*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHEJAY* @wattpad
Page 9
#BeginningOfMySadStory✨
Tun a daren farkon aurena da Sulaiman labari na ya fara chanzawa na fara sanin meye rayuwa take ciki, baka sanin matan aure na facing a lot of problems sai kayi auren kaji meke cikin sa, maza kala kala ne it depends on yanda Allah ya tsara kalar mijin da zaki aura baki San ya halinsa yake ba dan bazae nuna maki halinsa a waje sai kin shiga daga ciki, da yawan mu kafin aure muna da buri ko nace zabin ko mafarkin kalar mijin da muke son mu aura, amma sai kaga things suddenly changed. *Haka Nawa mijin yake* kuma shi Allah ya rubuta zan aura harda rabon haihuwa tsakani abunda yafi tsana a rayuwar sa kenan, baya son haihuwa ko meye dalilinsa nan sani ba, tun a wannan daren farkon ya bani wasu pills nasha dan ban san aikin me sukeyi ba kawai na sha ne kamar yanda ya bukata.
•••••••••🦋
Wasu hawaye ne suka zubowa adda Maryam na tausayin kanwarta ta duk da bata karasa karantawa taji wace kalar wahala Afeefah ta Jura ba a gidan auren ta, bata taba sanar da kowa akan cewa Sulaiman baya son haihuwa ba duk da dukan daya mata Ranar da aka maidata daga mahaifi har ta samu dislocation a hannun damanta kawai tace sun samu matsala ne a daren amma bata gayawa kowa matsalan da suka samu ba duk da tambayar duniya da aka mata. Haka ta ajiye diary din ta kwanta dan dare ya raba pass 3, bacci barawo ne ya dauke ta badan ta shiryama zuwan sa ba.
••••••••••••✨
______________
*AFEEFAH*
______________Tun Bayan sallar magrib take nemen diaryn ta amma shiru duk inda take tunani zata iya ajiyesa ta duba bata gani ba sosae hankalinta ya tashi ta shiga damuwa da kyar ta samu tayi sallahr isha haka ta hargitsa dakin amma ko littafi Mai kama dashi bata gani ba dole ta hakura ta kwanta, kusan karfe 12am Faty ta shigo dakin mekewa tayi da sauri tace "Faty bana son wasa idan ke kika daukar mun diary to ki bani kayana, na yafe miki karantawar da kikayi"
Dariya Faty tayi tace "God of mercy, Allah da gaske bani na daukar miki diary ba Afeefah maybe you kept it somewhere else"
Tace "No Faty I kept it under my pillow after I wrote what had happened during the day sai na fita gurin su Adda Maryam Bayan na dawo kuma sai ban gani ba and I've searched everywhere but I couldn't find it"
Faty tace "eyya bari gobe da safe I will help you look for it kinji" Afeefah tace "alright"
Kukan Ammi ne ya maida Afeefah kan gado ta dauke ta sosae kukan yarinyar ke kuma sakata tsanar Sulaiman da bai mata wannan wulakancin ba da yanzu suna tare, tsaki tayi tareda daukar yarinyar ta fara aikin lallashi amma a banza dan little Ammi ba dai kukan banza ba kuma bata tashiyin kukan sai dare yayi. Yanda Afeefah taga tana haka taga dare sai gurin 2 Ammi tayi bacci bayan ta ajiyeta ya shiga toilet ta dauro alwala sallah ya dinga yi har karfe 3 kana ta kwanta amma duk da haka tunani ya hanata yin bacci sosai take son tayi bacci amma fir yace baisan zancen ba. Sae bayan sallahr asuba tayi ma Ammi wanka ta cika mata ciki kana ta bada ita dakin Aunty ita kuwa bacci ta kwanta dan sosae take jinsa.•••••••••••••🖤
___________
*SULAIMAN*
___________Gaba daya ji yake kamar duniya ta tsanesa ne sai yanzu yake kara nadamar abunda ya aikata ma Afeefah, zaune yake akan dining kallo daya yana breakfast dinda Atika ta ajiye masa ya dauke ido Fried sandwich ne da Costard daya ji madara, tunanin ranar da Afeefah ta fara saka shi cin sandwich ne ya fado masa.
•🦋
Sanye take da wata doguwar girar egg yolk yellow material kanta yasha kananun kitso two step kai kawo take tsakanin kitchen da dining bayan ta gama jera gaba daya kayan breakfast din ta koma daki a dai dai lokacin da sulaiman ke saka takalman sa, gaban dressing mirror dinta taje ta dakko turaren ta Amir oud ta dawo gabansa fess masa tayi ta dakko hularsa muhadu banki dake ajiye kan gado ta saka masa smiling tayi tare da hade fingers dinta biyu 👌🏻 alamun yayi kyau, jawo ta yayi tareda hugging dinsa yace "ji nake kamar karna fita yau" zaro ido tayi tace "dalili" yace "I just want to spend time with you" dukan wasa ta kai masa a kirji tace "ni ban yarda ba"
Yace "serious" tace "ina Bayan Jumma'at zaka dawo"
Yace "ehh" tace "toh ai ba jimawa zakayi ba ni kaga ma I don't have lectures today and su Faty zasu zo yau" smiling yayi yace "kice karma na dawo tunda baki zakiyi" mararai cewa tayi tace "Allah ni dae ban yarda ba kawai ka dawo" yace "toh zan dawo mrs" dariya tayi tace "you are getting late muje kayi breakfast" hannun sa ta kama suka fita har dining Bayan ya zauna ta saka mishi sandwich dinsa akan plate sae tea data hada masa a mug ta bashi. Kallo ya bita dashi tare da yatsine fuska yace "meye wannan" tace "sandwich ne na maka mr" yace "nifa kin San dan kauyene ban iya ci ba" dariya tayi tace "kai mr amma da dadi fa" yace "aa matas barni kawai nasha tea" kallonsa tayi kamar zatayi kuka tace "yanzu sai da nasha wahala na maka kace bazaka ci ba" jawo hannunta yayi yace "kin San nifa ba iya cin wadan nan abubuwan nayi ba ko pizza ke kika koya min cinsa" tace "ehh wannan na zan koya maka ne Allah da dadi" yace "toh" zama tayi ta dauka fork da table knife ta yanka masa dai dai wanda zai shiga bakin sa ta bashi karba yayi ya fara ci sosai yaji dadin sa a haka har suka gama ci. Ranar da Atika ta karba girki yace ta masa sandwich tace ita bata iya ba yace "to ki koya mana Kinga Afeefah ta iya kuma da dadi sosai"
Idan ranta yayi dubu ya baci hakan yasa tayi downloading video din yanda ake hada sandwich tayi masa duk da ba wani dadi yayi ba.•🦋
Numfashi ya fesar tare da mikewa tsaye dan yayi late kota kan abuncin dake gabansa baibi ba ya wuce abunsa.
____________________________
*Dedicated to Hassan Atk with love ❤️*
_____________________________*manage plss idan na samu time zan maku posting zuwa dare insha Allah*
~~~~~~~~~
Subscribe for my channel #Neeshar.jay
~~~~~~~~~~Vote
Comment
Share*Lioness*👑
YOU ARE READING
Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ
RomanceBana gaya miki bana son haihuwa ba wlh saena zubar da wannan cikin naki dan a tsari na haihuwa ki shirya karbar magani" "Wlh baka isa ka sakani zubar da kyautar da Allah ya bani ba Sulaiman kayi duk abunda zakayi" "Kayi hakuri Sulaiman bazan iya kom...