Wife Material🧕🏻

302 36 1
                                    

                             #WalimaDay

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

                             #WalimaDay

                             #WalimaDay

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

                        #Dinner🖤✨


*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_

Written by *NEESHAR.JAY*

*NEESHEJAY* @wattpad

Page 8

#WifeMaterial

Jin motsi na a bayan sa ya saka shi jiyowa, kallo daya  yamin ya dauke Kansa baice min komai ba, shiru ne ya biyo baya har na tsawon minti 3  gashi sanyin Ac ya fara min yawa dan bana son sanyi ko kadan. Jin tarina ne  ya saka shi dago Kansa "baki iya sallama bane"
Shiru nayi Ina cigaba da wasa da fingers dina yace "am i not talking to you" cikin sanyina na tace "ya nayi sallama fa" shiru yayi kafin yace "get lost" kallon mamaki na bisa dashi kafin na iya daga kafana na bar parlourn. Ina fita nayi kicibus da Siyama da sauri na matsa gefe, wani mugun kallo ta watsa mun daya saka ni jin kayan cikina na motsi da sauri na bar gurin. Bayan na koma part din mommy na tarar gaba daya sun watse hakan yasa na shiga daki kawai, dukan su sunyi shirin kwanciya hakan yasa na tube kayana dan na samu nayi wanka  ina jinsu suna tambayana ko dukana ya fu'ad yayi na masu banza na shiga toilet ban jima ba na fito tare da saka kayan baccina na dauko hijab har kasa na saka saboda kayan riga da wando ne. Shafa'i da witiri nayi Bayan na idar na linke hijab din da sallaya a daidai lokacin kiran Sulaiman ya shigo wayana dauka nayi tareda yin sallama bae amsa ba yace "ina kika ajiye wayarki" numfashi na sauke tace "na saka charge ne, Ina yini"

"Lpy qalau ykk"

"Lpy alhmdllh" nan muka cigaba da firar mu har karfe 10:47pm kafin na mishi sallama shima badan yaso ba nima haka take a gurina amma bazanyi abunda nasan idan ni akama ba zanji dadi ba, yana da mata bana so na shiga hakkinta shi yasa bana bari  idan muna waya mu wuce 11. Addu'a nayi na kwanta, tunanin abunda ya fu'ad yamin dazun ya fado min smiling kawai nayi Ina kara jan blanket dina.

Kwana ki sai tafiya sukeyi kamar yanda aurena keta matsowa hakan yasa aka fara shiye shiryen abunda ya dace.  Ana saura sati daya biki gaba dayan mu muka zo kebbi banda ya fu'ad da yace sai satin aure. Gidan ya cika da mutane kowa sae shriye shirye yake yi ni ddai nawa ido ne kawai, kome akayi sai dai nayi smiling saboda bani da bakin magana gaba daya jina nake wani iri sosai miskilanci na ya karu bana magana saita kana abu daya nasan Inayi shine murmushi yanzu ko waya da Sulaiman na rage sosai na rasa dalili.
Maganar matar sa kuma idan nace nasan abunda take tsarawa nayi karya tun ranar data kirani bata kuma kira ba har yau hakan yasa nima nayi watsi da  tunanin ta na cigaba da harkokina.
Bana son hayaniya shi yasa kawai na yanke shawaran yin event daya wato walima ba yanda 'yan gidan mu  basuyi ba amma fir naki dan bana son bidi'a, ba yanda suka iya sai hakuri duk da gaba daya ji suke kamar su rufeni da duka. Abu daya ne ya faranta masu rai Jinda sukayi Sulaiman yace abokansa sun shirya masa dinner hakan yasa sukayi farin ciki sosae suka fara hidimar fitar da anko, anko biyu sukayi daya na walima sai daya na dinner.

Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ  Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ  Where stories live. Discover now