*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHEJAY* @wattpad
Page 3
#Flash Back
Mota ce tayi parking a cikin makeken harabar gidan Sen Mahmoud Bagudo, da gudu yaran gidan suka fito suna ma yayar su da ta dawo oyoyo dukawa tayi gaba daya yaran suka shige mata jiki sati biyu tayi bata gidan amma yanda suke mata kamar wacca tayi shekara bata gida Afrah da tafi kowa surutu tace "Adda feefah munyi missing dinki sosae da bakya nan kuma kullum sae yaya Bello yaci zalin mu ko Ummi" ta tambayi ummi dake gefe.
Aiko kamar jira take caraf ta amshi zance "ehh adda ranar da kika tafi ya hana mu kallon Nickelodeon"
Shafa kansu tayi tace "iyayen complain daga dawo wa na ko gida ban shiga ba toh naji zan mishi mgn kunji"
Ihu sukayi suna tsallen murna Fateemah tace "ni dae ba ruwana idan ya dawo ku kadae kukayi abinku"
Afrah tace "jimin Adda faty wae ba ruwan ta to wayace yaci zalinmu"
Ummi tace "dan yaga ba Mai rama mana ne yanzu kuma adda feefah is back"
Dariya kawae tayi tace "bazan iya da wannan surutu ba idan na biye maku sae mu kwana anan muje ciki" kama hannun su tayi suka wuce part din Hajja suka nufa dan Afeefah tasan halin ta yanzu sae ta fara mata fada ita kuma ba son hayaniya take ba.Parlourn shiru ba kowa sae Ac da tv dake aiki ga wani kamshin turare dake fita daga cikin burner dinda ke aiki, zama tayi a parlour ta aika Afrah ta duba ko Hajja na dakin ta ne
Dawo wa tayi tace "ehh adda amma tana toilet ne"
Kallon agogon dake parlourn tayi ta ga lokacin sallar asr yayi gashi ko azahar bata yi ba kuma barin ta parlourn nan wata masifa ce gashi Hajja na dadewa a sallah hakan yasa ta yanke shawarar shiga dakin su Afrah tayi sallah kafin Hajja ta fito.Tana shiga Hafsa na fitowa daga toilet da alama alwala tayi itama da sauri ta fada jikin yar uwar ta Afeefah tace "ni daga ni karki karyani Dan Allah yarinya da nauyi sae kace buhun cement"
Turo baki Hafsa tayi tana "kae Addah buhun cement fa kika ce"
Cire hijab dinta tayi tace "eh mana ko kin rage cin tsiyane yanzu"
Sallaya Hafsah ta dauko tare da hijab dinta tace "idan na biye miki adda sae lokacin sallah ya wuce gashi aiki zanyi yanzu"
Toilet Afeefah ya nufa tana cewa "kanki dae ake ji"
Itama alwala tayi tana fitowa ta tada sallah sae da tayi azahar kana ta dora da asr bayan ta idar suka gaisa da Hafsah kana suka fita gaba daya zuwa dakin Hajja suna fita tana fitowa tareda kwala kiran sunan Hafsah.Hafsah tace "gani Hajja"
Har kasa Afeefah ta duka ta gaida Hajja ya tsine fuska tayi tace "ae da na dauka sae bayan shekara zaki dawo"Smiling kawae Afeefah tayi tace "aa Hajja dama uncle ne yayi tafiya bayan naje gidan da kwana biyu shine yace na zauna har ya dawo"
"Ohh waya kawo ki toh"
"Flight na biyo sae Ado driver ya dauko ni nayi tunanin Abba ae yama gaya miki"
Zama Hajja tayi tana cewa "ina kuwa zae gaya min ke da kanki baki kirani kin gaya min ba amma ita Ramlatu data fi ni mahimmanci ai kin gaya mata"
Dama abunda take gudu kenan "Hajja ba haka bane Allah na kiraki wayar ki bata zuwa"
"Hmmm jeki dan Allah ni karki cika ni da surutun banza"Mike wa tayi ta fita itada Hafsa da duk ranta bae mata dadi ba abunda Hajja kema Afeefah gaba daya yan dakin su basa jin dadi dan yarinyar ba ruwanta.
Part din Aunty Amarya suka shiga tana parlour itada Ya Adam da Adda Hadeeza Asiya da twins sae tsiya suke ma Adam akan budurwar wae bata da gashi shi kuma ya hade fuska sbd su Asiya dake gurin a dole karsu rainashi "kanta kamar kwallon mangwaro" cewar Adda Hadeexa ba yan parlourn kadae ba harda su Afeefah da suke shigowa yanzu wae da sukayi dariya duk da basu dan mgnr da akeyi ba.
Kare hade fuska yayi yace "Aunty kina jinsu fa amma kikayi shiru"
Dariya tayi itama tace "kae ku tashi ku bani guri kun tasa mun yaro a gaba kuna masa tsiya"
Afeefah da take neman gurin zama tace "Haba Aunty daga dawowa na za'a fara korana"
"Aaa lale maraba yan Lagos ai ban ganki ba ya hanya"
"Lpy Aunty ina yini"
"Lpy qalau ya hanya"
"Alhmdllh Aunty""Adda Hadeey ina yini"
"Lpy Afeefatu ya hanya"
Turo baki tayi tace "Haba adda Hadeey daga dawowa na kuma sae tsokana"
Dariya itama tayi ta juya gurin Adam tace "ya Adam ina yini""Lpy yar kanwata ya hanya da kuma su uncle"
"Duk suna lpy ya Adda Ameera"
"Tana lpy bakya nan shiyasa suka saka ni gaba suna cimin fuska"
"Barni dasu Yaya zan rama maka tunda na dawo"
"Yauwa yar kanwata shi yasa neke ji dake"
Da sauri Hafsa ta amshi zancen da "ya Adam ni fa"
Kallon ta tayi yace "cab kedin hm Bari kawae nayi shiru"
Dariya akayi gaba daya parlourn Aunty tace "hmm an gama cin amfanin mangwaro za'a yarda kwallo ko da da bata tanan kullum sae ka nemi Hafseey na"
"Barshi Aunty ae tunda ya dawo Nima na Hutu da dahuwar Indomie da dare"
"Zaki Sani ae" cewar Adam.Daki Afeefah ta wuce da trolley dinta tana fadin "nikam na gani Bari na Warsaw ruwa na fito"
Da toh Hafsa ta amsa suka zauna suna firar su har aka Kira sallahr magrib kana suka mike gaba daya
************
Bayan kwana biyu suka shirya gaba dayansu dan komawa school dama strike aka je shi yasa Afeefah ta fiya Lagos gidan uncle Tukur.
Morning lecture suke dashi su hudu shi yasa suka fito da wuri sauran yaran gdan ma suka fito dan there getting late kallon su Afeefah tayi cike da sha'awan yanda kowa yayi kyau cikin uniform dinda 'Brilliance' suke yaran sae su Afeefah dake FUBK
Kallon yanda suke rigimar shiga gaba tayi sae ta tuna lkcn da suke yara......*Story*......
*Dadicated to Hassan Atk with love ❤️*
_____________
Subscribe for my YouTube channel plssss Ayshartou's diary plsssss dan Allah
_____________
Vote
Comment
Share
YOU ARE READING
Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ
RomanceBana gaya miki bana son haihuwa ba wlh saena zubar da wannan cikin naki dan a tsari na haihuwa ki shirya karbar magani" "Wlh baka isa ka sakani zubar da kyautar da Allah ya bani ba Sulaiman kayi duk abunda zakayi" "Kayi hakuri Sulaiman bazan iya kom...