Part 2

430 46 1
                                    

*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
                _(Nefarious Hubby)_

   Written by *NEESHAR.JAY*

   *NEESHEJAY* @wattpad

Page 2

Gaba ɗaya daren bata samu bacci ba ko kaɗan ga kukan da ammi ta addabe ta dashi cikin daren ko sallar da take yi dole tayi raka'a biyu kawai ta idar gaba daya ammi ta dagula mata lissafi ji take daba yarinya ce yar wata biyu da kwana huɗu ba da ba abinda zai hana ta dake ta baƙin cikin da Abban  ta ya saka ta a ciki ta rasa me za ta yi tunani

Mitstsika ido Hafsa tayi kukan Ammi ya hana ta
barci ga shi da alama tana Jin Afeefah na jin kukan nata amma taƙi kula ta, saukowa tayi daga kan gadon tare da kunna fitilar ɗakin haske ya gauraye ko ina Afeefah na zaune ta rafka uban tagumi da alama bata ma san Hafsa ta farka ba, ɗaukar Ammi tayi ta Sab'a a kafaɗa bedside drawer taje ta ɗauko zam-zam ta bata amma hakan bai sa ta daina kukan da take ba. Hakan yasa ta koma gefen Afeefah ta zauna kallon tausayi take bin 'yar uwar ta ta da shi dan idan kaji labarin wahalar da Tasha a gidan mijin ta sai ka zubar da ƙwalla a haka kuma auren soyayya suka yi gaba ɗaya ji  ta yi kalmar aure ta fice mata a rai *sabo da* ganin yanda yayar ta ta koma kamar mara gata *sai* kace ba ita bace *Daddy's favorite* ba Jin kukan Ammi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, dafa Afeefah da tayi zurfi sosai cikin tunani tayi firgigit ta ɗago fake smile tayi wa Hafsah tace "Au kin tashi"

Hafsah tace "hmm adda wannan dogon thinking ɗin da kika shiga ina zaki ji motsi na ga Ammi sai kuka ta ke kamar ranta zai fita kuma zafi nake ji saboda kin kashe Ac akan bakya son sanyi wallahi adda ban San ya zaki yi ba idan kika auri  mai son sanyi ni kam bari na koma ɗakin mu gaskiya ba zan iya kwanciya zafi ya kashe ni ba"

Dariya Afeefah tayi tana karb'ar Ammi tace "toh uwar mita naji  mai hali  dai baya taba  canza wa"

Dariya Hafsa tayi tace "Haba Adda da fa Ac yayi 10mins zaki ce ɗaki yayi sanyi a kashe ina zan iya kwanciya dake kam"?

"Toh naji  sai da safe ki kashe min fitilar idan za ki tafi"

"Au haka zaki ce bama zaki bani hakuri ba kice na kwanta"

"Aa jeki abinki dan ba zan kunna Ac ba  sai kuma gobe sanyin dakin haka yayi"

"Chabb ba da ni ba na gudu kamm, karfe nawa ma ne wai.."? kallon agogon dake makale a ɗakin tayi 2:13am ta furta a fili "Bari naje na runtsa kafin 4 dan gobe da safe zan fita  please Adda karki bar Ammi tana kuka"

Miƙewa tsaye tayi tana ajiye Ammi daga koma bacci tace "toh uwar Ammi  sai da safe"

Dariya tayi ta fita tare da kashe wutar ɗakin Afeefah kuma ta haye gado amma ina bacci yace  bai san zancen ba  sai tunani fal da ya cika zuciyarta da ruhinta gaba ɗaya ta kasa samun sukuni ga ciwon hannunta har yanzu duk da an gyara tana Jin zafi sosae kamar yanzu ne akayi gyaran Bayan kuma ya kwana biyu sae Allah ya isa take zabga ma Sulaiman ga wata irin tsana da take mishi Mara misaltuwa.

    _____••

Washe gari da safe bayan ta farka daga baccin daya dauketa Bayan sallahr asuba ta mike daga kan gadon ganin babu Ammi yasa ta shige toilet dan tasan tana hannun yaran gdan gashi yunwa takeji rabontawda abinci har ta manta. Wanka tayi ta fito ta shirya cikin zani da riga na atampha mae kawae ta shafa ta fice dan cikinta sae kukan yunwa yake mata dakin aunty ta fara shiga bayan sun gaisa ta fice zuwa dinning tea ta hada tareda soyayyen dankali ta zauna ci sae da ta koshi kana ta fita part din sauran iyayenta dan haka ne al'adar gidan da safe kowa zae tashi yaje ya gaida mutanen gida. A parlourn mama ta hadu da Ashir ukasha da dawood suna kallo Bayan sun gaisa ta shiga dakin mama suka gaisa tana fitowa Abba na shigowa har kasa ta duka ta gaidashi yace "ya akayi ban ganki part Dina ba"

Tace "Abbana dama yanzu zanje yau din nan bacci nayi sosae"

Yace "a yanada kyau ai ina amaryata ne"

"Tana dakin Aunty"

Abba yace " toh a kawo min ita na ganta"

Tace "toh Abba". Har ta kae bakin kofa yace "Afeefatu ina din mgn dake a parlour na kinji"

Tasan tatsuniyar gizo bazae wuce koki ba toh kawae tace tareda ficewa daga parlourn Abba dasu Ashir kuma kallon tausayi suka bi yar uwarsu dashi duk wahalar da sulaiman ke gwada mata bata taba kawo kararsa ko afuska ta nuna tana da damuwa ba sae yanzu da abun yayi muni.

A gefen Sulaiman kuma gaba daya daren ranar kasa bacci yayi sae tunanin yanda yayi misusing opportunity dinsa kawae yake yi tunanin yanda Afeefah zata masa nisa, nisa na har abadah yake yi lallai ya tafka babban kuskure a rayuwa da ana maeda hannun agogo baya da ba abunda zae hanashi dawo da rayuwarsa da Afeefah ba ya gyara duk laifin da ya mata dan a yanda yake gani tana gab da kubuce masa..... tunanin ranar daya fara ganin ta yakeyi...



       *FLASHBACK*


    *Dadicated to Hassan Atk with love❤️*


   ___________________

*Dan Allah you guys should plsss Ina rokonku dan Allah kuyi subscribing YouTube channel Dina @Ayshatou's diary plssssss dan Allah thanks*
_____________________




Comment
Vote
Share

Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ  Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ  Where stories live. Discover now