Shimfida

1.1K 79 2
                                    

*Haka Nawa Mijin Yake*🦋
_(Nefarious Hubby)_🦋


Written by *NEESHAR.JAY*

*NEESHEJAY* @wattpad

*#SHIMFIDA*


Alhaji Mahmoud shine yaro uku a gurin Alh Adam Bagudo da matarsa Hajiya Hadeeza wacce suke Kira da inna, asalinsu yan garin Bagudo ne karamar hukumar dake cikin jihar kebbi, Alh Adam babban Dan kasuwa ne da yayi fice a harkar siyar da kayan sakawa danginsu atampha lace shadda da sauransu, sana diyyar wannan sana'ar tashine ya koma cikin birnin kebbi da zama a unguwar Badariya da zama idan kace Alh. Adamu Bagudo ba wanda bae sanahi ba.

Zaman lapiya yake sosae da iyalansa matarsa daya da yara 5, ba yanda ba'ayi ba akan ya kara aure firr yaki danshi ba mutum bane Mae son hayaniya gashi yana ganin yanda gdansu ake fada kamar zasu tashi gari hakan yasa kwata kwata bayada sha'awar kara aure.

Alh. Tukur shine yaron sa na farko babban dan kasuwa ne shima dayayi fice sosae, yana da mata biyu da yara 7 suna zama a kano.

Sae Alh. Ahmad shikuma sana'ar chanji yake yi Kuma alhmdllh sana'ar ta karbesa sosae, yana da mata daya da yara 3 yana zama a lagos ne.

Sae Alh. Mahmoud Wanda yake service yanzu danshi degree yayi sauran yan uwansa Kuma iya diploma suka tsaya ba yanda babansu baeba akan su koma makaranta sukaki acewarsu iya diplomar ta ishe su,

Sae Fateemah da Falmata yan biyu suma duk sunyi aure amma suna zuwa makaranta duk da haka suna karatunsu fateema na karantar mass com Falmata Kuma Polital science.

    Alh Mahmoud babban dan siyase yana da mata  hudu Hjy Ameena wacca suke cema Mama Hajja itace ta farko

Halayen Hajiya Ameena shine bata son mutane, bata hada yaranta da kowa ba sannan ga bakar muguntar da take ma yaran matar Alh Mahmoud ta uku. Yaranta sune
Ashir
Adam
Ukusha
Asiya
Falmata
Hafsa
Maimunatu(afrah)

Sae Matar sa ta biyu Hjy mariya suna kiranta da mama, bata da hayaniya shi yasa mutane ke mata kallon Mae daukar kae sannan bata daukar raini daga gurin ko waye dan tafito ne daga gdan masu hannu da shuni. Yaranta
Maryam
Hadeeza
Faruk
Dawood
Bello

Sae Matar sa uku Hjy Aisha wacce suke Kira da ammi macece mai hkr matuka dan ba karamin wahala take sha a gurin hjy Ameena ba sbd kyau da Allah yayi mata asalinta yar Bagudo ce amma a birnin kebbi suke zama itada iyayenta masu kudi ne sosae dan idan kace Alh Ali Bagudo ba wanda bae sanshi ba babban Dan siyasa ne, bata da hayaniya Kuma kowa nata ne ga fara'a da son mutane, yaranta biyu
Afeefah
Waheedah
A gurin haihuwar waheedah ne Allah ya dauki ranta sosae mutuwar ta girgiza mutane musamman Alh Mahmoud da mahaifinta da Allah ya Dora masa son yar duk cikin yaransa sbd hakuri irin nata.

Sae Hjy Ramlatu itace amaryar sa suna kiranta da Aunty macece mae son girma da fada amma duk da haka tana son mutane dan kaf gdan idan ka cire Alh Mahmoud tafi kowa kula da Afeefah da waheeda sbd biyayya da suke mata Kuma Allah ya dora mata son yaran. Yaranta
Hassan da Hussaina
Fateemah.
Aisha(ummi)

      Wannan sune zuri'ar gdan Alh Mahmoud Badugo.

******

Sulaiman matashin Lecturer mai ji da kansa yana da rufin asirinsa dan yana samun albashi mae tsoko sbd yanada masters dinsa so salary dinsa ba daya yake da masu degree ba.

Matarsa ta farko Atika yarinya yar kwalisa itama mae ji da kanta sannan tana mugun son Sulaiman shi yasa koda yace baya son haihuwa bata ka dashi ba bugu da kari shawarar da take samu gurin kawarta shamsiya.


**********

Fu'ad yaro ga yayar maman Afeefah Asalinsu yan Yelwa ne. Alh Muhammad Yelwa a Bagudo ya hadu da matarsa Hjy Zainab suna zaman lpy sosae da matarsa aban qaunarsa.

Yaransu hudu ne
Fu'ad shine na farko, matashin saurayi yanada shekara 30 yanzu, matarsa daya Siyama da yaro daya Suhail da shima dakyar ta yarda ta haifesa acewarta ita bata shirya haihuwa ba bata so ta tsufa da wuri

Umar(faruq) shine na biyu
Ahmad(Ashraf)
Sae auta Husnah



______________*______________

*Toh ku biyoni dan ganin yanda wannan qayataccen labarin zae kasance*

Karku manta comment on every single paragraph and vote and every page plssss

Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ  Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ  Where stories live. Discover now