika 11pro max din" Afeefah tace "keda kike da X kuma miye na wani chanza waya ni da banda iphone din ma na hakura ai" dariya Faty ta mata tace "Allah tunda kikayi aure kika koma yar kyau bari na gaya miki toh ko su Waheedah ya Fu'ad ya chanza masu waya 11pro ce dasu" Afeefah tace "sunji dadi kuwa"
Abba yace "karki damu Afeefatu kema zan siya maki wacce ce babba" ya ukasha yace "irin tawa ce Abba" Abba yace "nawa ne?" Yace "600k" Abba yace " yanzu haka kawai ka ciri kudi har dubu Dari shida ka siya waya anya kuwa ukasha" dariya yayi yace "Abba nima fa Abban Lagos ne ya siya min"
Abba yace "lallai toh shikenan tunda daddy's fav ce zan siya mata" Faty ta fara dukan kafa a kasa tace "Abba ni fa" yace "sai kun gama makaranta ai zan siya" tace "wow that's my sweet dad mungode Allah ya Kara Nisan kwana ya Kara budi kuma" Abba yace "Ameen .. bari kuje masjid lokacin sallah ya kusa" gaba daya suka fito parlourn ukasha da Abba suka wuce masallaci su kuma su Afeefah suka koma part din Hajja.
••••••••••••••🦋
Bayan sallar juma'a gidan ya cika kowa yazo sai fira suke da barkwanci Bayan sunci abinci Abba ya saka a kira masa gaba daya mutanen gidan saboda jiya Adda Maryam ta kirasa ta labarta masa komai hakan yasa ya tara kowa na gidan.
Bayan sun zauna aka bude taro da addu'a kana Abba yayi gyaran murya ya fara magana "jiya yar uwarku Maryam ta kirani ta sanar dani wani zancen daya daga hankali na har Auntyn ku tayi tambaya sai dai ban gaya mata ba" shiru kowa yayi yana maida hankalinsa sosae ya cigaba "Kowa yasan cewa Afeefah ta kafe akan bazata koma gidan aurenta ba wanda kuma har yanzu tayi ta sanar damu dalilin dayasa" rassss gaban Afeefah ya fadi ta jefa ma Adda Maryam wani kallon tuhuma ita kuma ta dauke kai hakan yasa ta maida dubanta gun abba daya fito da diary din Afeefah hawaye ne suka fara zubo mata a ido tana maimaita Kalmar innalillahi kasa tayi da kanta 'wato kenan duk neman diary din nan da nayi yana gurin Adda maryam toh meyasa hankali na bai bani ita ta dauka ba tunda ranar da suka zo ne na nema na rasa' maganar da Abba keyi ne yasaka zancen zucin da take yi "kowa yasan cewa Afeefah mai hakuri ce a cikin ku bata taba gaya maka damuwarta koda kuwa yankan jikinta akeyi karna cika ku da surutu Maryam tashi ki fada masu abunda ke faruwa ko hankalin yan uwanki zai kwanta"
Mikewa Adda Maryam tayi ta fada masu duk abunda ya faru gaba daya parlourn jikin kowa ya mutu murus su Faty harda Kuka ba wanda bai tausaya ma Afeefah ba a cikin su
Lallai rayuwar nan kwara daya ce sai dai tana zuwa da sauyin kaddara kala kala Afeefah tayi hakurin zaman aurenta ko a fuska bata taba nuna masu tana cikin wani hali ba su kuma ba wanda hankalin sa ya kawo wannan abun zai faru duk sai yanzu ne ma suke tunanin abubuwa daki daki shi yasa kenan tayi ta jinya a asibiti ashe dai ciki ake zubar mata to meyasa hankalin su bai taba basu su tambayi de abunda yayi sana diyar zubewar cikin ba? Wannan itace tambayar da suke ma kansu.
Cikin tsagwaron bacin rai Ashir ya mike yace "Abba bazata koma gidan sa ba koda hakan na nufin barin numfashi na a doran kasa"
Adam yayi sauri ya amshe zancen "Wlh kuwa Abba bazata koma ba kuma bama so ka saka baki cikin wannan maganar kawai ka zuba ido kayi kallo"
Wata irin ajiyar zuciya safa ta sauke hawaye na cigaba da zubo mata non stop Abba yace "Toh wai da kuke so na zuba ido nayi ta kallon ku idan komai ya lalace fa bama shi ba kun tambayi ita Afeefah din kunji ta bakin ta kuwa"
Ai bata San lokacin data dira gaban Abba ba cikin matsanancin kuka ta fara magana "na rokeka Abba dan girman son da kake ma Allah da manzon sa karka ce na koma abbana Kanin rai nice fa Afeefah Afeefahn ka koka manta ne Abba dan Allah wlh bazan iya ba zuciyata barazanar tarwatse wa take yi......" numfashin ta ya fara sama sama sai ganinta suka yi luuuu ta tafi kasa.
*Sorry guys I don't think zanyi typing gobe shi yasa na maku page mai tsawo yau*
*Karku manta zaku iya siyan book Dina Barikin sojoji a 200 kawai ku nuna min kauna❤️*
*And plssssssssss subscribing to my channel dan Allah na rokeku kumin subscribing ga sunan _Neeshar.jay_ nagode da kaunar ku❤️🔐*
#TeamAfeefah
#TeamSulaimanVote
Comment
Share
![](https://img.wattpad.com/cover/210623472-288-k184867.jpg)
YOU ARE READING
Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ
RomanceBana gaya miki bana son haihuwa ba wlh saena zubar da wannan cikin naki dan a tsari na haihuwa ki shirya karbar magani" "Wlh baka isa ka sakani zubar da kyautar da Allah ya bani ba Sulaiman kayi duk abunda zakayi" "Kayi hakuri Sulaiman bazan iya kom...