*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHEJAY* @wattpad
*Not Edited*😞🥺💔
Page 10
Kiran wayarta da Waheedah tayi ne ya sakata farkawa badan baccin ya ishera ba cikin muryar bacci ta daga wayar tare da yin sallama, ko amsawa Waheedah bata samu damar yi ba tace "Adda guess what?" Mikewa zaune Afeefah tayi tace "Waheedah ban hanaki wannan banzar dabi'ar ba" turo baki tayi kamar tana gabanta tace "Wslm Adda Ina yini"
Tsaki Afeefah tayi tace "idan zaki gyara ki gyara toh me yasa kika tashe Ina bacci" zaro ido tayi tace "Adda yaushe kika koyi baccin safe?" Afeefah ta murza idonta dake cike da bacci har yanzu tace "ban samu nayi bacci bane jiya" cike da damuwa Waheedah tace "toh meya hanaki bacci Loml" shiru Afeefah tayi can kuma sai ta chanza maganar tace "I cant guess just tell me" ajiyar zuciya Waheedah ta sauke tace "me yasa idan muna magana kike son chanza topic din I asked you something and kina son banzantar da magana ta kin San yanda nake ji kuwa Adda me yasa bakya son sharing problems dinki dani after all ni kadai kike da da zaki iya gawa matsalar ki, Adda kin san yanda nake ji yanzu haka tun ranar da mukayi waya da Adda Maryam ta gaya mun komai baki San halin da na shiga ba kinfi so ki rike shanye damuwan ki keka dai ko, sai yanzu Na gane bani da wani amfani a gurinki da nice ko sauro ya cijeni zan kiraki na gaya miki, ba kowa ce damuwa bace mutum zai iya barwa kansa ba maybe da kin sanar dani kaso 30 zai rage daga cikin abunda kike ji. Anyway dama I called to inform you that yah Farouk yayi new girlfriend Mai sunanki"Share kwallar da ta zubo daga idanun ta tayi tace "Waheedah"
Da sauri tace "Adda zamuyi magana an jima mommy na kirana" kit ta kashe wayar.
Da kallo Afeefah ta bi wayarta dashi tasan cewa zatayi complain ne shiya sa Waheedah kashe mata waya, shiru tayi tare da fa dawa duniyar tunani, kiran sallahr azahar ne ya sakata saukowa daga kan gadon ta nufi bayi.
••••••••••••••🦋
Adda Maryam kam bata samu damar zama karanta book din ba sae bayan Asr saboda bakin da tayi, Bayan tayi sallah ta rufe kofar part dinta tunda yara suntafi Islamiya, bedroom dinta ta koma tareda kunna Ac ta dale gadonta ta jawo diary din ta Dora daga inda ta tsaya
__________✨
Amarci muke ci sosae abinmu dan har yanzu ma ba'a koma skl ba, kamar yanda kowa ya sani Bayan kwana 7 ake fara raba kwana toh hakan ta kasance, zaune muke gaba dayan mu a parlourn sulaiman Atika sai cika take tana batsewa kamar ta fashe ni dai kaina a kasa Ina wasa da zoben hannuna, gyaran murya yayi yace "kamar yanda kuka sani idan amarya tayi kwana bakwai ake raba kwana, shi yasa na kiraku dan naji yanda zaku tsara abun dan ni bazan maku shishshigi ba"
Tabe baki Atika tayi tace "hmmm sai yanzu ne kasan baza ka mana shishshigi ba Wlh ka ban mamaki sulaiman ban taba tunanin akwai ranar da zaka min kishiya ba, meka nema daga gurina ka karasa meye bana maka?" Daga mata hannu yayi yace "ba complain na Kira kimin anan ba madam"
Tsaki tayi tare da dauke kai yace "kun min shiru ku nake sauraro" Afeefah tace "nikam duk abunda tace na amince" kallon sa ya maida kan Atika yace "toh kinji me tace what is your decision"
Tsaki tayi tace "da can da zakayi auren ka nema decision dina ne sai yanzu akan wani raba kwana zaka tambayeni idan kaga dama kayi zaman ka a gurinta meye matsalata" murmushi yayi yana jinjina kai yace "haka kika ce" cike da rashin kunya tace "Ras kuwa" yace "toh nida amaryata muna godiya dama nan gama morar amarcina ba" dagowa Afeefah tayi ga mamakinta taga Atika ta mike ta fice fuuuu kamar guguwa. Wani miskilin murmushi sulaiman yayi yace "kina wasa dani Atika I will make you regret abunda Kika fada" mikewa yayi ya kalli Afeefah yace "mrs zan fita" rakashi tayi har bakin kofa kana ta koma daki cike da tunanin haukar Atika.
![](https://img.wattpad.com/cover/210623472-288-k184867.jpg)
YOU ARE READING
Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ
RomanceBana gaya miki bana son haihuwa ba wlh saena zubar da wannan cikin naki dan a tsari na haihuwa ki shirya karbar magani" "Wlh baka isa ka sakani zubar da kyautar da Allah ya bani ba Sulaiman kayi duk abunda zakayi" "Kayi hakuri Sulaiman bazan iya kom...